Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/07/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Hotunan yadda Real Madrid ta gabatar da Endrick

  3. Dakarun RSF sun kaddamar da sabbin hare-hare a birnin El-Fashir - rahotanni

    Rahotanni daga Sudan na cewa dakarun RSF sun kaddamar da sabbin hare-hare a birnin El-Fashir da suka yi wa kawanya.

    Mazauna birnin sun ce an yi ta harba makaman atilari da ruwan bama-bamai da safiyar yau Asabar, kuma sama da mutum 20 ne suka mutu.

    El Fashir dai shi ne birni na karshe da ke yankin Darfur da ya rage a hannun sojojin gwamnatin shugaba Abdel Fattah Al-Burhan.

    Tun farkon shekarar nan dakarun RSF karkashin jagorancin janar Muhammad Hamdan Dagalo ko Hemeti, ke fafatawa domin karɓe El-Fashir.

    Birnin ya kuma kasance wurin mafaka ga 'yan gudun hijirar da yakin basasar Sudan ya raba da muhallansu.

  4. Firaministan Habasha ya ziyarci yankin da aka samu zaftarewar ƙasa

    Zaftarewar ƙasa

    Asalin hoton, Amensisa Ifa

    Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ziyarci yankin da aka samu mummunar zaftarewar ƙasa da ya afka wa ƙasar, wanda ya hallaka sama da mutum 250 ranar Litinin.

    Abiy ya yi magana da iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, waɗanda ke kusa da wurin, yayin da jami'ai ke ci gaba da neman gawawwaki.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce adadin waɗanda suka mutu a yankin na Gofa da ke kudancin Habasha, zai iya ƙaruwa zuwa 500.

    Habasha ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a faɗin ƙasar, inda aka sauke tutoci zuwa ƙasa.

  5. Ban samu wasikar cewa masu zanga-zanga za su yi amfani da Eagle Square ba - Wike

    Wike

    Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ya ce har yanzu bai samu wasika kan buƙatar amfani da dandalin Eagle Square ba domin yin zanga-zanga da aka shirya fara wa ranar 1 ga watan Agusta.

    Wike ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a babban birnin tarayya ranar Asabar, gabanin fara zanga-zangar wadda aka yi wa lakabi da "Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa".

    Ya ce babu wata wasika da aka aika wa ofishinsa na buƙatar amfani da dandalin na Eagle.

    Ministan ya ce masu niyyar yin zanga-zanga kada su yi amfani da kafafen sada zumunta kawai wajen aika sako zuwa ofishinsa. Ya ba su shawarar cewa su bi hanyoyi da suka kamata wajen yin hakan.

    Tun da farko, Wike ya yi gargaɗi kan yin zanga-zangar.

    "Ga waɗanda ke son yin zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta, babu wurin yin hakan a babban birnin tarayya," in ji shi.

    Ya kuma gargaɗi masu shirya zanga-zangar da su guji yin hakan.

  6. Mutum tara sun mutu a hari kan yankin tuddan Golan na Isra'ila - rahotanni

    Hari

    Asalin hoton, EPA

    Aƙalla mutum tara ne suka mutu bayan da aka kai wani harin roka a filin kwallo a yankin tuddan Golan wanda Isra'ila ta mamaye, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.

    Ma'aikatar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce wani roka da aka harba ya faɗa kan Majdal Shams da ke yankin.

    Yawancin waɗanda suka jikkata sun kasance yara da kuma matasa.

    IDF ta ɗora alhakin kai harin kan ƙungiyar Hezbollah, sai dai Mohamed Afif, shugaban ofishin yaɗa labarai na ƙungiyar, ya musanta hannu a kai harin a Majdel Shams da ke arewacin Isra'ila.

    Sojojin Isra'ila da Hezbollah na artabu da juna a kan iyaka tun bayan fara yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas a watan Oktoban bara.

  7. Mutum uku sun mutu a ruftawar gini a Jigawa

    Umar Namadi

    Asalin hoton, Namadi/Facebook

    Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku, bayan da gini ya rufta kansu a karamar hukumar Taura da ke jihar.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce lamarin ya afku ne yau Asabar a garin Gujungu.

    "Da misalin karfe 10 na safe muka samu kiran waya, inda ake faɗa mana cewa wani gini mai ya rufta. Nan da nan muka garzaya zuwa wajen, inda muka samu ginin mai hawa biyu a ƙasa," in ji sanarwar.

    Sun ce ba a kammala aikin ginin ba lokacin da ya rufta.

    "Mutum uku ne suka rasa ransu nan take bayan ruftwar ginin," in ji ƴan sandan.

