Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 27/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 27/11/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Amurka ta dakatar da shigar ƴan Afghanistan ƙasar bayan an harbi wasu jami'an tsaro

    jami'an tsaron tarayya na Amurka

    Maaikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta dakatar da duba buƙatar duk wasu takardu na ƴan Afghanistan na shiga ƙasar har sai abin da hali ya yi, bayan da aka harbi wasu jamian tsaro na tarayya biyu a Washington.

    Shugaba Trump ya ce mutumin da ake zargi da kai harin ɗan Afghanistan ne da ya shiga kasar a 2021.

    An bai wa Dubban ƴan Afghanistan da suka yi aiki da Amurka wata kariya ta musamman ta zama a Amurka bayan da Amurka ta janye daga ƙasarsu kuma suka faɗa yanayi na ramuwar gayya daga Taliban.

  2. Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu

    ..

    Jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne da asubahin ranar Alhamis.

    Malamin ya rasu ne a wani asibiti da ke jihar Bauchi.sakamakon ƴar gajeriyar jinya.

    Majiyoyi daga iyalansa sun ce za a yi jana'izar shehin malamin ne a ranar Juma'ah.

    Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya rayu tsawon shekaru 100 a duniya, inda ya rasu ya bar ƴaƴa da jikoki masu yawa.

    Cikakken labari kan rayuwar malamin na nan tafe..........ku kasance da mu..

  3. Maraba

    Masu bibiyar shafin BBC hausa na kai-tsaye, barkanku da safiyar yau Alhamis.

    A yau ma shafin namu zai mayar da hankali ne kan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook, Instagram, youtube da kuma X, inda muke wallafa muku bidiyo.