Kammala rahotonni
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Asabar.
Sai kuma gobe za mu kawo muku wasu rahotonnin a wani shafin daban.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/08/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Asabar.
Sai kuma gobe za mu kawo muku wasu rahotonnin a wani shafin daban.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban rundunar sojin Rasha, Janar Valery Gerasimov, ya ce dakarun ƙasar na kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a fagen dagarsu da ke cikin Ukraine.
Janar Gerasimov ya ce yanzu Rasha na iko da kusan duka yankin Luhansk da kuma fiye da kashi 70 cikin 100 na sauran yankuna uku da ta mamaye a gabashin Ukraine ɗin.
Tun da farko Shugaban Ukraine Zelensky ya zargi Rashar da amfani da lokacin neman shirya tattaunawar zaman wajen kai "munanan hare-hare". Hare-haren da Rashar ta kai da tsakar dare sun kashe mutum ɗaya.
Ministocin harkokin waje na ƙasashen Tarayyar Turai na yin wata ganawa a birnin Copenhagen na Denmark, inda suke tattaunawa batutuwa da dama ciki har da ƙaƙaba wa Rashar ƙarin takunkumai.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce aƙalla mutum 13 ne suka mutu sannan sama da 20 suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da ɗimbin jama'a ya kife.
Mazauna jihar ta Zamfara sun bayyana cewa jama'a sun shiga jirgin ruwan ne domin tsere wa wani hari da ƴanbindiga suka kai kan wasu al'ummomi.
Jihar dai ta zama cibiyar tashin hankali wanda ƙungiyoyin ƴanbindiga ke haddasawa - sannan a ɗaya gefe sun janyo zubar da jini da kuma mutuwar mutane da dama a faɗin arewacin Najeriya.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta faɗa a watan Mayu cewa idan gwamnati ta gaza shawo kan waɗannan hare-hare da ake kaiwa lamarin zai janyo mutuwar dubban mutane da kuma gagarumin bala'i.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙungiyar Houthi a Yemen ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai Sanaa, babban birnin ƙasar, sun janyo mutuwar firaministan mulki Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi.
Harin na ranar Alhamis ya kuma jikkata wasu manyan jami’ai da dama.
Sai dai an bayyana cewa Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi ba ya daga cikin waɗanda ake gani a matsayin manyan jagororin ƙungiyar.
Kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun ruwaito cewa sojojin ƙasar na da yaƙinin cewa watakila sun kashe dukkan jagororin ƙungiyar 12 da ke samun goyon bayan Iran.
Ƴan Houthi sun sha kai hare-hare da makamai masu linzami kan Isra’ila domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Gaza.

Asalin hoton, @elrufai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta zargi tsohon Gwamna Nasir El-Rufai da shirya taron siyasa ba bisa ƙa'ida ba, inda ta ce an yi rikici har da harba bindiga.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Mansir Hassan, ya fitar ta ce ta ƙaddamar da bincike kan rikicin da 'yandabar siyasa suka yi a garin na Kaduna.
"Binciken farko-farko ya nuna cewa taron ya jawo hatsaniya, inda har 'yandaba da 'yanjagaliyar siyasa suka gwabza wanda kuma ya jawo jami'an tsaron da ke tare da tsohon gwamnan suka yi harbin da ya jawo tayar da hankali a jihar," in ji sanarwar.
Sai dai matasan jam'iyyar haɗaka ta ADC sun yi Allah wadai da rikicin, inda suka zargi jam'iyyar APC mai mulkin jihar da "tura musu 'yandaba domin hana su gudanar da taron".
A cewar rundunar 'yansandan: "Domin gano gaskiyar lamari, mun bincika kuma shugabannin jam'iyyar sun nesanta kansu daga taron, kuma suka musanta iƙirarin tsohon gwamnan da waɗanda suka shirya taron."
Nasir El-Rufai na cikin jagororin siyasar Najeriya na ɓangaren adawa da suka dunƙule a jam'iyyar haɗaka ta ADC domin ƙalubalantar APC a babban zaɓe na 2027.

Asalin hoton, Nigeria Police
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Neja ta ce ta kama mutum biyu bayan wani mutum ya ɗauke su haya domin kashe wani mutum da ya aure tsohuwar matarsa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa dakarun da ke bakin aiki ne suka kama Muhammad Mohammed mai shekara 40, da Mohammed Usman mai shekara 35 a Beji da ke birnin Minna.
"Bayan fara bincike, aka ga bindiga ƙirar gida a tare da su, da harsasai, da kuma naira 13,000," in ji sanarwar.
"Waɗanda ake zargin sun amince cewa wani mai suna Dogo ne ya biya su domin halaka mutumin da ya auri tsohuwar matarsa. Sun ce ya biya su kuɗin mota N13,000 tare da alƙawarin N100,000 idan sun kammala aikin."
Rundunar ta ce ta ƙaddamar da neman kama Dogo.