    An kuma samu jikkatar wasu mutum huɗu waɗanda dukkansu suka fito daga karamar hukumar Ungogo na jihar Kano, inda a yanzu ake ci gaba da yi musu jinya a asibitin Jahun.

    Ƴansandan sun ƙara da cewa an ɗauki gawawwakin mutane da suka rasu zuwa asibitin.

    Kwamishinan ƴan sandan jihar CP AT Abdullahi, ya miƙa sakon ta'azziyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu a lamarin, tare da addu'ar Allah ya gafarta musu.

  8. Me ya sa ƴan Najeriya ke son fita zanga-zanga, duk da kamen da ake yi?

  9. Endrick ya sharɓi kuka lokacin da Real Madrid ta gabatar da shi

    Endrick

    Asalin hoton, Real Madrid FC

    Real Madrid ta gabatar da Endrick a gaban magoya baya ranar Asabar a Santiago Bernabeu, wanda ya ɓarke da kuka.

    Ya ce dalilin kukan shi ne ''Tun ina ɗan yaro na ke mai goyon bayan Real Madrid, yanzu kuma na zama ɗan kwallon ƙungiyar.''

    Filin ya ɗauki magoya baya da yawa har da ƴan Brazil da dama, waɗande ke dauke da rigar kasar da kuma ta ƙungiyar Palmeiras.

    Fitattun tsoffin ƴan wasan Real Madrid sun halarci bikin tare da iyayen Endrick, haka shima mahaifin ɗan wasan, Douglas Ramos ya sha kuka a lokacin da zai zauna a kan kujera.

  10. Harin Isra'ila ya kashe Falasɗinawa 30 a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar lafiya a Gaza karkashin ikon Hamas ta ce an kashe mutane aƙalla 30, an kuma jikkata sama da 100, a wani hari da Isra'ila ta kai wata makaranta ɗauke da ɗaruruwan Falasɗinawa da aka ɗaiɗaita.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne kan cibiyar Hamas da ke cikin ginin makarantar a yammacin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

    Tun da farko, sojojin sun yi gargaɗin cewa dole ta sa za a rage kwashe mutane a kusa da birnin Kha Younis saboda ƙaruwar barazanar mayaka da kuma harin rokoki.

    Ita ma ma'aikatar tsaron Isra'ila (IDF) ta yi irin wannan gargaɗi a makon da ya gabata.

  11. Gane Mini Hanya tare da gwamnan Yobe

    A makon jiya ne, hukumomi a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya suka ce, sun ɓullo da shirin bunƙasa kiwon awaki ga mata zalla kuma kyauta, a wani mataki na haɓaka kiwo da sana’o’in dogaro da kai tsakanin mata.

    A ƙarƙashin shirin za a bai wa mace ɗaya akuya biyu da ɗan taure ɗaya wanda ake fatan cikin wata shida za su iya haifar ‘ya’ya.

    A filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, gwamnan jihar Mai Mala Buni ya yi bayanin cewa matakin na ɗaya daga cikin shirin bunƙasa noma da kiwo ta hanyar bayar da tallafin kayan aikin noma da suka haɗa da tantan ko tarakta da iri da kuma maganin ƙwari.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  12. Netanyahu ya ce Isra'ila za ta halarci taron tsagaita wuta kan yaƙin Gaza

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce zai aika wakilai zuwa birnin Rum na Italiya, domin halartar taron tattauna batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

    Mista Netanyahu ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da tsohon shugaban Amurka, kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a jam'iyyar Republican, Donald Trump a wata ziyara da yake yi a Amurkan.

    Furucin firaministan Isra'ilan na zuwa ne kwana guda bayan tattauna batun tsagaita wutar yaƙin a ganawarsa da shugaba Biden da wadda ke fatan yi wa jam'iyyar Demokrats takarar shuagabancin ƙasar, Kamala Harris.

    Gwamnatin Biden ta ce Isra'ila da Amurka na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin.

    Misis Harris ta ce ba za ta yi ''shiru'' game da batun ba, ganin yadda mazauna Gaza ke ''wahala'', inda ta yi kira ga duka ɓangarorin biyu su cimma matsaya.

  13. Sanata Ifeanyi Ubah ya rasu

    ..

    Asalin hoton, Senator Ifanyi Ubah/ Facebook

    Ɗan majalisar dattawan Najeriya mai wakilitar Anambra da Kudu Ifeanyi Uba ya rasu.

    Cikin wata sanarwar da mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon. Benjamin Kalu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya kaɗu da mutuwar Sanatan.

