Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/10/20224

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Badriyya Tijjani Kalarawi

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnan Rivers ya amince da mafi ƙarancin albashin N85,000

    Gwamnatin jihar Rivers ta sanar da amincewa da mafi ƙarancin albashin naira 85,000 ga ma'aikatan jihar.

    Shugaban ma'aikatan jihar, George Nwaeke ne ya sanar da cewa gwmnan jihar, Sim Fubara ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin ne a wani taron da ya wakana tsakanin ɓangaren gwamnatin da ƙungiyar ƙwadago na jihar, kamar yadda Channels ta ruwaito.

    Nwaeke ya ce mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba.

    A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin tattaunawar, Chukwu Emecheta, yaba wa gwamna Fubara ya yi bisa amincewa da buƙatar ma'aikatan jihar.

    Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙungiyar kwadago na jihar Rivers, Alex Agwanwor, ya ce mafi ƙarancin albashin zai rage da ma'aikatan jihar raɗaɗin tsadar rayuwa da ake ciki.

  3. Fashwar tankar mai a Jigawa: "Muna tsaye a gefe kawai sai muka ji boom"

    Har yanzu jama'a na ci gaba da bayyana yadda fashewar tankar mai a jihar Jigawa ta yi sanadiyyar rasuwar ɗaruruwan mutane a jihar.

  4. Biden ya gana da shugaban Jamus a kan yaƙin Ukraine da Gabas ta Tsakiya

    Shugaban Amuka Joe Biden ya gana da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, a Berlin, domin tattauna batun yaƙin da ake yi a Ukraine da kuma Gabas ta Tsakiya.

    Tun farko, Mista Biden ya ce tattaunawarsu za ta duba batun ƙara ƙoƙari wajen taimakawa Ukraine a yaƙin da take da mamayar da sojojin Rasha ke mata.

    Biden ya kuma kira kisan da aka yi wa shugaban Hamas, Yahya Sinwar a Gaza a matsayin wani lokaci da aka yi adalci, to amma ya bayyana fatan cewa lokaci ne kuma da za a duba yiwuwar samun zaman lafiya a yankin.

    Daga bisani shugabannin biyu za su haɗu da firaiministan Burtaniya Keir Starmer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.

  5. Isra'ila ta buƙaci fararen hula su tashi daga yankunan da take hare-hare a Lebanon

    Rundunar sojin Isra'ila ta yi kiran da a kara samar da ƙarin gada a arewacin ƙasar a yayinda take ƙara zafafa hare-harenta a kan Hezbollah da ke Lebanon.

    Rundunar ta kuma fitar da sanarwar buƙatar a cigaba da kwashe mutane a yankin tare da gargaɗin mazauna yankunan da ta ke kai hare-hare a kudancin Lebanon da su bar gidajensu su nufi arewaci.

    A nata ɓangaren, Hezbollah ta ce tana ƙara tunkarar abin da ta kira wani sabon babi a yaƙin da suke yi.

  6. An rufe makarantu a Punjab saboda zanga-zangar ɗalibai

    Hukumomi a lardin Punjab na ƙasar Pakistan sun bada umarnin rufe dukkan cibiyoyin ilimi a yau saboda zanga-zangar da ɗalibai suka yi domin nuna adawa da cin zarafin mata.

    An soma zanga-zangar ce a Lahore bayan da aka samu rahoton an yi wa wata ɗaliba fyaɗe a cikin makaranta a lokacin hutun ƙarshen mako.

  7. Ƙwararrun direbobi ne kawai za su riƙa tuƙa tankokin mai –Minista

    Minista a ma'aikatar albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya ce gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin tsara wasu dokoki domin tabbatar da cewa ƙwararrun direbobi ne kawai za su riƙa tuƙa tankokin mai, sannan za a riƙa duba motocin sosai kafin a ba su dama suka riƙa jigilar albarkatun man fetur a ƙasar.

    Ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje garin Majia da ke ƙaramar hukumar Taura da ke jihar Jigawa bayan fashewar tankar mai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ya ce, "ina ƙara kira ga ƴan Najeriya da cewa duk lokacin da suka ga irin wannan matsalar ta auku, su yi gaggawar sanar da ƴansanda ko wasu jami'an tsaro domin a tsare wurin domin hana mutane zuwa.

