Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/07/2024.

Taƙaitattu

  • An sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta
  • IMF ta rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya
  • Turkiyya da Nijar suna tattaunawar ƙulla ƙawancen soji da tattalin arziki
  • Gwamnan Kano ya naɗa sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu

Rahoto kai-tsaye

  1. Biden zai ci gaba da yaƙin neman zaɓensa

    Joe Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Joe Biden zai ci gaba da yakin neman zabe, bayan yunkurin kashe Donald Trump da aka yi a ranar Asabar lamarin da ya karade kafafan yada labaran Amurka.

    Zai yi jawabi ga taron bakaken fata masu zabe a Nevada, wanda galibi muhimmin wani bangare ne na masu zaben jam’iyyar Democrats, amma yanzu suna nuna alamun rashin kwarin gwiwa ga shugaban da ke neman yin tazarce.

    A nasu bangaren ‘yan jam’iyyar Republican na cikin rana ta biyu ta gudanar da babban taronsu, inda aka amince da takarar Mr Trump a jiya Litinin, bayan da ya sanar da Sanata JD Vance a matsayin wanda zai yi masa mataimaki.

    Biden na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga ƴan Democrats ya janye daga takarar suna bayyana shakku kan tsufa da lafiyarsa.

  2. An gano wani kogo a duniyar wata

    Kogo

    Asalin hoton, NASA

    A karon farko masana kimiyya sun gano wani kogo a duniyar wata.

    Zurfinsa ya kai mita 100, zai iya zama wurin fakewar mutane, a matsayin wani sansani, kamar yadda masanan suka bayyana.

    Sun ce ɗaya ne daga cikin ɗaruruwa da ke ɓoye a duniyar da ba a gano ba.

    Ƙasashe sun daɗe suna lalaben matsuguni a duniyar wata, amma sai sun kare masu bincike daga tururi da tsananin zafi da kuma yanayi na sararin samaniya.

    Helen Sharman, ƴar sama jannati ta farko a Birtaniya ta shaida wa BBC cewa sabon kogon ya yi kama da sansani mai kyau da ɗan'adam zai iya fakewa, tare da cewa mutane za su iya rayuwa tsawon shekara 20 zuwa 30.

    Sai dai ta ce kogon yana da zurfi sosai wanda dole sai ƴan sama jannati sun bi dubaru na yadda za su shiga su fita.

  3. An kama masu safarar hodar iblis da aka ɓoye a cikin ayaba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu karnuna na jami'an tsaro a Ecuador sun gano ton 6,23 na hodar iblis da aka ɓoye cikin ayaba, kamar yadda ƴansanda suka sanar.

    Karnukan ne suka yi jagora ga ƙwace kwalin hodar iblis din guda 5,630 da aka bayyana darajarsu ta kai dala miliyan 224.

    An kama mutum biyar bayan kamen, kamar yadda ofishin mai gabatar da kara ya bayyana.

    Hukumomi sun ce an kama jirgin ruwan wanda ke kan hanyarsa zuwa Jamus, kuma an ɓoye hodar iblis din cikin kwandunan ayaba da za a fitar daga ƙasar.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama har da manajan gonar ayaba inda ake zargin daga can aka cusa hodar iblis din domin fataucinta.

  4. Kotu ta yi watsi da buƙatar cire ajami a kuɗin Najeriya

    Takardun kudin Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotun tarayya a Legas kudancin Najeriya ta yi watsi da wata ƙara da aka shigar gabanta na neman cire rubutun ajami a kuɗin ƙasar.

    Barista Malcolm Omirhobo ne ya shigar, inda yake kalubalantar Babban Bankin Najeriya CBN kan kotu ta umarce shi domin cire rubutun ajami na haruffan larabci daga takardar kuɗin ƙasar.

    Kotun ta yi watsi da karar a ranar Talata inda mai shari’a Yellim Bogoro ya nuna cewa wanda ya shigar da karar ya gaza bayar da hujjoji da za su nuna cewa Babban Bankin Najeriya ya Sanya rubutun ajami da wata mummunar manufa.

    Kafin zartar da hukuncin, kotun ta ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yanci inda ya jaddada da cewa babu fifita wani addini ko kabila.

    Tun a 2020 aka fara shari’ar, wanda sai a yau Talata babbar kotun ta Lagos ta zartar da hukunci.

    Mai shari’a Yellim, wanda ya yi watsi da karar ya kara da cewa kotun ta dogara ne da shari’ar Cif Gani Fawehinmi da Akilu da aka yi a shekara ta (1998), inda kotun ta ce yayin da Cif Omirhobo ke da gurbi don sauraron kararsa amma kuma ya kasa bayar da isasshiyar hujja da za ta nuna cewa tsarin da Babban Bankin Najeriya ya yi don ci gaba da amfani da rubutun Ajami kan takardun kudin Naira da rubutun Larabci, an yi shi ne da muguwar manufa.