Asalin hoton, Reuters
Wani mutum ya harbe tsohon shugaban majalisar dokokin Ukraine Andriy Parubly a garin Lviv da ke yammacin ƙasar, a cewar hukumomi.
Wani bidiyo da ke waɗari a intanet da aka ce na kisan ne ya nuna wani mutum sanye da kakin direban isar da saƙo na zuwa wajen Parubly a gefen wani titi ɗauke da bindiga, kafin daga baya ya bar wurin.
Yanzu jami'an tsaro sun ƙaddamar da neman maharin.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya siffanta kisan a matsayin "kisan gilla mai haɗari" kuma ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan Parubly.
Parubly mai shekara 54 ya shahara ne lokacin zanga-zangar Euromaidan a Ukraine, inda mutane suka dinga neman ƙasar ta kyautata alaƙa da Tarayyar Turai da kuma sauke tsohon Shugaban Ƙasa Viktor Yanukovych mai goyon bayan Rasha a 2014.

Asalin hoton, EPA
Mutum uku sun mutu a Indonesia sakamakon wutar da masu zanga-zangar suka tayar a ginin gwamnati da ke birnin Makassar da ke gabashin tsibirin Sulawesi.
Wani jami'in gwamnati ya ce jami'ansu biyu sun makale a cikin ginin, yayin da wani jami'in gwamnati guda kuma ya mutu a asibiti.
Wutar ta tashi ne a yayin zanga zangar da ake a fadin kasar akan mutuwar wani direban tasi a Jakarta,babban birnin kasar. Direban tasin Affan Kurniawan, ya mutu ne bayan da wata motar 'yan sanda ta kade shi.
Jami'an gwamnatin kasar na zargin masu zanga-zangar da afka wa ginin gwamnatin da kuma cinna masa wuta. Wani mutum da ke gefen wajen da ake zanga-zangar ya ce "na shaka barkonon tsohuwa hakan ya sa na ta yin atishewa ba kakkautawa."

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce a ranar 18 ga watan Satumban wannan shekarar da ake ciki ne dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya saka a jihar Rivers za ta zo ƙarshe.
Wike ya bayyana haka ne bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ake yi a yau Asabar, 30 ga watan Agusta, inda ya ce da zarar dokar ta-ɓacin ta kawo ƙarshe, zaɓaɓɓun ƴanmajalisar jihar za su koma bakin aiki kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
"An gudanar da zaɓen cikin lumana, kuma mutane suna ta tuttuɗowa akwatunan zaɓensu domin su kaɗa ƙuri'arsu," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "na san cewa zuwa ranar 18 ga watan Satumba dokar ta-ɓaci da aka saka a jihar Rivers za ta zo ƙarshe, inda majalisar jiha za ta koma aiki."
Ministan ya ce kasancewar an samu gwamnati a dukkan matakai a jihar - gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi da majalisa- don haka a cewarsa dukkan abin da ake buƙata an samu na cire dokar ta ta-ɓaci.

Asalin hoton, AMINU DAURAWA/FACEBOOK
A jihar Kano, hukumar Hisba ta sanar da cewa ta warware korafe-korafe ko rigingimu tsakanin ma’aurata har dari shida da ashirin da daya cikin shekara daya.
Mutuwar aure gagarumar matsala ce da ke shafar mutane, kama daga matan da ake saki da mazan da ‘ya’yan, sanadiyyar wani sabani ko rashin jituwa.
Wannan dalili ne yasa hukumar ta HISBA ta ke kokarin sulhunta ma’aurata don su ci gaba da rayuwa cikin fahimtar juna tare da ‘ya’yansu.

Asalin hoton, National Emergency Management Agency (NEMA) Nigeria
Hukumomi a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce mutum ɗaya ya rasu, sannan an ceto wasu daga haɗarin kwale-kwale da ya auku a jihar.
Haɗarin ya auku ne a ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Shagari, inda fasinjojin cikin kwale-kwalen da dama suka ɓace kafin a bazama neman su.
Mai taimaka wa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu a hukumar agajin gaggawa ta jihar SEMA, Aminu Bodinga ne ya tabbatar wa tashar Channels ta faruwar lamari.
Rahotanni sun ce a sanadiyar agajin gaggawa ta hukumar NEMA da SEMA ta jihar da sauran takwaororinsu tare da haɗin gwiwa ƴan garin ne aka samu nasarar ciro gawar wani mai shekara 29.
Haka kuma an samu nasarar ceto mutum, a daidai lokacin da ake ci gaba da neman wata dattijuwa mai shekara 80.
Wannan kifewar kwale-kwalen ita ce ta uku da aka yi a jihar Sokoto a cikin mako biyu bayan na ƙauyen Kojiyo da ke ƙaramar hukumar Goronyo da kuma wanda ya auku a ƙauyen Garin-Faji da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar harkokin wajan Amurka ta tabattar da soke bisa shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da wasu jami'ai Faalasdinawa 80.
Wannan mataki dai zai hana Mahamoud Abbas hallatar taron koli na MDD da za a yi a watan Gobe a birnin Washington na Amurka.
A taron ne dai aka yi tunanin kasashe da dama sun anniyar amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai ƴanci, wanda shi ne babban burin mutanen yankin.
Isra'ila ta dage kai da fata cewa bai kamata a ba Falasɗinu ƴanci zama cikakkiyar ƙasa, kuma tana samun goyon bayan Amurka.

