"Dakarun RSF sun kashe mutum 14 a sansanin gudun hijira"
Asalin hoton, Getty Images
Masu aikin sa kai a yankin Dafur na ƙasar Sudan sun ce aƙalla mutum 14 ne suka rasu bayan dakarun RSF sun yi luguden wuta a wani sansanin ƴan gudun hijira.
Sansanin na Abu Shouk dama can yana fama da ƙarancin abinci ya daɗe yana fuskantar barazanar hari daga dakarun na RSF a yunƙurinsu na kama birnin El Fashe.
Masu aikin agajin sun ce ƙananan yara na cikin mutanen da aka kashe ɗin, sannan sama da mutum 20 sun jikkata.
Fafaroma Leo ya buƙaci a kawo ƙarshen yaƙi a Ukraine
Asalin hoton, Reuters
Sabon Farafaroma na ɗarikar Katolika, Fafaroma Leo ya gana da wasu shugabannin ƙasashen duniya, ciki har da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Tun da farko bayan rantsar da shi, Fafaroman ya yi kira da a tabbatar da zaman lafiya a Ukraine.
Haka Mr Zelensky ya gana da mataimakin shugaban Amurka, J.D. Vance domin tattaunawa game da wayar tarho da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi Putin na Rasha da kuma yiwuwar ƙaƙaba wa Rasha takunkumi.
Magajin Garin Bucharest ke kan a zaɓen Romania
Asalin hoton, Reuters
Zaɓen jin ra'ayoyin jama'a zagaye na biyu na shugaban ƙasar Romania ya nuna alamun nasara ga Magajin Garin Bucharest mai sassaucin ra'ayi, Nicusor Dan.
Ƙuri'u sun nuna yana gaban ɗan adawa George Simion mai tsattsauran ra'ayi da kashi goma cikin ɗari.
A zaɓen farko Mista Simion ne ya samu nasara.
Nasarar nan za ta kawar da damuwar ƙasashen da ke ƙawance da ƙasar game da goyon bayan da take bai wa Ukraine da ƙungiyar EU.
Ƴanbindiga sun kashe manoma a Kebbi
Asalin hoton, Getty Images
Wasu mahara da ake zargi ƴanbindiga ne sun kai hari a ƙauyen Waje da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi, inda suka kashe manoma 15, sannan suka jikkata mutum uku, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Tafida, wanda ya wakilci gwamnan jihar, Nasir Idris a wajen ta'aziyar rashin, ya bayyana takaicinsa kan kisan, sannan ya sanar da tallafin da gwamnatin jihar za ta ba iyalan waɗanda abun ya shafa.
Hakimin Waje, Bala Danbaba ya yaba da zuwan wakilin gwamnatin jihar, sannan ya yi godiya bisa tallafin rage raɗaɗin da gwamnatin ta bayar.
Ya ce ƙaramar hukumar na da iyaka da jihohin Neja da Zamfara da Sokoto, wanda a cewarsa hakan ya sa take fuskantar hare-hare, sannan ya buƙaci a ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro domin kare kwarorowar mahara jihar.
Shugaban ƙaramar hukumar Danko Wasagu Hussaini Aliyu Benea ne ya tabbatar da cewa kashe musu manoma 15, da kuma jikkata guda uku.
Ƙungiyar ci gaban matasan arewa ta buƙaci ƴan Najeriya su koma ga Allah
Asalin hoton, Others
Ƙungiyar Ci gaban Matasan Arewa ta Arewa Youth Advancement Forum (AYAF) ta ce akwai buƙatar a ƴan Najeriya su koma ga Allah ta hanyar yi wa ƙasar addu'o'i domin samun waraka daga matsalolin da take fuskanta.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwar bayan taro da ta fitar bayan taronta a Abuja a ƙarƙashin shugabancin Mukhtar Sagir Dambatta, inda ta buƙaci ƴan Najeriya su dage da addu'a domin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta, "musamman rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki."
Ƙungiyar ta ce matsalolin da ƙasar ke fuskanta za su faskara matuƙar ba a koma ga Allah ba domin neman taimakonsa da kariyarsa.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ƴan ƙasar baki ɗaya da su bayar da gudunmuwarsu wajen ilimantarwa, "domin da ilimi da aikin taimakon kai da kai da kuma haɗin kai ne za a iya ganowa tare da magance dukkan matsalolin da al'umma suke fuskanta tun kafin su girmama," kamar yadda sanarwar ta nuna.