    Sauran wadanda suke cikin shari’ar sun hada da kungiyar kare haƙƙin Musulmi karkashin daraktanta Farfesa Ishaq Akintola da kuma Umar Kalgo, wani fitaccen lauya mazaunin jihar Kebbi.

    Babban Daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi , Farfesa Ishaq Akintola, bayan yanke hukuncin ya ce wannan nasara ce mai cike da albishir ga Musulmi da masoya Musulunci a fadin kasar.

    A martanin da ya mayar kan hukuncin, Mista Omirhobo ya ce ya nemi a ba shi kwafin hukuncin kuma zai yi nazari don daukar mataki na gaba.

    Da yawa dai ba su fahimci cewa kafin zuwan turawan mulkin mallaka galibin ana amfani ne da haruffan larabci domin rubuta harsunan Afirka da ake kira "Ajami."

  5. Falasdinawa kusan 50 sun mutu a sabbin hare-haren Isra'ila

    Harin ya shafi wata mota a Mawasi

    Asalin hoton, EPA

    Rahotanni daga Gaza na cewa an kashe tare da raunata Falasdinawa da dama a wasu sabbin hare hare ta sama da rahotanni suka ce Isra'ila ta kai.

    Ma'aikatar Lafiyar Hamas a Gaza ta ce fiye da 50 aka kashe, sannan wasu fiye da 20 sun jikkata bayan da wani harin makami mai linzami ya fada kan wata mota a yankin Mawasi.

    Hari na biyun da aka kai kuma an rawaito cewa ya fada kan wani wajen cin abinci a wata makaranta da ke sansanin Nuseirat.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana kai farmaki ne kan mayaƙan Hamas kuma tana duba rahoton farar hular da lamarin ya shafa.

  6. Kotu ta hana Emefiele zuwa ƙasashen ƙetare neman magani

    Emefiele

    Wata babbar kotu a Abuja ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeria na zuwa neman maganin rashin lafiyar da ba a bayyana ba a ƙasashen waje

    Emefiele, wanda kotu ta bayar da belinsa kan zargin almundahana, an kuma tuhume shi da laifuka da suka hada da buga sabbin kuɗi da fitar da biliyoyin naira ba tare da amincewar shugaban ƙasa ba.

    A makon da ya gabata ne, Emefiele ya nemi kotu ta ba shi fasfo dinsa domin tafiya Birtaniya neman magani, lauan EFCC da ya shigar da ƙara ya ƙalubalanci buƙatar inda ya ce barin tsohon gwamnan Babban Bankin barin Najeriya hatsari ne.

    EFCC ta shigar da sabbin tuhume-tuhume kan Emefiele, tana zarginsa da cin mutuncin ofishinsa da rashawa a lokacin da yana gwamnan Babban Bankin.

  7. Gwamnan Kano ya amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu

    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar da za ta samar da masarautu uku masu daraja ta biyu.

    Gwamnan ya amince da dokar ne bayan amincewar majalisar dokokin jihar ta Kano a ranar Talata.

    Sabuwar dokar ta masarautar Kano da ta ƙunshi sarki mai daraja ta ɗaya guda ɗaya da masu daraja ta biyu guda uku.

    Wannan na zuwa bayan hukuncin wata babbar kotun jihar da ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da dokar masarautun Kano ta 2020 ta kafa da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.

    Yanzu dai abin jira a gani shi ne - waɗanda gwamnatin ta Kano za ta naɗa sarakuna masu daraja ta biyu.

  8. Ƴansandan Najeriya sun kama wani babban ɗan Kirifto

    Shugaban ƴansandan Najeriya

    Asalin hoton, @PoliceNG

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan wani babban ɗankasuwar Kirifto da aka fi sani da sunan Blord da ta kama.

    Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Blord ne kan zargin damfara ta hanyar amfani da kirifto.

    A sanarwar, rundunar ta ce tana bincike bayan koke da ƙorafi da ta samu game da kamfanoni da suka hada da na gidaje da ake fakewa da kirifto da ke da alaƙa da wanda take zargi Blord.

    "Lifukan sun haɗa da zargin damfara da sunan kirifto, da damfara a intanet da laifukan damfara na kwamfuta da tallafi ga ta'addanci," a cewar sanarwar.

