Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Ahmad Bawage da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Harin da Ukraine ta kai a Rasha ya kashe mutum biyu

    Gwamnan yankin Moscow ta ce mutum na biyu ya mutu sakamakon hare-haren jirage maras matuƙa a cikin dare da Ukraine ta kai birnin.

    Andrei Vorobyev ya ce mutumin ɗan shekara 50 ya mutu ne a asibiti, inda ya ce kuma akwai wasu mutum biyu na kwance a asibitin ɗauke da munanan raunuka.

    Tun da farko kafar yaɗa labaran Rasha ta ce wani mutum mai shekara 38 da ke aikin gadi a wani filin ajiyar motoci ya mutu sanadiyyar harin.

  2. Hotunan hare-haren da Ukraine ta kai a Moscow

    Ga wasu daga cikin hotunan ɓarnar da harin da Ukraine ta ƙaddamar kan Rasha ya yi a wani ɓangare na babban birnin ƙasar, Moscow.

    At least two person has been killed and three injured in the drone attack on Moscow, officials say

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hukumomi a Rasha sun tabbatar da cewa yanzu haka kimanin mutum biyu ne suka mutu sanadiyyar hare-haren na jirage marasa matuƙa.
    The drone attack appears to be the largest that Ukraine has launched so far

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ana ganin cewa wannan shi ne hari mafi girma da Ukraine ta ƙaddamar kan Rasha ya zuwa yanzu
    The attack comes ahead of a meeting of US and Ukrainian officials in Saudi Arabia

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Harin na zuwa ne gabanin tattaunawar da za ta gudana tsakanin jami'an gwamnatin Ukraine da na Amurka a Saudiyya domin nemo hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
  3. Kalli bidiyon ɓarnar da harin Ukraine ya yi a birnin Moscow na Rasha

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  4. Ukraine ta kai gagarumin hari kan birnin Moscow

    Ukraine

    Asalin hoton, Governor Andrei Vorobyov/Reuters

    Ukraine ta kai hari kan birnin Moscow da sanyin safiyar yau Talata.

    Wannan na ɗaya daga cikin hare-hare mafi girma na jiragen yaƙi mara matuƙa da Ukraine ta kai kan Moscow tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙasasehn biyu.

    Magajin garin Moscow Sergei Sobyanin ya ce an harbo jiragen sama marasa matuƙa aƙalla 60 a lokacin da suke tunkarar birnin.

    Harin ya tilasta rufe biyu daga cikin manyan filayen jiragen saman Moscow.

    Ya zuwa yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.

    Wannan harin ya biyo bayan wasu munanan hare-hare da makamai masu linzami da Rasha ta kai kan garuruwan Ukraine.

  5. Jami’an Amurka da na Ukraine za su gana a Saudiyya a yau Talata

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami’an Amurka da na Ukraine za su gana a kasar Saudiyya a yau Talata domin tattaunawa da nufin ɗinke alakar da ke tsakaninsu da kuma tabbatar da ko Ukraine na shirin yin sulhu domin kawo karshen yaki da Rasha.

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio - wanda ke jagorantar tawagar Amurka - ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Kyiv a shirye ta ke ta amince da shirin shugaba Trump na tsagaita wuta cikin gaggawa.

    Ya ce ba za a iya cimma tsagaita wuta da kawo karshen wannan yaki ba sai dai idan ɓangarorin biyu sun sassauta.

    Shi ma shugaba Zelensky yana a Saudiyya, duk da cewa ba a sa ran zai taka wata rawa a tattaunawar ba.

  6. Budewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata. Barkanku da shigowa shafinmu na kai tsaye inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram da YouTube domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da kuma muhawara kan labaran da mu ka wallafa.

    Ku kasance tare da mu.