Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/07/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Mutum uku sun mutu, 30 sun maƙale bayan ruftawar mahaƙar ma'adinai a Ghana

    ...

    Hukumomi a kudancin Ghana sun ci gaba da aikin ceton masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da ake fargabar sun makale a ƙarƙashin wata mahaƙa da ta rufta a ranar Laraba.

    An tabbatar da mutuwar mutum uku, yayin da wani mutum guda ke kwance a asibitin cikin mawuyacin hali, bayan ruftawar mahaƙar da ke ƙauyen Akyem Wenchi a gundumar Denkyembour a yankin gabas.

    Jami'ai sun ce ana fargabar akwai mutum 30 da suka maƙale bayan ruftawar mahaƙar.

    Kawo yanzu ba a san dalilin da ya haifar da ruftawar mahaƙar ba.

    Jami'an tsaro sun fice daga yankin, bayan da wasu fusatattun matasa da mazauna yankin suka mamaye mahaƙar a lokacin da ake aikin ceton.

    Taswirar yankin da ramin haƙar ma'adanai ya rufta kan mutane a Ghana
    Bayanan hoto, Taswirar yankin da ramin haƙar ma'adanai ya rufta kan mutane a Ghana

    Shugaban yankin, wanda kuma shi ne shugaban majalisar tsaron yankin, Umar Ahmed ya ce ''hayaniyar mutane ce ta hana tawagar ceton ci gaba da aikinsu''.

    “Dole mu bar yankin, saboda ya zama babu tsaro ga ma'aikatan namu, musamman lokacin da fusatattun matasan suka isa yankin suna rera waƙoƙi.''

    Umar Ahmed ya shaida wa kafofin yaɗa labaran ƙasar cewa ji yayi kamar yana cikin barazana, don haka ya fice daga yankin don kare kansa.

    Ƴansanda a yankin Akwatia sun jima suna fama da masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a yankin.

  2. Dele Momodu ya fice daga PDP zuwa ADC

    Dele Momodu

    Asalin hoton, Dele Momodu/Facebook

    Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon gogaggen ɗanjaridar nan na Najeriya, Dele Momodu ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa sabuwar haɗakar ADC ta 'yan hamayya.

    Momodu - wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasar - ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda wasu da ya kira ''masu yaƙi da dimokraɗiyya'' suka hana jam'iyyar numfashi.

    Cikin wasiƙar ficewar tasa da ya aike wa shugaban jam'iyyar na mazaɓarsa ta Ihievbe a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, ranar Alhamis 17 ga watan Yuli, fitaccen ɗansiyasar ya ce dole ce ta sa ya ɗauki matakin domin maido da martabar dimokraɗiyya.

    “Dalilina a bayyane yake, wasu masu yaƙi da dimokraɗiyya sun maƙure jam'iyyar daga ciki da wajen jam'iyyar'', kamar yadda wani sashe na wasiƙar ya nuna.

  3. Gobara ta halaka aƙalla mutum 50 a Iraƙi

    Jami'an lafiyar Iraƙi sun ce wata gobara da ta tashi a wani kataren kanti ta kashe aƙalla mutum 50.

    Gobarar ta tashi a kantin - da ke birnin Kut da ke gabashin ƙasar - ranar Laraba a kantin da aka buɗe kwanaki biyar da suka gabata.

    Bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe saman ginin.

    Gwamnan lardin Wasit, inda gobarar ta auku, Mohammed al-Miyahi ya ce mafi yawan waɗanda suka mutu mata ne da ƙananan yara.

    Rahotonni sun ce yanzu haka an shawo kan gobarar, tuni gwamnan yankin ya ce an ɗauki matakin shari'a kan wanda ya mallaki kantin.

  4. Bayan addu'ar uku za mu koma Katsina don ci gaba da karɓar gaisuwa - Radda

    Gwamnan Katsina

    Asalin hoton, Umaru Dikko Radda/X

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ce bayan kammala addu'ar uku a gidan tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari da ke Daura, shi da tawagar gwamnatin tarayya za su koma gidan gwamnatin Katsina domin ci gaba da karɓar gaisuwa daga baƙi masu zuwa.

    Cikin wata hira da BBC, Gwamna Radda ya ce iyalan tsohon shugaban ƙasar za su ci gaba da zama a gidansa da ke Daura domin ci gaba da karɓar gaisuwa daga masoya da dangi.

    ''Amma mu za mu koma koma gidan gwamnati tare da tawagar gwamnatin tarayya, inda za mu shafe tsawon mako guda muna karɓar gaisuwa daga baƙin da za su zo'', in ji shi.

    Tawagar gwamnatin tarayya da ke Daura ta ƙunshi ministoci kusan 22, ƙarƙashin jagorancin babban sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.

  5. Shugaban Syria ya zargi Isra'ila da kai munanan hare-hare a ƙasarsa

    .

    Asalin hoton, .

    Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya zargi Isra'ila da kai munanan hare-hare kan fararen hula da gine-ginen gwamnatin ƙasarsa.

    Isra'ila ta ce sojojin Syria sun kai hari kan fararen hula ƴan al'ummar Druze a birnin Sweida.

    A jiya Laraba Isra'ilar ta kai hare-hare ta sama kan ma'aikatar tsaro da fadar shugaban ƙasar Syria.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce jami’an diflomasiyyarsa sun kwashe tsawon dare suna aiki domin warware rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Mista Rubio ya ƙara da cewa ''wannan lamari ne mai cike da sarƙaƙiya, da aka daɗe ana yinsa tsakanin ɓangarori daban daban kuma hakan ya janyo matsalar rashin fahimta tsakanin Syria da Isra'ila amma muna fatan nan bada jimawa ba za a shawo kan lamarin''.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu domin samun sahihan labarai