Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/06/2025

Taƙaitattu

  • MDD ta soma taron gaggawa kan rikicin Isra'ila da Iran
  • Rukunin farko na sojojin Afirka ta Kudu sun dawo gida daga Kongo
  • Iran ta harba makamai masu linzami tsakiyar birnin Tel Aviv
  • Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta - Ayatollah
  • 'An samu raguwar shigar da man fetur Najeriya saboda ƙaruwar aikin matatun ƙasar'
  • 'Ban san yadda na tsira daga hatsarin jirgin da ya kashe fasinjoji fiye da 241 ba'
  • Manyan Jami'an Iran biyar da suka mutu a hare-haren Isra'ila
  • Babu hannun Amurka a harin da Isra'ila ta kai wa Iran - Trump
  • Mali ta amince da ƙudurin ƙara wa mulkin soji shekaru biyar
  • Ta yaya za a kwatanta ƙarfin sojin Iran da na Isra'ila?
  • Isra'ila ta kai wa Iran jerin hare-hare da kashe manyan kwamandojinta

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida, Aisha Ja'afar da Usman Minjibir

  1. 'Ban san yadda na tsira daga hatsarin jirgin da ya kashe fasinjoji fiye da 241 ba'

    Vishwashkumar Ramesh, ɗan ƙasar Birtaniya, ne kaɗai wanda ya tsira daga hatsarin jirgin saman Air India da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 241.

    Ramesh yana zaune ne a kujerar 11A a cikin jirgin Boeing 787 da ke kan hanyarsa zuwa birnin London.

    Gidan talabijin gwamnatin India, DD News, ya yi hira da Ramesh, wanda a halin yanzu yana jinya a asibiti.

    “Ban san yadda na tsira daga hatsarin jirgin ba da ya kashe fasinjoji fiya da 241” in ji shi.

    “A farkon hatsarin, na yi tunanin zan mutu. Na buɗe idona, na cire bel ɗin kujera sannan na yi ƙoƙarin fita daga cikin jirgin.”

    Ramesh ya ce ɓangaren da yake zaune a jirgin bai buge da ginin masaukin ba, kuma yana kusa da bene na ƙasa.

    “Kofar wajen da nake zaune ta karye sai na ga ƙaramar sarari, a nan ne nayi ƙoƙarin fita daga cikin jirgin,” in ji shi.

    Ya ce ya ga ma’aikatan jirgin da fasinjoji suna mutuwa a gabansa.

    Bidiyon da ke nuna Ramesh yana ƙoƙarin tsira daga jirgin da ke ƙonewa ya bazu sosai a intanet.

    Ya ce ya ji raunin ƙonewa a hannunsa na hagu kuma an kai shi asibiti da gaggawa cikin motar asibiti.

    Da safiyar ranar Juma’a, Firamiinista Narendra Modi ya kai ziyara wurin Ramesh a asibitin gwamnati inda ake kula da shi a yanzu.

  2. Manyan Jami'an Iran biyar da suka mutu a hare-haren Isra'ila

    Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’, da ta ce ta kaddamar da nufin wargaza shirin nukiliyar Iran, ya kashe manyan jami’an soja da ƙwararru a fannin nukiliyar ƙasar, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran suka ruwaito.

    Ga jerin jami'an da aka tabbatar da mutuwarsu a harin na Isra'ila.

    • Hossein Salami - Babban kwamandan rundunar juyin juya halin ƙasar (IRGC)
    • Gholamali Rashid - Kwamandan hedikwatar Khatam-al Anbiya
    • Fereydoon Abbasi - Ƙwararren masanin nukiliya kuma tsohon shugaban Hukumar Makaman nukiliyar Iran
    • Mohammad Mahdi Tehranchi - Ƙwararren masanin nukiliya, wanda kuma ke da hannu a shirin makaman nukiliyar ƙasar.
    • Mohammad Bagheri - Shugaban ma’aikatan sojin Iran

    Rahotannin kafofin yaɗa labaran Iran sun ce harin Isra'ila ya kuma jikkata Ali Shamkhani, babban mai bai wa shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei shawara.

  3. Hotunan yadda harin Isra'ila ta lalata Tehran, babbar birnin Iran

    Ga wasu hotuna daga Tehran, babban birnin Iran da ke nunu lalacewar da harin Isra'ila ta kai a daren Alhamis ta haddasa.

  4. Farashin man fetur ya tashi bayan hare-haren Isra'ila kan Iran

    Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan da Isra’ila ta tabbatar da kai hari kan Iran, lamarin da ya haifar da ƙaruwar fargabar rikici mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Yan kasuwa da masu zuba jari na nuna damuwa cewa rikici tsakanin Iran da Isra’ila na iya kawo cikas ga fito da man fetur daga wannan yanki mai albarkatun makamashi.

    Farashin man fetur na da tasiri kai-tsaye ga farashin komai, kama daga kayan abinci i zuwa kuɗin sufuri da sauransu.

    Masu nazarin tattalin arziki sun shaida wa BBC cewa ‘yan kasuwa a kasuwar makamashi za su riƙa sanya ido don ganin ko Iran za ta mayar da martani a cikin kwanaki masu zuwa.