  9. Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab sama da 50

    Sojojin Somaliya da mayakan sa-kai, da dakarun hadin gwiwa na ƙasashen duniya, sun gudanar da wani samame a tsakiyar yankin Galgudud, wanda ya yi sanadin mutuwar mayakan al-Shabab aƙalla 50 kamar yadda gidan Talabijin mallakin gwamnatin kasar ta ruwaito.

    Gidan talabijin ya nuna hotuna a shafukan sada zumunta na X da Facebook, wadanda ke nuna hasarar rayukan da aka samu a harin da aka kai a yankin Dhabaqle, da ke tsakanin garuruwan Masagaway da Osweyne.

    Daga cikin waɗanda aka kashe har da manyan kwamandojin ƙungiyar al-Shabab, a cewar rahoton.

    Rundunar Sojin ƙasar ta kuma wallafa wani faifan bidiyo a kan shafin X da ke nuna harin da aka kai kan mayakan al-Shabab.

    A martanin da ta mayar, al-Shabab ta yi iƙirarin cewa ta kashe sojoji 27 tare da raunata wasu 38 a fafatawar da sojoji a Galgudud.

    Harin da sojojin ke ci gaba da kai wa 'yan ƙungiyar Al-Shabab da ke rike da wasu muhimman yankuna na yankin Galgudud da suka hada da garuruwa irin su el Buur da Galhareri da Gal'ad da kuma kauyuka daban-daban na yankin.

  10. Wa'adin da aka bai wa mazajen Ukraine na shiga aikin soja na gab da cika

    Sojojin Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    An samu dogayen layuka a wuraren da ake daukar aikin Soja a Ukraine a yayin da ranar da aka ware don ɗaukar bayanan maza masu shekarun 18 zuwa 60 ke gab da cika.

    Wakilin BBC ya ce wani mutum ya shaida musu cewa yana ganin abu ne mai kyau ya bayar da gudunmuwarsa da kuma amfani da makamai na miliyoyin fama-famai.

    Wani kuma daga cikin mutanen ya ce yana cikin damuwa saboda idan aka ba shi aiki zai tafi ya bar dansa wanda ke da nakasa.

    Duk wanda bai je ya bayar da bayanansa ba za a ci tarar sa ko kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

    Ma'aikatar harkokin tsaron Ukraine ta ce kawo yanzu maza fiye da miliyan hudu ne sun suka bayar da bayanansu.

    Ukraine na fuskantar ƙarancin dakaru yayin da Rasha ke cigaba da lugudan wuta. Ƙasar na kokarin ƙara yawan sojojinta domin cike gurbin waɗanda suka rasu ko kuma suka nakasa sakamakon yaƙin.

  11. Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya yi wa 'yan NYSC kyautar N100,000 kowannensu

    @jidesanwoolu

    Asalin hoton, @jidesanwoolu

    Bayanan hoto, Gwamna Sanwo-Olu kenan a kan mambari lokacin da yake halartar bikin yaye masu yi wa ƙasa hidima a Legas

    Gwamnan jihar Legas babban birnin kasuwancin Najeriya ya yi wa matasa masu yi wa ƙasa hidima na NYSC kyautar naira 100,000 kowannensu da ke cikin rukuni na Stream I ajin Batch B.

    Da yake jawabi sanye da kakin hidimar ƙasa yayin bikin sallamar matasan a sansanin horarwa da ke yankin lyana Ipaja, Sanwo Olu ya kuma yi alƙawarin ɗaukar mutum 100 daga cikinsu aiki a jihar.

    "Saboda yadda kuka jajirce, kowannenku zai koma gida da N100,000," in ji shi. "Za a tura muku kuɗin a asusunku mako mai zuwa."

    Kazalika, gwamnan ya yi alƙawarin ware naira biliyan biyar wajen gina sabon sansanin horar da matasan NYSC.

    Mutum 4,254 hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta tura jihar Legas domin gudanar da aikin a wannan karon, wanda ake gudanarwa duk shekara bayan mutum ya kammala digiri ko babbar difiloma na farko matuƙar bai wuce shekara 30 ba.

  12. 'Yan bindiga sun yi iƙirarin ƙwace iko da wani kauye a Burkina Faso

    Wasu da ake zargin 'yanbindiga ne sun ƙwace iko da garin Bomborokuy da ke lardin Kossi a yammacin Burkina Faso, kamar yadda jaridar Burkina Info ta ruwaito.

    A cikin wani bidiyo da jaridar ta wallafa a shafinta na X, an ga wasu mutum biyar sanye da kakin soja suna harba bindigogi suna magana da yaren yankin.

