Putin ba zai min wargi ba - Trump
Shugaba Amurka Donald Trump ya ce ba don shi ne shugaban Amurka ba, da yanzu shugaban Rasha Putin ya mamaye Ukraine baki ɗaya.
Trump ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar wato White House, inda ya ƙara da cewa ba zai laumci wargi ba.
"Ni ne shugaban Amurka, don haka Putin ba zai min wargi ba," in ji Trump a lokacin da suke shirye-shiryen ganawa da Putin a Alaska.
Trump ya ce tun a farko ganawar ce zai fahimci inda Putin ya dosa, domin a cewarsa, "gawanar ba za ta ɗauki lokaci mai tsawo ba."
Ya ce maƙasudin ganawar ita ce a buɗe ƙofar tattaunawa domin samar da yarjejeniyar da za ta kai ga tsagaita wuta a Ukraine.
Daga wannan tattaunawar ce za a samu damar janyo shugaban Ukraine ciki domin a ci gaba da tattaunawa tare har a samar da maslaha.
"Idan tattaunawar ta yi kyau, zan kira Zelensky shi ma sai mu haɗu, amma ina fargaba da kashi 25 cewa tattaunawar ba za ta yi nasara ba."