    "A ɓangaren gwamnati muna ƙoƙarin tsara wasu dokoki domin hana sake aukuwar lamarin. Tun daga tabbatar da ƙwararrun direbobi ne suke jigilar man, sannan dole motoci su kasance suna cikin hayyacinsu," in ji shi.

    "Don haka za mu ɗauki namu matakan a matsayin gwamnati, mutane ma suna da rawar da za su taka."

  8. Hezbollah ta harba makamai masu linzami sama da 70 a Isra'ila - IDF

    Rundunar tsaron Isra'ila, IDF ta ce Hezbollah ta harba makamai masu linzami 75 daga Lebanon zuwa Isra'ila.

    A cikin ƴan awannin da suka gabata, Hezbollah ta ce ta harba wasu rokoki zuwa arewacin Haifa da ke cikin Isra'ila.

    A ɗaya gefen kuma, tashar talabijin ta NNA na gwamnatin ƙasar Lebanon ta ruwaito cewa an kai hare-hare ta sama a garuruwan Anqoun da Maaroub da Taraya da ke kudancin ƙasar da yammacin yau.

  9. Ƙungiyar NURTW ta gargaɗi masu safarar makamai a motocin sufuri

    A Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, ƙungiyar direbobin motocin haya ta NURTW a jihar ce ta yi gargaɗi a kan yadda ake ƙara samun mutanan da take kamawa da ke suke safarar makamai ta hanyar amfani da motocin sufuri.

    Ƙungiyar ta sanar da cewa a lokuta da dama ƴaƴanta sun sha kama masu ɗauke da bindigogi samfarin AK47 a ɓoye cikin kaya a babbar tashar motar garin Gusau babban birnin jihar.

  10. Bai kamata a yi jimamin rasuwar Sinwar ba - Firaministan Burtaniya

    Firaministan Burtaniya, Keir Starmer ya ce, "babu wanda ya kamata ya yi jimamin rasuwar shugaban Hamas Yahya Sinwar."

    Starmer ya bayyana haka ne a Berlin, inda ya ce, "akwai jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a wuyansa, inda ya kitsa kashe mutane a ranar 7 ga Oktoba, da ma jinin Falasɗinawa waɗanda aka kashe ko suka sha wahala a sanadiyar rikicin da ya jawo."

    Sai dai a game da yaƙin Isra'ila a Gaza, Starmer ya ce ya amince da ƴancin Isra'ila na kare kanta, "amma sulhun diflomasiyya zai fi kyau wajen kawo ƙarshen yaƙin."

    "Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mu yi kira da tsagaita wuta, da kuma sakin waɗanda ake garkuwa da su a Gaza, sannan a fara kai kayayyakin agaji zuwa Gaza, sannan a fara tattauna yiwuwar samar da ƙasashen biyu ƴantattu," in ji Starmer.

    Da yake gargaɗi ga Isra'ila, Starmer ya ce, "yanzu duniya ba za ta cigaba da karɓar uzuri ba na kawo tsaikon kai kayayyakin agaji."

  11. An samu ƙarin talakawa miliyan 14 a Najeriya a 2024- Bankin duniya

    Bankin duniya ya fitar da rahoton ci gaban Najeriya, inda a ciki ya ce sama da mutum miliyan 129 ne suke zaune cikin talauci a ƙasar.

    A rahoton wanda bankin ya fitar jiya Alhamis a Abuja, ya nuna hauhawan farashin kayayyaki ne ye jefa miliyoyin ƴan ƙasar a cikin yunwa, kamar yadda Channels ta ruwaito.

    Bankin ya ce sama da mutum miliyan 129, ya nuna ƴan ƙasar masu fama da talauci ya ƙaru ne daga kashi 40.1 a shekarar 2018 zuwa kashi 56 a shekarar 2024.

    Rahoton ya ƙara da cewa a shekarar 2023 mutum miliyan 115 ne suke fama da talauci, wanda hakan ke nufin an samu ƙarin mutum miliyan 14 a bana.

  12. Al'ummar musulmin ibo sun taya ɗansu murnar zama limamin babban masallacin ƙasa

    Al'ummar ibo musulmi sun yi murna tare da taya ɗaya daga cikinsu murnar zama limamin babban masallacin ƙasa da ke Abuja.