A yau Asabar ne mutanen jihar Rivers suka fito domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar guda 23.
Jihar mai arzikin man fetur na da akwatunan zaɓe guda 6,866 a mazaɓu 319, inda za a zaɓe domin maye gurbin shugabannin da kotun ƙolin Najeriya ta sauke.
Kimanin wata shida da suka gabata ne kotun ƙoli ta yanke hukuncin soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka yi a ranar 5a ga watan Oktoban shekarar 2024, wanda hukumar zaɓen jihar RSIEC ta shirya.
A wancan lokacin zaɓen ya ɗauki hankali ne kasancewar Ministan Abuja, kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya ja daga da dakataccen gwamnan jihar, Sim Fubara, wanda a ƙarshe gwamnan ya tsayar da ƴantakara a jam'iyyar APP, sannan suka lashe ƙananan hukumomi 22 cikin 23, lamarin da ɓangaren Wike suka nuna rashin jin daɗinsu a kai.
Ɓangaren Wike ne suka shigar da ƙarar ƙalubalantar zaɓen, inda aka yi ta shari'a har aka kai kotun ƙoli, wadda ta soke zaɓe.
A zaɓen na yanzu, alamu na nuna akwai wani shiri tsakanin manyan jam'iyyu na APC da PDP, inda ƴan takara uku ne kawai PDP ke da su wato Dr. Gift Worlu mai takarar ƙaramar hukumar Obio/Akpor da Allwell Ihunda na binrin Fatakwal sai Chukwu Ogbogu na Ogba/Egbema/Ndoni.
Amma sauran ƙananan hukumomin guda 20 ƴan APC ne suka tsaya duk da cewa akwai wasu ƙananan jam'iyyun da suka shiga zaɓen.
Har yanzu dai jihar na ƙarƙashin mulkin riƙon ƙwarya ne, bayan Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaƙa ba dokar ta-ɓaci a jihar saboda rikice-rikicen da suka dabaibaye ta.

Asalin hoton, NPF
Shugabannin al'umma sun jagoranci sulhu da wasu jagororin ƴanbindiga, inda a ranar Alhamis da ta gabata aka rattaba hannu a yarjejeniyar sasanci da ƴanbindigar da suke addabar ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.
An shiga sasancin ne domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da garkuwa da mutane da satar dabbobi da sauran su a yankin.
Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi da shugaban ƙaramar hukumar Kurfi, Babangida Abdullahi Kurfi ne suka jagoranci zaman sasancin a dajin Wurma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Daga cikin jagororin ƴanbindiga da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da Alhaji Shu’aibu.
Sun amince za su ajiye makami, sannan za su saki waɗanda suka yi garkuwa da su, kuma suka yi alƙawarin manoma za su koma gona.
Kurfi ta zama ƙaramar hukuma ta biyar da suka shiga yarjejeniyar sasanci da ƴanbindiga a Katsina bayan Jibia da Batsari da Safana da Danmusa.

Asalin hoton, Getty Images
Babban sakatare a Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kadu kwarai da gaske da yadda fada ke kara kazanta a yammacin Darfur na kasar Sudan, inda aka kashe gomman mutane a kwanakin baya bayannan.
Antonio Guterres, ya yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta a El Fasher, inda ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnati da kuma mayakan RSF.
Kafar yada labaran Sudan ta ce gwabzawar da aka yi a jiya Jumma'a abar tashin hankali ce saboda mayakan RSF sun yi amfani da jirage marasa matuka a kokarin da suke na kwace ikon filin jirgin saman da ke birnin.
Likitocin da ke yankin na fama da karancin kayan aiki da magungunan da za su rinka bawa wadanda wannan rikici ke shafa. El Fasher na karkashin kawanya fiye da shekara guda.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya fusata kwarai da gaske a game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke cewa wasu daga cikin manufofinsa na haraji sun saba wa ka'ida, inda ya ce idan har aka kyale hukuncin kotun ya yi aiki to ko shakka babu zai lalata Amurka.
Kotun ta yanke hukunci cewa shugaba Trump ya kawo wasu manufofi da suka sabawa ka'idawa domin kakaba wa kasashe abokan kasuwancin Amurka harajin babu gaira babu dalili.
Hukuncin kotun bai shafi haraje harajen da aka sanya wanda ke kan ka'ida ba kamar harajin da aka sanya akan karafa da wasu kayayyaki da ake shiga da su cikin kasar.
Wakilin BBC ya ce wannan dai wani koma baya ne ga shugaba Donald Trump, sai dai hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke bai kawo karshen manufofin harajin nasa ba wanda zai ci gaba da aiki har zuwa tsakiyar watan Oktoba domin wannna zai ba shi damar daukaka kara a kotun kolin kasar.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC.
A yau za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kamar yadda muka saba a kullum.
Ku kasance tare da mu.