Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan majalisar wakilan Najeriya sun ba wa Tinubu wa'adin mako biyu
Majalisar wakilan Najeriya ta bai wa shugaba ƙasar Bola Ahmed Tinubu wa'adin mako biyu da ya gabatar mata da kasafin kuɗin shekara mai zuwa ta 2025.
Ƴan majalisar sun kuma nemi Bola Tinubun da ya saki kuɗi ga ma'aikatu da hukumomin kasar, yadda ya kamata, don aiwatar da kasafin kuɗin shekarar da muke ciki ta 2024, da ta tasar wa ƙarewa.
Wa'adi da yan Majalsiar wakilan suka bai wa shugaba Bola Tinubun na zuwa ne a yayin da shugaban na Najeriya ke hutu a kasar Faransa, ya yin da shi kuma mataimakin shugaban ƙasar ya tafi wata ziyarar aiki Sweden.
Haka kuma Majalisar wakilan Najeriyar ta buƙaci shugaba ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ya yi aiki da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasar, kan kasafin kudi nan da makwanni biyu masu zuwa.
Hwanarable Kabiru Alasan Rurum ɗan majalisar wakilai daga jihar Kano, ya ce kawo kasafin kuɗi a kan lokaci na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, kuma jinkirta shi na illata tattalin arziki, don haka wannan na daga cikin dalilan da suka sa Majalisar ta buƙaci a gabatar musu da kasafin 2025 cikin makonni biyun.
Haka kuma Rurum ya ce ƙudurin ya umarci da a ci gaba da hanzarta aiwatar da kasafin kudin na 2024, wanda a cewarsa ''Yawancin ma’aikatu da hukumomi ga kasafin kuɗi an amince da shi, amma har yanzu ba a sakar masu kudaden da za su aiwatar da shi ba, kuma ga shekara ta zo ƙarshe"
Sai dai dan Majalisar ya ce baya jin sati biyun da suka bayar zai cika ba tare da an fara aiwartar da wannan kuduri ba, ganin yadda aka sami sauyi idan majalisa ta yi magana shugaban kasar na saurara, don haka a jira wa’adi ya cika tukun in yaso sai a ga wane mataki majalisar za ta ɗauka.
Me Bangaren gwamnatin ke cewa?
Ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban na Najeriya kan harkokin watsa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce da alama ƴan majalisar basu yi bincike ba kan lamarin, kafin ɗaukar wannan mataki.
“Ina ga kamar yan majalisa basu su yi zuzzurfan bincike ba kan wannan batu kafin kai shi gaban majalisa ba, akwai wani sabon tsari da aka samar kan yadda ake fitar da kuɗaɗen da ake aiwatarwa, da zai tabbatar da cewar ba a yi almundahana ko bayar da kwangilolin bogi ba yadda aka saba yi a baya. In ji shi
Abdulaziz Abdulaziz din ya kuma ce har yanzu akwai sauran lokaci, na gabatar da kasafin kudin, kuma ya tabbatar da cewar, da zarar an kammala za a kai kasafin gaban majalisar kamar dai yadda aka saba.
A ƙarshen watan Disamba mai zuwa ne dai ake sa ran kasafin kuɗin na Najeriya na bana na 2024 zai kare aiki, wanda hakan ke nufin a yanzu bai wuce wata biyu da mako biyu ba aikinsa ya ƙare kenan, wanda kuma daga nan za a fuskanci sabon kasafin kuɗin na baɗi na 2025.