    Hukumomin masallacin ne suka sanar da naɗa Farfesa Iliyas Usman a matsayin sabon liman a masallacin na ƙasa.

    Usman, wanda farfesan Larabci ne, ɗan asalin ƙabilar Ibo ne, kuma yanzu ya shiga cikin sauran limaman masallacin.

    Sauran limaman su ne Farfesa Ibrahim Maƙari da Farfesa Muhammad Kabir da Sheikh Ahmad Onilewura, waɗanda suke aiki a ƙarƙashin jagorancin murshida, Farfesa Ahmad Sa'id Galadanci.

    Ƙungiyar musulman Kudu maso Gabas sun taya sabon limamin murna, sannan suka yi addu'ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin.

    Ƙungiyar ta South East Muslims Organisation of Nigeria (SEMON) ta ce, "muna taya farfesa Ilyasu Usman murnar zama limamin Masallacin Abuja. Allah ya sa naɗinka ya ƙara haɗa kan al'umma," kamar yadda sanarwar, wadda shugaban ƙungiyar, Dokta Suleiman Afikpo da sakatarensa, Ustaz Sirajuddeen Ugwu suka sanya wa hannu wadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

  13. Gwamnatin Nijar ta ce tana gudanar da aikace-aikace domin jin daɗin al'umarta

    Hukumomin mulkin sojin jumhuriyar Nijar sun sanar da cewa sun gudanar da manyan ayyukan da gyare-gayre tare da ɗaukar matakai domin ƴan ƙasar su gani a ƙasa.

    Gwamnatin ta ce burinta shi ne mutane a birane da ma yankunan karkaran ƙasar baki ɗaya su mori mulkin. Faraministan ƙasar Ali Mahamane Lamine Zeine wanda kuma shi ne ministan ma’aikatar tattalin arzikin ƙasar ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya yi a ƙasar.

  14. Amurka ta tuhumi tsohon jami'in leƙen asirin Indiya da kashe ɗan awaren Sikh

    Amurka ta tuhumi wani tsohon jami'in leƙen asirin Indiya da laifin jagorantar wani shiri da aka yi na kashe wani fitaccen ɗan awaren Sikh a birnin New York a bara.

    Jami'an Amurka sun ce Vikas Yadav na aiki ne da gwamnatin Indiya a lokacin da ake zargin an shirya kutunguilar.

    Ana zargin Mista Yadav da haɗa baki da wani mutum domin kashe Gurpatwant Singh Pannun, ɗan ƙasar Amurka da Canada, wanda ke shugabantar wata ƙungiya ta masu neman kafa ƙasa mai cin gashin kanta ga mabiya addinin Sikh a Indiya.

    An ɗaure ƙarin wani mutum da ake zargi da hannu a shirin Nikhil Gupta, a gidan yarin Brooklyn, inda yake jiran shari'a.

    Matakin na Amurka ya zo ne bayan dambarwar diflomasiya da ta kunno kai tsakanin Canada da Indiya, bayan da hukumomin Canada sun zargi manyan jami'an Indiya da hannu a kisan Hardeep Singh Nijjar, wani ɗan gwagwarmayar Sikh a yankin British Columbia da ke karkashin ikon Canada a 2023.

  15. 'Mun gano Koriya ta Arewa ta tura sojinta don taimakawa Rasha a yaƙi da Ukraine'

    Hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu ta gabatar da wasu hotunan tauraron ɗan'adam da ta ce sun tabbatar da cewa Koriya ta Arewa ta tura sojojinta don su taimakawa Rasha a yaƙin ta da Ukraine.

    Hukumar leƙen asirin ta ce tuni sojoji 1,500 suka isa gabashin Rasha don samun horo.

    Ta ce an tura sojojin ne a cikin wani jirgin ruwan Rasha a farkon watan da muke ciki.

    Hukumar ta ce sojin na Koriya ta Arewa sun sanya kayan sarkin Rasha sannan suna amfani da maƙaman da aka ƙera wa Rasha da nufin bad-da kama.

    A makon da ya gabata, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce an tura sojojin Koriya ta Arewa yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Rasha ta sayi dukkan maƙamanta ne daga Pyonyang don amfani da su a Ukraine, inda hakan ya ba wa Koriya ta Arewa damar samun kuɗaɗen da take buƙata don inganta harkokin maƙamanta.