    Rahotonni sun ce marigayin ya rasu ne a Birtaniya kwana biyu bayan wata tafiya da ya yi zuwa ƙasar domin a duba lafiyarsa.

    A shekarar da ta gabata ne Sanata Ifeanyi Ubah ya fice daga jam'iyyarsa ta YPP zuwa APC mai mulkin ƙasar.

    Mutuwar ɗan majalisar na zuwa ne kwana biyu bayan rasuwar shugaban ƙungiyar kare muradun 'yan ƙabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, Chief Emmanuel Iwuanyanwu.

    Tuni shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigarin da kuma gwamnatin jihar Anambra kan rasuwar sanatan da ya bayyana a matsayin ''jajirtacce''.

  14. An soke jigilar wasu jiragen ƙasa a Faransa bayan hari kan layin dogon

    .

    Asalin hoton, SHUTTERSTOCK

    An soke uku daga cikin layin dogo 10 mafi gudu a Faransa ranar Asabar, bayan da wasu mahara suka ƙaddamar da hari kan layin dogon ƙasar ranar Juma'a gabanin bikin buɗe gasar Olympics a birnin Paris.

    Firaministan ƙasar,Gabriel Attal ya ce jami'an tsaro na ci gaba farautar maharan layin dogon da ya kira da ''masu zagon ƙasa'', da ke neman gurgunta sufurin jiragen ƙasa a Faransa, a daidai lokacin da aka fi buƙatar amfani da jiragen.

    Hukumar sufurrin jiragen ƙasa ta ƙasar, ta ce za a jinkirta amfani da wasu layin dogon da ke kai wa da komowa zuwa birnin Paris a ranar Asabar da kusan sa'a biyu, yayin da za a soke kashi ɗaya cikin huɗu na jiragen da ke jigila tsakanin ƙasashen nahiyar Turai.

    Ministan sufurin ƙasar, ya ce zuwa ranar Litinin komai zai daidaita duka titinan jiragen za su koma aiki.

    A ranar Juma'a ne dai wasu mutane da ba a san kosu wane ne ba suka kai hari kan wasu titunan layin dogon, inda suka cinna wuta tare da yanke wasu muhimman wayoyin layin dogo, gabanin bikin buɗe gasar Olympics a birnin Paris.

    Kawo yanzu babu wata ƙungiya ko wasu gungu da suka ɗauki alhakin harin, sai dai hukumomi na ci gaba da bincike.

    Wata majiya mai alaƙa da binciken da ta shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, AFP cewa maharan sun ''shirya'' sosai kafin su ƙaddamar da harin

  15. Gwamnatin Jigawa za ta haɗa hannu da Saudiyya don inganta makarantun allo

    ..

    Asalin hoton, Umar Namadi/X

    Gwamnatin jihar Jigawa za ta haɗa hannu da gidauniyar 'Alfurqan Qur'anic' ta ƙasar Saudiyya don inganta makarantun tsangaya da ke faɗin jihar.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce an cimma hakan ne bayan wata ziyara da shugaban gidauniyar, Sheikh Abdalla Ibn Nasir Al-Utaibiy, ya kai wa gwamnan jihar, Mallam Umar Namadi ranar Juma'a a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse.

    Sheikh Al-Utaibiy, ya ce manufar haɗin gwiwar shi ne zamanantar da hanyoyin karatun allo domin sauƙaƙa hanyoyin koyon karatun da kuma haddar Al-qur'anin mai tsarki.

    Ya ƙara da cewa gidauniyarsa ta ƙware wajen amfani da hanyoyin zamani na koyon karatun alqur'ani da kuma sauƙaƙa koyar da shi ga masu lalurar ji (kurame) da ƙananan yara.

    Jihar Jigawa na daga cikin jihohin ƙasar da ake tura ƙananan yara makarantun Allo na gargajiya da ake kira 'almajirci' domin samun ilimin alqur'ani.

    Wasu iyayen kan tura yaran zuwa makarantun tsangayar ba tare da tanadar musu abincin da za su ci ba, inda a wasu lokutan yaran kan ƙare a bin gidajen mutane da kasuwanni da kan tituna suna barar abincin da za su ci

    Wani abu da masana da gwamnatoci ke ganin rashin dacewarsa, suna masu fargabar hakan ka iya jefa rayuwar ƙananan yaran cikin hatsari.

    A nasa ɓangare gwamnan jihar jigawa, Mallam Umar Namadi ya ce gwamnatinsa na gudanar da wasu tsare-tsare don inganta makarantun tsangayar da ke faɗin jihar, ta hanyar haɗa wa yaran da ilimin boko da koya musu sana'o'in da za su dogara da kansu.

    Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta gina manyan makarantun tsangaya na zamani a shiyoyin jihar uku, da nufin samar wa jihar malaman qur'ani masu ƙwarewar sana'o'in hannu, sannan suke da wayewa ta fannin ilimin boko.

  16. Abu biyar da muke so masu zanga-zanga su gabatar mana kafin fara ta - 'Yansanda

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Police/X

    Yayin da wasu 'yan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa ranar 1 ga watan Agusta, rundunar 'yan sandan ƙasar ta buƙaci masu shiga zanga-zangar su gabatar mata da sunaye da cikakkun bayanansu.

    Babban Sifeton 'yansandan ƙasar, Koyode Egbetokun ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja bababn birnin ƙasar.

    Ya ƙara da cewa duk ƙungiyoyin da ke da muradin shiga zanga-zangar su gabatar da sunaye da cikakkun bayanansu ga kwamishinonin 'yansandan jihohin da suke.

    Mista Egbetokun ya ce rundunar ta ɗauki matakin ne don tabbatar da an yi zanga-zangar cikin kwanciyar hankali da lumana.

    “Za mu tabbatar da 'yancin da kundin tsarin mulki ya bai wa 'yan Najeriya na taruwa don gudanar da zanga-zangar lumana,” in ji shi.

    “Domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, muna kira ga duka ƙungiyoyin da ke sha'awar shiga zanga-zangar, su gabatar da cikakkun bayanansu da kwamishinonin 'yansandan jihohin da za su yi zanga-zangar''.

    Bayanan da Babban Sifeton 'Yansandan ya buƙaci masu son shiga zanga-zangar su gabatar sun haɗa da:

    • Wurin da za su taru da hanyoyin da za su bi.
    • Lokacin da suke tunanin za su ɗauka suna yi
    • Sunaye da lambobin wayar jagororin da suka shirya zanga-zangar.
    • Matakan hana shigar ɓata-gari cikin zanga-zangar.
    • Gano waɗanda za su iya tayar da fitana a lokacinta.
  17. Donald Trump ya caccaki Kamala Harris

    .

    Asalin hoton, .

    Ɗan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya caccaki Kamala Harris da ake kyautata zaton za ta zama 'yar takarar jam'iyyar demokrats a wajen taron kiristoci masu ra'ayin riƙau.

    Yayin da yke jawabi a wajen taron a jihar Florida, mista Trump ya bayyana wadda alamu ke nuna za ta zama abokiyar karawarsa a zaɓen watan Nuwamba da cewa ba ta cancanta ba.

    Ya ce a matsayinta ta mataimakiyar shugaban ƙasa ''a gwamnatin da ta gaza'' - ta kasa taɓuka komai, inda miliyoyin baƙin haure suka tsallaka kan iyaka.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa goyon bayan da Trump ke samu ya ragu, tun bayan janyewar Joe Biden tare da mara wa Kamala Harris baya a makon da ya gabata.

  18. 'Mu yi amfani da ƙuri’a don sauya shugabanni maimakon zanga-zanga'

    ..

    Asalin hoton, Rabi'u Kwankwaso/X

    Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya yi kira ga 'yan ƙasar da ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da su yi amfani da ƙuri'arsu wajen sauya shugabannin, maimaikon fitowa zanga-zangar.

    Kwankwaso ya ce ƙasar ta tsinci kanta a halin matsin rayuwa da take ciki ne sakamakon kasa ɗaukar matakan da suka dace da jagororin ƙasar suka yi tun a shekarar 2007.

    Cikin wata sanarwa da jagoran Kwankwasiyyar ya fitar ya ce har yanzu lokaci bai ƙure ba, na yadda za a farfaɗo da ƙasar da samar wa al'umma abubuwan ci-gaba da na walwala.

    Ya ci gaba da cewa hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar samar da shugabanci nagari, da bin doka da kyakkyawan tsari da yin abubuwa yadda suka dace.

    ''Abin takaici ne yadda halayen shugabanninmu na rashin iya mulki suka jefa ƙasarmu musamman matasa cikin yunwa da rashin tsaro da fusata ta yadda har wasu daga cikinsu suka fara yanke ƙauna game da gyaruwar ƙasarmu'', in ji Kwankwaso.

    Wasu matasan Najeriyar na shirin gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu kan halin matsi da tsadar rayuwa da sauran matsalolin da al'ummar ƙasar ke fuskanta.