    "Ƙungiyar 'yanbindiga da ke dauke da makamai sun ayyana karɓe iko da Bomborokuy tare da ƙalubalantar shugaban mulkin soja Ibrahim Traore da ya kwato garin," a cewar rahoton.

    Shafin Wamaps ya ruwaito cewa an kashe aƙalla fararen hula 20 a yankin ranar 12 ga watan Yuli tare da yin kaca-kaca da wata tasha ta tsaro da wasu dakarun sa-kai na gwamnati mai suna VDP ke kula da ita.

    An kashe wani jami'in VDP ɗaya sannan aka jikkata wasu huɗu, a cewar shafin.

  13. Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 40 a Afghanistan

    Ambaliyar ruwa

    Asalin hoton, EPA

    Jami'ai a gabashin Afghanistan sun ce aƙalla mutum 40 sun rasa rayukansu sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi da ya haddasa ambaliyar.

    Akwai wasu kusan 350 kuma da suka samu rauni.

    Mamakon ruwan sama gami da tsawar da aka yi a lardin Nangahar ranar Litnin da tsakar dare ya lalata gidaje 400, a cewar jami'in hukumar agajin gaggawa na yankin.

  14. An harbe mutum ɗaya cikin masu zanga-zanga a Kenya

    Kenya

    Asalin hoton, Reuters

    An kashe mutum ɗaya a Kenya yayin zanga-zangar da ta sake ɓarkewa a Nairobi babban birnin ƙasar domin nuna ƙyamar tsare-tsaren gwamnati.

    Wakiliyar BBC da take wurin, Mercy Juma, ta ce 'yansanda ne suka harbi mutumin a Kitengela da ke kudancin birnin daidai lokacin da aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.

    Ana cigaba da zaman fargaba a Kitengela da kuma wasu sassan ƙasar, inda aka samu rahotonnin arangama da jami'an tsaro.

    Shaidu sun ce an yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa mutanen, abin da ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama a wasu yankunan.

    Masu zanga-zangar sun toshe wani titi mai muhimmanci da ya haɗa ƙasar da maƙwabciyarta Tanzania.

  15. Labarai da dumi-dumi, Majalisar Kano ta amince da ƙirƙirar ƙananan masarautu uku

    Majalisar Dokokin Kano

    Asalin hoton, Kano State Assembly

    Majalisar Dokokin Kano ta amince da dokar kafa masarautu uku masu daraja ta biyu.

    A yayin zamanta na yau Talata ne majalisar ta yi wa dokar karatu na biyu da na uku.

    Sabuwar dokar ta tanadi Gaya, da Ƙaraye, da Rano a matsayin ƙananan masarautu kuma dukansu za su kasance ne a ƙarƙashin Masarautar Kano mai daraja ta ɗaya.

    Masarautar Rano na da ƙananan hukumomi uku na Rano, da Bunkure, da Kibiya. Masautar Ƙaraye na da biyu; su ne Karaye da Rogo, sai kuma Gaya da ke da Gaya, da Ajingi, da Albasu.

    Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu...

  16. Labarai da dumi-dumi, Kocin Ingila Southgate ya ajiye aikinsa

    Gareth Southgate

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila Gareth Southgate ya ajiye aikinsa bayan jagorantar tawagar zuwa wasan ƙarshe na gasar ƙasashen Turai karo biyu a jere.

    Tawagar ta Three Lions ta sha kashi a hannun Sifaniya da ci 2-1 a wasan ƙarshen da suka buga ranar Lahadi, da kuma wanda Italiya ta doke su a bugun finareti shekara uku da suka wuce.

    A ƙarshen shekarar nan ne kwantaragin kocin mai shekara 53 zai ƙare, inda ya ja ragamar ƙasar tasa ta haihuwa wasa 102 cikin shekara takwas.

    "A matsayina na ɗan Ingila mai cike da alfahari, taka wa Ingila leda da kuma jagorantar ta alfarma ce a rayuwata," in ji Southgate.

    "Hakan ya fi komai a rayuwata, kuma na yi duk mai yiwuwa.

    "Amma lokacin sauyi da kuma buɗe wani sabon babi ya yi."

  17. Yau Najeriya ke kammala kwashe alhazanta daga Saudiyya

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, Nahcon

    Hukumar Alhazan Najeriya ta ce za ta kammala kwashe mahajjatanta da suka je aikin Hajji na bana a yau Talata daga Saudiyya.

    "Jimillar mahajjatan jihar Kwara 312 ne za su isa birnin Ilorin a jirgin kamfanin Air Peace," in ji hukumar Nahcon cikin wata sanarwa a yau Talata.