Amurka ta buƙaci ma'aikatan ofishin jakadancinta na Nijar su riƙa "fita a motoci masu sulke'
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Amurka ta buƙaci ma'aikatan ofishin jakadancinta da ke Jamhuriyar Nijar da duk idan za su fita, su riƙa "fita ne tare da zirga-zirga" a motoci masu sulke.
Amurka ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda ƙaruwar "garkuwa da mutane" kamar yadda cibiyar tsaro ta Wamaps ta bayyana a X.
An yi wannan kashedin bayan rahotannin garkuwa da mutane da aka riƙa samu a ƙasar, inda a kan sace baƙi musamman ƴan ƙasashen waje, lamarin da ake zargin ISWAP da aikatawa, duk da cewa babu ƙungiyar da ta fito ta ɗauki alhali.
Haka kuma Amurka ta shawarci mutanenta da ke ƙasar da su zama masu sa ido musamman a duk lokacin da suka kasance a wuraren da ake zuwa yawon buɗe, kuma su kasance masu rage bayyana kansu.
An kama dattijo mai shekara 80 da miyagun ƙwayoyi a Kaduna
Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru mai shekara 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi.
A wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa Femi Babafemi ya fitar wadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna ne bayan samun bayanan sirri a game da harƙallarsa.
Sanarwar ta ce an taɓa kama Ashirun bisa fataucin miyagun ƙwayoyi, aka ɗaure na shekara goma tsakanin 2014 zuwa 2024.
"Ya ce ya kasance a harƙallar fataucin miyagun ƙwayoyi na tsawon shekara 46," kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami'an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Sunday mai shekara 82 da ƴarta mai shekara 32 mai suna Chisom Uchechi a jihar Abia da miyagun ƙwayoyi.
Ɗan ƙunar bakin-wake ya hallaka mutum goma a Mogadishu
Aƙalla mutum gome ne suka rasa ransu bayan da wani ɗan ƙunar bakin-wake ya tayar da bam a wani sansanin sojoji a Mogadishu, babban birnin Somaliya.
Ƙungiyar Al Shabaab ta ɗauki alhakin kai harin.
Jami'an lafiya a asibitin sojoji sun ce sun karɓi mutum 30 da suka jikkata.
Wani ganau ya bayyana cewa ya ga lokacin da wani mutum ya fita daga cikin a-daidaita sahu ya ruga cikin jama'a sanna ya tayar da bam ɗin.
Shi ma wani shaidan gani da ido ya ce akwai ɗaruruwan matasa a sansanin sojojin.
Mayaƙan Al Shabaab sun sha kai hare-hare kan wuraren da ake ɗaukar sabbin jami'an soji.
Mutum 27 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kwara
Asalin hoton, Getty Images
Mutum 27 ne suka rasu bayan da kwale-kwalensu ya kife a karamar hukumar Kaiama na jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa fasinjojin na kan hanyar su ne ta komawa gida daga kasuwa a jihar Neja, lokacin da jirginsu ya nitse.
Wani da ya tsira daga hatsarin, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon ɗaukar kaya fiye da kima, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.
Ya ce iska mai ƙarfi da ta taso musu - ita ma ta taimaka wajen kifar da kwale-kwalen, duk da cewa bai bayyana adadin mutanen da ke cikin jirgin ba.
Shugaban karamar hukumar ta Kaiama, Abdullahi Danladi, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar don zuwa ta'aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa, ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar samun hatsuran kwale-kwale da ake yi ba a kowace shekara.
Ya sanar da shirin kafa wani kwamitin da zai ɗabbaka saka rigunan kariya da hana tafiye-tafiye cikin dare da kuma aiwatar da sauran matakai na tsaro.
Hatsarin jirgin ruwan na zuwa ne watanni bakwai bayan samun irinsa da ya lakume rayukan mutane 100 a yankin.
'Dukkan asibitoci uku da ke arewacin Gaza sun daina aiki'
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza, ta ce dukkan asibitoci uku da ke arewacin yakin sun daina aiki.
Sojojin Isra'ila sun yi wa ɗaya daga cikinsu da ya rage yana aiki ƙawanya wato asibitin da ke birnin Beit Lahia.
An ruwaito kashe mutum sama da 130 a wasu hare-hare da aka kai cikin dare, duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa a Qatar don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce a shirye yake wajen kawo karshen faɗan, muddin aka sake dukkan ƴan ƙasar da ake garkuwa da su - sannan Hamas ta ajiye makamansu.
Rahotanni daga Doha sun ce ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta ta ƙanƙanin lokaci da ake son cimma wa da kuma sakin waɗanda ake garkuwa da su.