  5. Babu hannun Amurka a harin da Isra'ila ta kai wa Iran - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa yana sane da hare-haren da Isra’ila ta kai kan Iran kafin ta kai amma ya jaddada cewa babu hannun Amurka a ciki.

    Trump ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Fox news dangane da hare-haren.

    Ya kuma maimaita cewa yana fatan Iran za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka domin rage barazanar shirinta na makaman nukiliya.

    "Iran ba za ta mallaki bam na nukiliya ba, kuma muna fatan komawa teburin tattaunawa." in ji shi a hirarsa da tashar talabijin na Fox News.

    Ya ƙara da cewa, "Akwai wasu daga cikin shugabannin Iran da ba za su sake dawowa ba," yana nuni da cewa Amurka ta tabbatar da mutuwar wasu shugabannin Iran a harin.

    Trump ya ce gwamnatinsa ta tuntubi wata muhimmiyar ƙasa kawarta a Gabas ta Tsakiya kafin a kai harin don sanar da su, sai dai bai ambaci sunan kasar ba.

  6. Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta - Ayatollah

    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce "Isra'ila ta shirya shan uƙuba" bayan hare-haren da ta ƙaddamar cikin dare kan cibiyoyin nukiliya na Iran da kuma kashe manyan jami'an sojinta.

    Ya ce Isra'ila "ta aikata mummunan laifi a cikin ƙasarmu a yau" kuma dakarunsa "ba za su taɓa bari lamarin ya tafi haka nan kawai ba".

    "Kan wannan laifi, Isra'ila ta tsoma kanta cikin mummunar makoma, kuma za ta girbi abin da ta shuka."

    Rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta ce tuni Iran ta kai mata farmaki da jirage marasa matuƙa sama da 100.

  7. 'An samu raguwar shigar da man fetur Najeriya saboda ƙaruwar aikin matatun ƙasar'

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce kuɗin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu da fiye da naira tiriliyan biyu.

    Cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar ta ce a shekarar da ta gabata daidai wannan lokaci, NAjeriya ta kashe naira tiriliyan 3.81 wajen shigar da man fetur ƙasar.

    NBS ta ce an samu raguwar kashi 54 cikin 100 idan aka kwatantan da shekarar 2024.

    Raguwar ta samu ne sakamakon ƙaruwar samar da man fetur a cikin gida, musamman daga matatar man Dangote,m, a cewar hukumar ta NBS.

    Ƙarin samar da fetur daga matatar Dangote ya rage dogaro da fetur daga kasashen waje, wanda Najeriya ta daɗe tana yi.

    Alƙaluman ƙididdigar shekara biyar da suka gabata sun nuna ƙaruwar shigo da man fetur har zuwa shekarar 2024.

    A zangon farko na 2020, an shigar da fetur na naira biliyan 732 inda ya ƙaru zuwa naira tiriliyan 1.29 a 2021, sannan ya ninka zuwa naira tiriliyan 2.69 a 2022.

    Rahoton ya kuma nuna cewa man fetur shi ne kayan da aka fi shigar da shi daga ƙasashen ECOWAS zuwa Najeriya a zangon farko na 2025, inda ya kai naira biliyan 89.18 - wanda ya kai kaso 44.51 cikin 100 na dukkanin kayayyakin da aka shigar da su daga yankin.

  8. Majalisar ministocin Mali ta amince da ƙudurin ƙara wa mulkin soji shekaru biyar

    Majalisar ministocin Mali ta amince da wani ƙudurin doka mai cike da ce-ce-ku-ce wanda zai bai wa gwamnatin sojin ƙasar ƙarin shekaru biyar a kan mulki.

    Wannan sabon ƙuduri da aka gabatar, wanda har yanzu yana buƙatar amincewar majalisar dokoki ta ƙasar, zai bai wa shugaban mulkin soja na Mali, Janar Assimi Goita, sabon wa’adi daga wannan shekarar har zuwa shekarar 2030.

    Goita dai ya karɓe mulki a juyin mulki a shekarar 2021 inda aƙa naɗa shi shugaban rikon ƙwarya.

    A watan da ya gabata, ya rusa dukkan jam’iyyun siyasa a cikin kasar.

  9. IDF ta ce Iran ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa a kan Isra'ila

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila (IDF), Birgediya Janar Effie Defrin, ya ce Iran ta ƙadammar ta hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙa kusan 100 kan Isra’ila, inda ya ce sojojinsa na ƙoƙarin kakkaɓo su kafin su isa.

    Defrin ya ƙara da cewa an kashe kwamandan dakarun juyin juya halin Iran (IRGC), da kuma kwamandan hukumar agajin gaggawa ta Iran a hare-haren Isra'ila da ta kai a daren jiya.

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an kashe Hossein Salami, babban kwamandan dakarun na IRGC.

    An kuma ayyana dokar ta-ɓaci a Isra’ila, saboda fargabar harin ramuwar gayya daga Iran.

  10. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Juma'atu, babbar rana.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.