    Jirgin nasu zai zama jigila ta 119 kuma ta ƙarshe da suka yi aikin mayar da 'yan Najeriya gida bayan kammala aikin Hajjin na bana.

    Nahcon ta ce za ta kammala aikin ne kwana uku kafin cikar wa'adin da ta tsara yin hakan.

    Jimillar mutum 47,171 hukumar ta kai Saudiyya cikin kwana 27, sannan ta dawo da alhazai 50,091 cikin kwana 25.

    Alhazan Najeriya da dama sun yi ƙorafi game da abincin da aka dinga ba su yayin zamansu a Saudiyyar.

  18. Najeriya ta kwashe 'yan ƙasarta 190 da suka maƙale a Daular Larabawa

    'Yan Najeriya

    Asalin hoton, Nema

    Bayanan hoto, A ƙarshen watan Yuni ma Najeriya ta ɗebo 'yan ƙasar 164 da suka maƙale a Libya

    Gwamnatin Najeriya ta kwaso 'yan ƙasarta 190 daga Haɗaɗɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da ƙasashen ke shirin gyara alaƙar difilomasiyya tsakaninsu.

    A cewar shugaban hukumar ba da agaji ta Nema reshen yankin arewa ta tsakiya cikin wata sanarwa, Bashir Garga, matafiyan sun isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 5:57 na yau Talata.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana cikakken dalilin da ya sa aka kwaso su ba, amma akan yi hakan ne akasari idan 'yan ƙasa suka samu matsalar da ta sa ba za su iya cigaba da zama a ƙasar da suke ba.

    "Hukumomin da ke da alhakin abin sun tantance mutanen kuma aka faɗakar da su game da muhimmancin ɗa'a bayan dawowarsu Najeriya," in ji sanarwar.

    Komawar tasu na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya da sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar cewa ita da UAE sun cimma yarjejeniyar da za ta kai ga ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya bizar shiga Dubai - babban birnin UAE - bayan sama da shekara ɗaya da hana su.

    A shekarar da ta gabata, Najeriya ta kwashe jimillar 'yan ƙasarta 542 daga ƙasar da ke yankin Larabawa na Gabas ta Tsakiya, a cewar rahoton jaridar Punch.

  19. Tinubu zai sake ganawa da 'yanƙwadago kan ƙarin albashi ranar Alhamis

    Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Ranar Alhamis da ta gabata Tinubu ya fara ganawa da 'yan ƙwadagon a fadar shugaban ƙasa

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai sake ganawa da wakilan haɗaɗɗun ƙungiyoyin ƙwadago da na 'yankasuwar ƙasar ranar Alhamis domin cigaba da tattaunawa kan mafi ƙanƙantar albashi.

    Ministan Yaɗa Labarai idris Mohammed ya faɗa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa jiya Litinin cewa shugaban zai ɗora ne kan tattaunawar da suka fara a makon da ya gabata, inda suka kasa cimma wata matsaya.

    Yayin da gwamnatin ta tsaya a kan tayin da ta yi na N62,000, 'yan ƙwadagon ma sun kafe kan N250,000 a matsayin sabon mafi ƙanƙantar albashin, wanda doka ta ce a dinga duba shi duk shekara huɗu.

    Ganawar tasu na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙananan hukumomi ke neman ɓullo da sabon tsarin ba su kasonsu na ƙananan hukumomi 774 a faɗin ƙasar bayan hukuncin kotun ƙoli da ya tabbatar da 'yancin kashe kuɗinsu da kansu - ba tare da sa-hannun gwamnoni ba.

  20. Zaɓen Rwanda: Kagame ya lashe kashi 99 na ƙuri'un da aka ƙirga zuwa yanzu

    Paul Kagame

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Rwanda Paul Kagame ya cinye kashi 99 cikin 100 na ƙuri'un da aka ƙirga zuwa yanzu bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a jiya Litinin, kamar yadda hukumar zaɓe ta National Electoral Commission (NEC) ta sanar a jiya.

    'Yantakarar adawa Frank Habineza na jam'iyyar Democratic Green Party ya samu 0.5, sai kuma ɗantakara mai zaman kansa Philippe Mpayimana da ya samu kashi 0.3.

    Shugabar Nec Oda Gasinzigwa ta faɗa cikin wata sanarwa a gidan talabijin ɗin ƙasar cewa fitowar masu kaɗa ƙuri'a ta kai kashi 98 cikin 100 na mutum miliyan tara da suka yi rajista.

    An ƙirga sama da ƙuri'u miliyan bakwai zuwa cikin daren da ya gabata.

    Kagame ya ci zaɓen 2017 da irin wannan tazara, inda yake neman wa'adin mulki na huɗu.