Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/10/20224

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Badriyya Tijjani Kalarawi

  1. 'Sun kwashe komai na gidana tare da ɗaiɗaita garinmu'

    Ƙasar Sudan na fama da mummunan yanayin yaƙi da ya ta'azzara ayyukan jin ƙai, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, yayin da wasu da dama ke fuskantar barazanar faɗawa ƙangin yunwa.

    Wannan na zuwa ne sakamakon yaƙin basasa da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF tun cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata.

    Babban birnin ƙasar, Khartoum, inda yaƙin ya soma ɓarkewa, har yanzu na fuskantar musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

    Karon farko tun bayan fara yaƙin wakilin BBC, Mohanad Hashim ya je ƙasar inda ya ziyarci gidansa da na dangi domin ganin halin da Omdurman bayan jerin munanan hare-hare.

  2. An naɗa Kithure Kindiki a matsayin sabon mataimakin shugaban Kenya

    Shugaba William Ruto na Kenya ya sanar da naɗa Farfesa Kithure Kindiki a matsayin sabon mataimakin shugaban ƙasar.

    Ya maye gurbin Rigathi Gachagua wqanda majalisar dattawan ƙasar ta tsige a jiya Alhamis.

    Sanarwar naɗin ta fito ne daga bakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, a lokacin wani zama don amince da sabon mataimakin shugaban ƙasar.

    Kundin tsarin mulkin Kenya ya bai wa shugaban ƙasa wa'adin kwanaki 14 da ya maye gurbin wanda aka tsige da kuma ƙarin watanni biyu kafin majalisa ta kaɗa kuri'a a kai.

    Sai dai ana ganin za a amince da dukkan matakai a zama na yau.

    Hakan na zuwa ne awanni bayan da sanatocin kasar suka amince da zarge-zarge biyar cikin 11 da ake zargin Mista Gachagua, wanda ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa.

  3. Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutu a fashewar tankar fetur a Jigawa ya kai 170

    Gwamnan jihar Jigawa ta ce mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar mai sun ƙaru zuwa 170.

    Gwamnan jihar Malam Umar Namadi shi ya bayyana wa BBC hakan, inda ya ce ƙarin wadanda suka rasun masu jinya ne a asibiti, waɗanda tuni ‘yan'uwansu suka ɗauki gawawwakin tare da yi musu sutura.

    Malam Namadi ya ce akwai ƙarin mutane 76 da suke kwance a asibitocin jihar da na birnin Nguru na jihar Yobe mai makobtaka.

    Hatsarin ya faru ne ranar Talata da daddare a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura na jihar ta Jigawa.

  4. Sojoji sun kama wasu ma'aurata da zargin haɗa-kai da ƴan bindiga a Taraba

    Dakarun shiyya ta shida na rundunar sojin Najeriya a jihar Taraba sun ce sun cafke wasu mutum uku waɗanda ake zargi da haɗa-kai da ƴan bindiga wajen aikata laifi, ciki har da wasu ma'aurata.

    Mai magana da yawun shiyya ta shida na rundunar sojin, Kaftin Oni Olubo, ya ce an kama mutanen ne a ƙauyen Lande Jessey da ke karamar hukumar Lau na jihar.

    Ya ce sun yi nasarar kama mutanen ne a wani samame da suka kai bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu.

    A cewarsa, waɗanda ake zargin su uku sun haɗa da Ahijo Sulaiman da Abdulrahman Isah da kuma Aisha Mohammed.

    Kaftin Oni ya bayyana cewa yayin bincike, sun gano cewa ana amfani da gidan ma'auratan biyu cikin mutanen da aka kama wajen ɓoye maƙamai na ƴan bindiga.

    "Sojojin Najeriya na da zimmar kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma, da kuma kare yankunan ƙasa," in ji Oni.

    Ya buƙaci al'umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga jami'an tsaro a kan lokaci a ƙoƙari da suke yi wajen kakkaɓe ayyukan ta'addanci da kuma rashin tsaro d aya addabi ƙasar.

  5. Za mu ci gaba da kai farmaki Gaza da Lebanon - IDF

    Dakarun tsaron Isra'ila sun ce za su ci gaba da kai farmaki Gaza da kuma Lebanon.

    Sun ce wasu dakaru sun faɗaɗa tare da kai farmaki cikin dare a yankin Jabalia da ke arewacin Gaza.

    IDF ɗin ta ci gaba da cewa sojojinta da kuma jiragen sama sun hallaka gomman waɗanda ta kira ƴan ta'adda a hare-haren da suka kai a yankin a cikin kwana guda.

    Sanarwar da suka fitar ta ce suna ci gaba da gano maɓoyar ƴan ta'dda tare da lalata maƙamansu a kudancin Lebanon.