    To sai dai Kwankwaso ya zargi gwmnatin tarayya da hannu a haifar da wasu matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

    ''Sa bakin gwamnatin tarayya a batun sarautar Kano, da tsige mataimakin gwamnan Edo da rikicin siyasar jihar Rivers da yi wa matatar mai ta Dangote zagon-ƙasa, da ce-ce-ce-ku-cen da yarjejeniyar SAMOA ta haifar, da rikici tsakanin Sanata Ali Ndume da APC, da rashin tsaro da sauran miyagun laifukan da za a iya kauce musu na daga cikin misalan abubuwan da suka haifar da matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan'', in ji Kwankwaso.

    Jagoran NNPP ya ce duk da cewa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwar, hanya ce da matasan za su nuna wa shugabbanni damuwarsu, amma ya ce yana da kyau matasan da ke shirin gudanar da zanga-zangar su sanya muradun ƙasar a gaba fiye da komai.

    Ya kira ga matasan ƙasar su zama masu haƙuri da gwamnatin, ta hanyar ba ta duk wata dama da goyon baya domin ta cimma nasara.

    ''A ƙarshe duk shugabannin da suka gaza, muna da dama a matsayinmu na 'yan ƙasa mu yi amfani da ƙuri'unmu, don zaɓar wasu da muke ganin za su kawo mana ci gaban da muke buƙata'', in ji shi.

    Kwankwason ya kuma yi kira ga masu shirin gudanar da zanga-zangar su yi la'akari abin da zanga-zangar za ta iya janyo wa ƙasar, don haka ya ce su haɗa kansu wuri guda cikin lumana su yi amfani da ƙuri'unsu don kawo wa ƙasar sauyi ta hanyar zaɓar shugabannin da suka cancanta.

    ''Duk da cewa tsarin dimokraɗiyya ya bayar da damar zanga-zanga, a wasu lokuta tana zuwa da wasu matsaloli, a baya mun ga yadda munanan abubuwa suka faru sakamakon zanga-zanga, inda har aka kai ga tashe-tashen hankulan da suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi''.

    Ya ƙara da cewa idan irin wannan abu ya sake faruwa, babu abin da zai haifar wa Najeriya sai ƙarin matsalolin rikicin ƙabilu da rarrabuwar kawuna.

  19. “Yawan hada-hada ba zai hana ku yin digiri a ABU ba”

    Kwalejin Karatu daga Nesa ta Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ta ce tana bunƙasa ayyukanta don bai wa ɗumbin masu sha’awar zurfafa ilminsu damar samun karatun digiri na ɗaya ko na biyu, ba tare da sun zauna a aji ba.

    Daraktan kwalejin, Professor Aliyu Yahaya ya ce duk yawan hada-hada ko uzurin sana’a ko aikin mutum, kuma a ko’ina mutam yake, hakan ba zai hana shi damar ci gaba da karatu ba a Kwalejin Karatu daga Nesa ta ABU.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  20. Mutumin da ya kashe tarin baƙaƙen fata a Afirka ta Kudu ya mutu

    ..

    Ɗaya daga cikin fitattun waɗanda suka kashe mutane da yawa a Afirka ta Kudu ya mutu.

    Louis van Schoor ya hallaka aƙalla bakar fata 39 manya maza da yara a tsakanin shekara ta 1986 da 1989.

    Jerin kisan da Louis van Schoor, wanda aka fi sani da laƙabin, The Apartheid Killer, ya yi sun kasance ne a birnin East London na kasar ta Afirka ta Kudu, inda a lokacin yake aiki a matsayin mai gadi wanda ba na hukuma ko gwamnati ba.

    A 1991 an kama Van Choor, aka gurfanar da shi gaban shari'a, inda aka same shi da laifin kisan kai bakwai kawai, aka kuma ɗaure shi, to amma daga baya an sake shi bisa dalilai na nuna halayya ta gari, bayan shekara 12 a gidan kaso.

    Har yanzu kisa aƙalla 32 da ya yi a wajen hukumomin ‘yansanda na ƙasar ya yi su ne bisa dacewa da doka.

    To amma wani rahoto da BBC ta yi ya nuna tababa sosai a kan abin da hukumomin ‘yansandan suka ayyana a matsayin dacewa na waɗannan kashe-kashe da ya yi ta hanyar harbe mutanen.

    Rahoton na BBC ya ƙunshi doguwar tattaunawa da aka yi da shi Van Schoor, inda ya bayyana abin da ya yi a matsayin mai ban sha’awa, a wani lokacin kuma yake bayyana abin da farauta, inda kuma ya yi zargi da dama a kan sanya hannun ‘yansanda a abubuwan da ya yi a shekarun na 1989.