Sojoji sun kama jirgin ruwa ɗauke da gangar mai fiye da 90,000 na sata a Ondo
Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kama wani jirgin ruwa ɗauke lita 90,000 na ɗanye mai da aka sace a tekun Araromi a jihar Ondo.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace ɗanyen man ne a rijiyoyin mai da aka yi watsi da su a yankin Igbokoda na jihar, kuma an nufi da shi jihar Legas kafin jami'an sojin ruwan su samu nasarar ƙwace shi daga hannun ɓarayin.
An gudanar da samamen bin sahun ɓarayin ne ranar Alhamis 15 ga watan Mayu, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu satar ɗanyen mai a yankin.
Da farko, jirgin ruwan ya yi yunkurin tserewa da ya hangi sojojin, kafin a cimma masa.
Jirgin ruwan da ke ɗauke ɗanyen man na sata da kuma abubuwa da aka ƙwato na hannun hukumomi kuma ana ci gaba da bincike.
Shugabannin Turai za su tattauna da Trump kan yaƙin Ukraine
Asalin hoton, Reuters
Shugaban gwamantin Jamus Friedrich Merz, ya ce shi da shugabannin ƙasashen Birtaniya da Faransa da kuma Poland za su tattauna da shugaba Donald Trump na Amurka ranar Litinin - gabanin ganawar Trump ɗin da shugaba Putin.
Mista Merz na magana ne a birnin Rome lokacin da ya haɗu da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.
Da yake bayyana batun tattaunawarsu, Trump ya ce yana son kawo karshen zubar da jini a Ukraine.
Rasha dai ta kaddamar da wani harin jirgi mara matuki mafi muni kan Ukraine a daren jiya, inda wata mata ta rasa ranta sannan mutun uku suka jikkata.
Tinubu zan mara wa baya a zaɓen 2027 - Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce ba zai yi takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 ba, sannan zai mara wa Tinubu baya.
Wike ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da sashen Pidgin na BBC, inda ya ce har yanzu shi ɗan jam'iyyar PDP ne.
"Ba zan sake yin takara ba. Ba zan yi takara da mutumin da nake yi wa aiki ba. Waye zai yi nasara idan ba shi ba?" kamar yadda Wike ya faɗa.
Wike wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers, ya yi takarar zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP don zama ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, sai dai ya yi rashin nasara a hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
Ministan na Abuja ya kuma nuna ɓacin-ransa kan matakin jam'iyyar na kin ware tikitin takarar shugaban ƙasa wa yankin kudu, abin da ya janyo ta faɗa rikici da ya yi mata nakasu a zaɓen da ya gabata.
Wike ya kuma soki wasu jagororin jam'iyyar, sai dai ya ce babu inda zai je yana nan a PDP daram.
Sojojin Isra'ila sun kashe gomman mutane a Gaza, in ji hukumomin lafiya
Asalin hoton, EPA
Hukumomin lafiya a Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun kashe gomman mutane a waasu hare-hare ta sama da suka kai.
Sun ce dukkan asibitoci da ke arewacin Gaza sun daina aiki yanzu.
Wani likita mai suna Hussam Hammouda, ya ce komai ya durkushe a asibtin da yake - hakan ya tilasta masa barin asibitin wanda sojojin Isra'ila suka yi ƙawanya.
Isra'ila dai na ci gaba da yin luguden wuta duk da cewa ana tattaunawar tsagaita wuta a Qatar a halin yanzu.
Rahotanni sun bayyana cewa Hamas ta yi tayin sakin sauran mutanen da take garkuwa da su, inda take son a yi yarjejeniyar tsagaita wuta ta watanni biyu.
Suna kuma son a koma kai agaji da sakin wasu Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.
Gwamnatin Borno ta haramta sare itatuwa ba bisa ka'ida ba
Gwamnatin jihar Borno ta amince da kudurin haramta sare itatuwa ba bisa ka'ida ba a faɗin jihar.
Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da haka ranar Juma'a, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin kare muhalli da inganta lafiyar al'umma.
Haka kuma, gwamnan ya amince da kudurin tsaftace muhalli wanda za a riƙa yin shara a a kowace Asabar ɗin farkon wata a faɗin jihar.
"A don haka, duk wani mutum da aka samu yana sare itatuwa ba bisa ka'ida ba, za a ci tararsa naira 250,000 ko kuma ɗaurin shekara uku a gidan yari. Idan ya sake aikata laifin, hukuncinsa shi ne ɗaurin shekara biyar ko tarar naira 500,000 ko kuma a zartas masa da duka hukuncin," in ji gwamna Zulum.
Gwamnan ya ce waɗanda aka samu ba sa tsaftace muhallinsu za a ci su tarar da ta kai naira 100,000 saboda saɓa wa umarnin da aka kafa na tsaftace muhalli.
Ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin kula da lafiyar al'umma da kuma rage yaɗuwar cutuka tsakanin al'ummomi.
Akwai fargabar dabbobi za su yi tsada lokacin babban sallah a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci a Najeriya, ta ce akwai fargabar dabbobi za su iya yin tsada a lokacin babbar sallah.
Sun ce hakan zai iya faruwa ne saboda takunkumin da gwamnatin Nijar ta saka na haramta fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje.
Ƴan kasuwar sun roki hukumomin Nijar su kalli maslahar al’umma su cire haramcin.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Muhammad Tahir ya shaida wa BBC cewa za a samu koma-baya a harkar sayar da dabbobi.
"Idan gwamnatin Nijar tana ganin matakin da ta ɗauka shi ne zai kawo saukin abubuwa, to gaskiya akwai matsala, saboda ƴan Nijar da ke hada-hadar dabbobin idan ba su samu mai saye ba babban koma-baya ne," in ji shi.
Ya ce akwai shanu da raguna sama da 50,000 waɗanda aka saya daga Chadi, inda yanzu haka suke maƙale a iyakar Chadi da Nijar.
"Gaskiya za a samu matsala. Muddin aka ɗauki tsawon lokaci ba a shigo da dabbobi daga Chadi ko Nijar ba to za a iya samun tashin gwauron zabi na dabbobi a kasuwannin mu. Mu kuma ba mu fatan haka," in ji Dakta Tahir.
Nijar dai na sahun gaba wajen fitar da dabbobi zuwa wasu ƙasashe musamman maƙwabta.
Hukumomin ƙasar sun ce sun ɗauki matakin haramta fitar da dabbobin ne don samar da rahusa a lokacin babban sallah.
Poland na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, wanda zai yanke hukunci kan ko gwamnatin haɗaka ta Donald Tusk za ta kai labari a kudurorinta na sauye-sauye cikin sassauci.
Shugaba mai barin-gado mai ra'ayin mazan jiya, Andrzej Duda, ya sha amfani da karfin kujerarsa wajen datse kudurorin da haɗakar ke gabatarwa, saboda rashin isassun kujeru a majalisa.
Mutum 13 ne ke takara a zaɓen, ciki har da magajin birnin Warsaw Rafal Trzaskowski mai sassaucin ra'ayi da kuma Karol Nawrocki, masanin tarihi.
Yadda aka koma yin hada-hada a Birnin Gwari bayan sulhu da ƴanbindiga
Al'ummar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna na ci gaba da nuna farin ciki dangane da yanayin zaman lafiya da ya koma yankin tun bayan cimma sulhu da ƴanbindiga.
Yanzu haka kasuwanni da sauran wuraren hada-hada na farfaɗowa a yankin, inda kuma mazauna yankin ke fatan ɗorewar zaman lafiyar.
Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
Ƴakin Gaza: Akwai yiwuwar a sake cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
Asalin hoton, Anadolu/Getty Images
Rahotanni na bayyana cewa akwai yiwuwar a sake cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, bayan ganawa tsakanin jami'an Hamas da Isra'ila a Qatar.
Majiyoyin Falasɗinawa sun shaida wa BBC cewa Hamas ta shirya sakin ƙarin mutum tara cikin sauran Israilawan da take riƙe da su - domin musayarsu da wasu fursunonin Falasɗinawa da komawa kai kayan agaji da kuma tsagaita wuta na kwanaki 60.
Tattaunar na zuwa ne bayan gagarumin hari da Isra'ila ta kaddamar a Gaza, a wani yunkuri na son ƙwace iko da wasu yankuna da kuma matsa lamba ga Hamas.
A yau Lahadi ake gudanar da bikin naɗin Fafaroma Leo na 14
Asalin hoton, Getty Images
A yau Lahadi ake gudanar da bikin naɗin Fafaroma Leo na 14, a matsayin Fafaroma - a wani gagarumin taro a fadar Vatican.
Zai soma aikinsa na Fafaroma a hukumance, kwanaki 10 bayan zaɓensa.
Shugabannin addinai na duniya da ƴyan siyasa da kuma sarakuna ne ke halartar bikin naɗin.
Wakilin BBC ya ce dubban mutane sun taru a dandalin St Peters, inda ake sa ran Fafaroma Leo zai yi zagaye a cikin motarsu ta Fafaroma.
Tun bayan sanar da sabon Fafaroma ake kwatanta shi da marigayi Fafaroma Francis, ta fuskar zaman lafiya da adalci.
Leo shi ne Fafaroma na 267 kuma na farko da ya fito daga Amurka.