Palace ta kawo karshen wasa tara ba tare da nasara ba a Premier League, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Ismaila Sarr ne ya ci wa Crystal Palace ƙwallon da ya ba ta maki ukun da take bukata a gidan Brighton a wasan mako na 25 a Premier League ranar Lahadi.
Kenan ƙungiyar Selhurst Park ta kawo karshen wasa tara ba tare da nasara ba daga ciki ta yi canjaras uku aka doke ta shida daga ciki.
Rabon da Palace ta ci wasa tun da ta doke Shelbourne a Conference League ranar 11 ga watan Disambar 2025 – lokacin tana cikin ƴan hudun farko, yanzu ta hada maki 32 tana kuma ta 13 a teburi da tazarar maki daya tsakani da Brighton ta 14.




