Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 08 zuwa 13 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 08 zuwa 13 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Palace ta kawo karshen wasa tara ba tare da nasara ba a Premier League, Premier League

    Ismaila Sarr ne ya ci wa Crystal Palace ƙwallon da ya ba ta maki ukun da take bukata a gidan Brighton a wasan mako na 25 a Premier League ranar Lahadi.

    Kenan ƙungiyar Selhurst Park ta kawo karshen wasa tara ba tare da nasara ba daga ciki ta yi canjaras uku aka doke ta shida daga ciki.

    Rabon da Palace ta ci wasa tun da ta doke Shelbourne a Conference League ranar 11 ga watan Disambar 2025 – lokacin tana cikin ƴan hudun farko, yanzu ta hada maki 32 tana kuma ta 13 a teburi da tazarar maki daya tsakani da Brighton ta 14.

  2. , Daga Jaridu

    Real Madrid na matsa kaimi kan ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri mai shekaru 29, ko da yake ɗan wasan Spain din na da sauran watanni 18 a kwantiraginsa. (Teamtalk)

    Arsenal na sha'awar kawo ɗan wasan tsakiya na Bayern Munich Leon Goretzka a kyauta a lokacin bazara, inda rahotanni suka ce Gunners ɗin sun yi ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan ɗan ƙasar Jamus mai shekaru 31 a watan Janairu. (Mirror)

    An danganta kocin Paris St-Germain Luis Enrique da karbar ragamar horar da Manchester United, amma dan kasar Spain din bai yarda cewa wannan aikin ne da ya dace da shi ba, kuma yana shirin sanya hannu kan wani sabon kwantaragi da kungiyarsa ta Faransa. (Mirror)

    Manchester United da Newcastle sun shiga cikin jerin kungiyoyin da ke neman dan wasan baya na Brentford da Italiya mai shekaru 21 Michael Kayode, mai shekaru 21. (Teamtalk)

  3. Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki huɗu a La Liga, La Liga mako na 23

    Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin La Liga da tazarar maki huɗu, bayan da ta doke Real Mallorca 3-0 ranar Asabar a Nou Camp.

    Ta ci ƙwallayen ta hannun Robert Lewandowski da Lamine Yamal da kuma Marc Bernal.

    Wannan nasarar ta kara sa matsi ga Real Madrid, wadda za ta fuskani Valencia ranar Lahadi a wasan mako na 23 a La Liga.

    Ranar Litinin Barcelona za ta je Ginona ranar Litinin 16 ga watan Fabariru, amma kafin nan za ta buga daf da karshe a Copa del Rel da Atletico Madrid ranar Alhamis.

    Ita kuwa Mallorca, wadda ke mataki ta 15 a kasan teburi, za ta karɓi bakuncin Real Betis a wasan gaba ranar 15 ga watan Fabrairu.

  4. Sabon ɗan wasan Liverpool, Jacquet ya ji rauni, Liverpool

    Sabon ɗan wasan da Liverpool ta saya, Jeremy Jacquet, zai shafe lokaci yana jinya, bayan da ya ji rauni a kafada lokacin da yake buga wa Rennes tamaula.

    Ɗan wasan tawagar Faransa mai shekaru 20, wanda ya amince zai koma Anfield da taka leda kan kuɗi fam miliyan 60 a makon da ya gabata, zai koma Liverpool ne a karshen kakar bana.

    Ya ji rauni ne a wasan da Rennes ta sha kashi 3-1 a hannun Lens a Ligue 1 ranar Asabar, haka shima Abdelhamid Ait Boudlal ya ji ciwo a fafatawar.

    Liverpool ta ɗauki Jacquet ne a lokacin kasuwar saye da sayar da ƴan wasa a watan Janairu, bayan yarjejeniyar ɗaukar mai tsaron bayan Crystal Palace, Marc Guehi, ta rushe a bara.

    Chelsea ma ta nuna sha’awar sayen Jacquet, wanda ya buga wasa biyar a tawagar Faransa ta ƴan kasa da shekara 21, kuma kocin Liverpool Arne Slot ya bayyana shi a matsayin matashi ne mai ƙwazo.

  5. Real Madrid ta ziyarci Valencia a wasan mako na 23 a La Liga, La Liga mako na 23

    Valencia ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 23 a La Liga da za su kara ranar Hahadi.

    Real Madrid tana ta biyu a teburi da maki 54 da tazarar huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama.

    Ita kuwa Valencia tana ta 17 a kasan teburin La Liga da maki 23 da tazarar maki ɗaya tsakani da Rayo Vallecano, wadda take ta 18 cikin ƴan ukun karshe.

    A wasan farko a bana da suka kara cikin Nuwambar 2025, Real ce ta ci 4-0 a Santiago Bernabeu.

    Kylian Mbappe ne ya ci biyu a karawar da kuma Jude Bellingham da Alvaro Carreras.

    Ƴan wasan Real Madrid da za su fuskanci Valanci:

    Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Sergio Mestre.Masu tsare baya: Carvajal, Alaba, Trent, Asencio, Carreras, Fran García, Rüdiger, Huijsen da kuma David Jiménez.Masu buga tsakiya: Camavinga, Valverde, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos da kuma Cestero.Masu cin ƙwallaye: Mbappé, Gonzalo, Brahim da kuma Mastantuono.

  6. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.