'Ban san yadda na tsira daga hatsarin jirgin da ya kashe fasinjoji fiye da 241 ba'

Asalin hoton, DD News
Vishwashkumar Ramesh, ɗan ƙasar Birtaniya, ne kaɗai wanda ya tsira daga hatsarin jirgin saman Air India da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 241.
Ramesh yana zaune ne a kujerar 11A a cikin jirgin Boeing 787 da ke kan hanyarsa zuwa birnin London.
Gidan talabijin gwamnatin India, DD News, ya yi hira da Ramesh, wanda a halin yanzu yana jinya a asibiti.
“Ban san yadda na tsira daga hatsarin jirgin ba da ya kashe fasinjoji fiya da 241” in ji shi.
“A farkon hatsarin, na yi tunanin zan mutu. Na buɗe idona, na cire bel ɗin kujera sannan na yi ƙoƙarin fita daga cikin jirgin.”
Ramesh ya ce ɓangaren da yake zaune a jirgin bai buge da ginin masaukin ba, kuma yana kusa da bene na ƙasa.
“Kofar wajen da nake zaune ta karye sai na ga ƙaramar sarari, a nan ne nayi ƙoƙarin fita daga cikin jirgin,” in ji shi.
Ya ce ya ga ma’aikatan jirgin da fasinjoji suna mutuwa a gabansa.
Bidiyon da ke nuna Ramesh yana ƙoƙarin tsira daga jirgin da ke ƙonewa ya bazu sosai a intanet.
Ya ce ya ji raunin ƙonewa a hannunsa na hagu kuma an kai shi asibiti da gaggawa cikin motar asibiti.
Da safiyar ranar Juma’a, Firamiinista Narendra Modi ya kai ziyara wurin Ramesh a asibitin gwamnati inda ake kula da shi a yanzu.












