Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 03/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. Jirage marasa matuƙa sun kai hare-hare a Ukraine

    Mahukunta a birnin Kyiv na Ukraine sun ce sun fuskanci hare-hare a cikin dare daga jirage marasa matuƙa na Rasha.

    Shugaban sojin a Kyiv, Serhiy Popko, ya ce an riƙa jiyo rugugi a sararin samaniya har na tsawo sa'o'i biyar.

    Akwai tarkacen da suka faɗa a yankunan birni, sai dai babu wanda ya jikkata.

    A birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashi kuma, makami mai linzamin na Rasha ya faɗa kan ganin rukunni gidaje, inda mutum 10 suka jikkata.

    Sai dai masu aikin ceto sun ce yana iya kasance akwai mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan gini.

  2. Inter Miami ta lashe MLS Shield na Amurka

    Ƙungiyar Inter Miami na Amurka ta samu nasarar lashe kofin MLS Supporter Shied karon farko bayan ta doke ƙungiyar Columbus Crew da ci uku da biyu.

    Fitaccen ɗan wasan Argentina, Lionel Messi ne ya zura ƙwallo biyu a wasan, sannan tsohon Luis Suarez ya zura ƙwallo na uku.

    Shi dai wannan kofi na Shiled ana ba ƙungiyar da ta fi taka rawar gani a kakar ƙwallon ƙafar ƙasar ne, wanda ƙungiyar ta samu a sanadiyar nasarar da ta samu wasanta na jiya.

    Wannan kofin shi ne kofi na 46 da Messi ya lashe, inda ya kafa tarihin zama ɗan ƙwallon da ya fi lashe kofuna a duniya.

    "Mun samu nasarar wannan, sai kuma tunanin me za mu yi a gaba," in ji Messi.

    Inter Miami na buƙatar ƙarin maki biyu a sauran wasanni guda biyu da za ta fafata a gasar domin kafa sabon tarihin maki mafi yawa a gasar MLS, wanda ƙungiyar New England Revolution ta kafa da maki 73 a shekarar 2021.

  3. Atiku ya buƙaci a mayar da mulkin Najeriya na karɓa-karɓa

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira da a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul domin mayar da mulkin ƙasar na karɓa-karɓa a tsakanin yankunan ƙasar guda shida.

    Atiku, wanda shi ne ɗantakarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi bara ya kuma yi kira da a mayar da shugabancin ƙasar ya zama zango ɗaya na shekara shida maimakon zango biyu na shekara huɗu-huɗu.

    Atiku ya aike da buƙatar hakan ne ga kwamitin gyara kundin tsarin mulkin ƙasar na Majalisar Dattawa, wanda ya fara zama domin yi wa kundin na 1999 garambawul ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Barau I. Jibrin, kamar yadda muka kalato daga jaridar Daily Trust.

    Haka kuma ya buƙaci a yi gyara a ɓangaren mafi ƙarancin matakin karatun masu neman shugabanci, da sauransu.

  4. Gwamnatin Najeriya ta buƙaci ƴan ƙasar da ke Lebanon su fice daga ƙasar

    Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM) ta shawarci ƴan ƙasar mazauna Lebanon su duba yiyuwar ficewa daga ƙasar, kasancewar har yanzu jiragen fasinja na jigala a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya fitar ya ce NIDCOM ta ce ta bayar da shawarar ne sakamakon damauwar da take da shi kan hare-haren da gwamnatin Isra'ila ke kai wa Hezbollah da wasu yankunan Lebanon

    Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta samu labarin yadda kawo yanzu wasu ƴan ƙasar da ke zaune a kudancin ƙasar, sun fice daga yankin, amma duk da haka hukumar ta shawarce su su ci gaba da kasancewa a wurare masu tsaro.

    Haka kuma hukumar ta NIDCOM ta shawarci ƴan ƙasar Mazauna Lebanon da su riƙa tuntuɓar ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar, kan duk wani abu da ya shafi tsaron lafiyarsu.

  5. Hezbollah ta jefa rokoki sama da 240 a arewacin Isra'ila

    Sama da rokoki 240 ne aka harba arewacin Isra'ila daga kudancin Lebanon a ranar Laraba, kamar yadda Rundunar Tsaron Isra'ila ta IDF.

    An wayi gari a safiyar Alhamis ana ci gaba da jin ƙarar jiniya a yankunan arewacin Isra'ila, kamar yadda IDF ta bayyana a Telegram.

    An jiyo ƙararrakin jiniya a yankunan Galilee Panhandle, kusa da iyakar Lebanon.

    Wannan dai na zuwa ƴan kwanaki bayan da dakarun Isra'ila suka ce sun shiga wani yankin Lebanon ta ƙasa domin fatattakar ƴan ƙungiyar Hezbollah.

    Ko a ranar Laraba sai da ƙungiyar Hezbollah ta sanar da kashe sojojin Isra'ila a fafatawar da suka yi a jiyan, inda ita kuma rundunar IDF ta Isra'ila ta ce sojoji takwas ƙungiyar ta kashe mata.

  6. Amurka ba za ta goyi bayan Isra'ila ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba - Biden

    Shugaba Biden ya ce Amurka ba za ta goyi-bayan Isra'ila ta kai hari a cibiyoyin nukiliyar Iran ba, da sunan martani kan hare-haren makamai masu linzami da Tehran ta ƙaddamar kwanaki biyu da suka gabata.

    A lokacin wani tsokaci da shugabannin manyan ƙasashen duniya na G7, Mista Biden ya buƙaci Isra'ila ta yi aiki da hankalinta.

    Shugaban na Amurka na waɗannan kalamai ne bayan jakadan Isra'ila a MDD ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta mayar da zazzafar martanin da Tehran ba ta taba tsammani ba.

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, shi ma ya aike da sakon gargaɗin cewa muddin Isra'ila ta tanka, to za ta sha mamakinsu.

    Shugaba Masoud ya kuma shaida cewa tsaron yankin gabas ta tsakiya, tsaron Musulmai ne baki ɗaya, don haka ba za su raga ba, dominsu ba sa takalar yaƙi ko zubar da jini.

  7. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum shida a Beirut

    Wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gini da ke tsakiyar Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon ya kashe aƙalla mutum shida tare da jikkata wasu shida, kamar yadda jami'a Lebanon suka bayyana.

    Ta jefa bam ɗin ne a wani bene da ke Bachoura, kusa da majalisar dokokin Lebanon, wanda shi ne hari na farko da Isra'ila ta kai a babban birnin ƙasar.

    Haka kuma sun kai hari a Dahieh, wanda shi ne yankin da Hezbollah ta fi ƙarfi.

  8. Assalamu Alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan BBC Hausa, inda muke kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kuma kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.