  6. Netanyahu zai jagoranci taro kan tsaro bayan kashe shugaban Hamas

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila na ruwaito cewa Firaministan ƙasar Benjamin Netanyah, zai jagoranci wani taro kan tsaro a yau Juma'a, bayan kashe shugaban Hamas Yahya Sinwar.

    Za a gudanar da taron da misalin karfe 11 na safe a hedkwatar sojojin Kirya da ke Tel Aviv.

    Ministoci da jami'an tsaro za su mayar da hankali kan ci gaban da ake samu a tattaunawar sakin waɗanda ake garkuwa da su a Gaza, in ji rahotanni.

  7. Janye tsare-tsaren Tinubu zai kawo cikas ga Najeriya - Bankin Duniya

    Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa muddin gwamnatin tarayya ta janye tsare-tsaren tattalin arziki da ta fara, to hakan zai iya janyo babbar cikas ga Najeriya.

    Babban wakilin bankin a Najeriya, Dr Ndiame Diop, shi ya yi wannan gargaɗi ranar Alhamis a Abuja yayin kaddamar da wani rahoto kan 'Cigaban Najeriya da kuma ɗorewarta' a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsaloli.

    Diop ya ce dole ne a ɓullo da tsare-tsaren domin ɗorewar Najeriya, duk da cewa za su janyo tsadar rayuwa da kuma wahalhalu ga ƴan ƙasar.

    "Janye waɗannan tsare-tsare zai jefa Najeriya cikin barazana da kuma tawayar tattalin arziki," in ji Diop.

    Ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ta samu a watannin farko na wannan shekara ya faru ne sakamakon cire tallafin man fetur da na kuma na canjin kuɗin waje, inda ya ce hakan ya nuna dole ne a ci gaba da tsare-tsaren.

    Tun a lokacin rantsuwar kama aiki ne, shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, abin da ya jefa ƴan Najeriya da dama cikin kunci da wahalhalu musamman ma masu karamin karfi.

  8. MDD ta yi Alla-wadai da harin Isra'ila kan wata makaranta a Gaza

    Hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (Unrwa), ta yi Alla-wadai da harin da Isra'ila ta kai ta sama kan wata makaranta da ke ɗauke da 'yan gudun hijira a Jabalia da ke arewacin Zirin.

    Mataimakiyar daraktan Unrwa, Sam Rose, ta shaida wa shirin BBC cewa lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 28, a yankin da mata da ƙananan yara ke zaman mafaka.

    Rundunar sojin Isra'ila a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce an kai harin ne kan 'yan ta'addar Hamas da na ƙungiyar Islamic Jihad, waɗanda ke gudanar da ayyukansu daga cikin makarantar Abu Hussein.

    Rose ta ce dole ne Isra’ila ta kara kaimi wajen kare fararen hula saboda ba su da wurin zuwa, kuma hakan na ɗaya daga cikin jerin abubuwan da suka shafi makarantun Unwra.

    Da aka tambaye ta ko ta yarda cewa mayaƙan Hamas na amfani da gine-ginen makarantar, ta ce ko da hakan gaskiya ne bai kamata a far wa fararen hula ba, inda ta yi kira da a gudanar da bincike kan abin da ya faru.

  9. Da sauran rina a kaba duk da kashe shugaban Hamas - Isra'ila

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce mutuwar shugaban Hamas, Yahya Sinwar, a ranar Laraba, ba ta nufin kawo karshen yaƙin Gaza.

    Mutumin wanda aka yi imanin shi ne ya kitsa harin 7 ga watan Oktoba da ya janyo mutuwar sama da mutum 1,200 a Isra'ila, ya mutu ne sakamakon farmakin da sojojin Isra'ila suka kai masa a Rafah da ke kudancin yankin.

    Mista Netanyahu ya ce mutuwar Sinwar za ta sa haske ya mamaye duhu a gabas ta tsakiya.

    Sai dai ya dage cewa Isra'ila za ta ci gaba da fafatawa da dukkan karfinta har sai ta ceto yan ƙasar da Hamas ke riƙe da su.

    Zuwa yanzu dai babu wani martani daga ƙungiyar ta Hamas game da wannan batu.

  10. Isra'ila ta fitar da bidiyon lokaci na karshe kafin kashe Yahya Sinwar

    Sojojin Isra'ila sun fitar da faifan bidiyo da ke nuna shugaban ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar a mintunan karshe kafin halaka shi.

    Bidiyon wanda wani jirgin sama mara matuki ya naɗa ya nuna wani mutum zaune da rauni a kan kujera, riƙe da itace a tsakiyar wani rusasshen gini, yayin da ya rufe fuskarsa da tutar Falasɗinu.

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya ce an kashe ƙarin wasu mutane biyu a farmakin.

    Mista Hagari ya ce dakarunsu za su ci gaba da bibiyar sauran shugabannin ƙungiyar Hamas da nufin kawo karshensu.

  11. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj Babbar Rana.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.