    Rasha dai ta yi watsi da zarge-zargen tana mai cewa labaran ba su tushe balle.

  16. 'Waɗanda suka mutu a Gaza tun bayan farmakin Isra'ila ya kai 42,500'

    Aƙalla Falasɗinawa 42,500 ne aka kashe sannan aka jikkata wasu 99,546 tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki a Gaza bayan harin ranar 7 ga Oktoba da Hamas ta kai ƙasar, a cewar ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas.

    Ma'aikatar ta ce alkaluman sun kunshi mutum 62 da aka kashe da kuma wasu 300 da aka jikkata cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

  17. Gwamnatin Kebbi ta rufe kwalejin kiwon lafiya a Jega bayan boren ɗalibai

    Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da umarnin rufe kwalejin kiwon lafiya ta Jega, bayan zanga-zanga da ɗalibai suka yi wanda ya rikiɗe zuwa tarzoma.

    Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Isah Abubakar Tunga ne ya sanar da haka ga manema labarai, inda ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi domin kaucewa yaɗuwar rikicin.

    Ɗaliban sun ce sun shiga zanga-zangar ne domin nuna fushinsu kan rashin yi wa wasu kwasa-kwasai rajista, rashin kyawun wurin zama da kuma rashin shugabanci na gari.

    An nuna wasu ɗalibai sun far wa gidan shugaban kwalejin, inda suka cinna wa gidansa wuta da kuma lalata motarsa.

    Tunga ya tabbatar da cewa za a kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.

    Ya kuma ce za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

    Yanzu dai kwalejin zai ci gaba da zama a rufe har na tsawon makonni uku, a cewar gwamnatin jihar.

  18. Biden na ganawa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz

    Shugaba Biden na ganawa da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, a Berlin domin tattauna batun faɗa da ake yi a Ukraine da kuma Gabas ta Tsakiya.

    Mr Biden ya ce tattaunawarsu za ta duba batun ƙara ƙoƙari wajen taimakawa Ukraine a yaƙin da ta ke yi da kuma mamayar da sojojin Rasha ke mata.

    Ya kuma kwatanta kisan da aka yi wa shugaban Hamas, Yahya Sinwar a Gaza a matsayin wani lokaci da aka yi adalci, to amma ya bayyana fatan cewa lokaci ne kuma da za a duba yiwuwar samun zaman lafiya a yankin.

    Daga bisani shugabannin biyu za su haɗu da Firaiministan Birtaniya Keir Starmer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.

  19. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta tabbatar da mutuwar Yahya Sinwar

    Wani babban jami'i a ƙungiyar Hamas ya tabbatar da mutuwar jagoran ƙungiyar, Yahya Sinwar.

    Khalil al-Hayya ya bayyana a cikin wani bidiyo cewa Sinwar ya mutu ne a bakin daga.

    Sinwar ya mutu ne sakamakon farmakin da sojojin Isra'ila suka kai masa a Rafah da ke kudancin Gaza.

  20. Ambaliya: Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi mutane su tashi daga bakin koguna

    Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya (NIHSA), ta ta shawarci ƴan Najeriya da ke zaune a gaɓar tekuna da su bar yankunan cikin gaggawa.

    Darakta-janar na hukumar, Umar Mohammed ne ya yi wannan gargaɗi a wata sanarwa, inda ya ce ruwan da ke tekun Benue ya kai matakin ambaliya saboda ƙaruwar mamakon ruwan sama.

    Ya kuma buƙaci mutanen da ke zaune a gaɓar tekun Neja da su ma su bar yankin, inda ya ce hukumomin madatsun ruwa na Kainji da Jebba na aikin kare afkuwar ambaliya.

    Mohammed ya yi kira ga ƴan Najeriya da su bayar da haɗin-kai ga hukumomin agaji domin ganin an rage barazanar ambaliya.

    A baya-bayan nan, gwamnati ta gargaɗi ƴan Najeriya da su tashi daga wuraren da ke da haɗarin afkawa cikin ambaliya sakamakon sake ruwan madatsar Lagdo daga Kamaru.

    Wannan ya zo ne bayan mummunar ambaliya da aka fuskanta a Maiduguri sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alau wanda ya kashe mutane 37 tare da ɗaiɗaita miliyoyi.