Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/07/2024.

Taƙaitattu

  • An sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta
  • IMF ta rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya
  • Turkiyya da Nijar suna tattaunawar ƙulla ƙawancen soji da tattalin arziki
  • Gwamnan Kano ya naɗa sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu

Rahoto kai-tsaye

  1. Mahara sun harbe mutum huɗu a masallaci yayin taron Ashura

    'Yan Shia

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansanda a ƙasar Oman sun ce aƙalla mutum hudu ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a harin da aka kai masallacin Wadi al-Kabir da ke kusa da babban birnin ƙasar Muscat.

    Hotunan da aka yaɗa a intenet sun nuna yadda mutane ke ƙoƙarin tserewa daga masallacin da aka bude wa wuta.

    Rahotonni sun ce mutanen sun taru a masallacin ne domin yin taron Ashura, wanda mabiya Shi'a ke yi duk shekara.

    Ba a cika samun irin wannan rikici a Oman ba.

    A gefe guda kuma, Ofishin Jakadancin Amurka ya yi kira ga ƴan ƙasarsa su yi taka tsantsan.

  2. Maraba

    Barkanmu da hantsin Talata, sannunmu da sake haɗuwa a shafin labara kai-tsaye.

    Umar Mikail da Usman Minjibir ne ke fatan za ku biyo mu domin samun rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya