Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina sojojin Lebanon suke bayan kutsen Isra'ila?
- Marubuci, Carine Torbey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC
- Aiko rahoto daga, Beirut
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da Hezbollah, matsala ce a kan abubuwa guda biyu da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa na kusan shekara 40.
Isra'ila ta ce ba za ta gaji ba sai ta ga bayan barazanar da Hezbollah ta Lebanon, ita kuma Hezbollah tana ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan Isra'ila.
Kimanin wata 11 da suka gabata, yaƙin a tsakanin ɓangarorin guda biyu na ta ƙara ta'azzara.
Yanzu da Isra'ila ta ƙaddamar da kutsawa cikin Lebanon ta ƙasa a karon farko tun bayan shekarar 2006, mutane da dama tambaya suke yi wai ina sojojin ƙasan Lebanon suke ne, kuma me suke yi domin hana yiwuwar hakan, musamman ganin irin tasirin da hakan zai yi a yankin baki ɗaya.
Shin sojojin Lebanon ko na Hezbollah suna kare ƙasar?
A zahiri dai sojojin ƙasa na Lebanon ba a ganin su a yaƙin na Isra'ila da Hezbollah - ƙungiyar da Amurka da Burtaniya da wasu ƙasashen suka ayyana a matsayin ta ƴanta'adda.
A ƙa'ida, aikin sojin ƙasa na ƙasar ne ke yaƙi da maƙiyan ƙasar, kuma a yanzu Isra'ila makiyar Lebanon ce.
Amma sojojin na Lebanon ba su da isassun kayan aiki da makaman da za su iya wannan fafatawar.
Rundunar sojin Isra'ila na da ƙarfi matuƙa, sannan ana tunanin babu ƙasar da ke samun tallafi daga ƙasashen yamma kamar ita - tallafin kuɗi da manyan makamai na zamani.
Bayan haka, akwai wani zargin da aka daɗe ana yaɗawa, wadda tsofaffin jami'an gwamnati da dama suka yi amanna da ita cewa Amurka ta daɗe tana hana gwamnatocin ƙasar sayen manyan makamai da zai iya zama barazana ga Isra'ila.
Matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki - wanda harin kamfanin takin zamanin Beirut da aka yi a 2020 ya ta'azzara - ya ƙara jawo wa sojin na Lebanon tsaiko.
Rashin kuɗi yana cikas ga ayyukan jami'an sojin, wanda yana cikin abubuwan da ake buƙata a duk wani aikin soji, kamar man fetur.
Tallafin Amurka ga sojojin Lebanon
Domin ƙara hana sojojin na Lebanon rawar gaban hantsinsu, Amurka, wadda Hezbollah ke gani a matsayin babbar maƙiyarta, ita ce kan gaba wajen tallafa wa sojojin Lebanon. A wasu ƴan lokuta ma Amurkar ce ke taimakawa wajen biyan albashin sojojin na Lebanon.
Sai dai sun fi bayar da tallafin motoci da kayan kariya da wasu makamai waɗanda ba su kai girman irin waɗanda take ba Isra'ila ba.
Sai dai wasu na ganin rashin kataɓus ɗin sojojin Lebanon a kan Isra'ila ba a kan ƙasar kaɗai ya tsaya ba.
"Ba rundunar sojin Lebanon ba, babu wata rundunar sojin ƙasashen Larabawa da za ta iya fuskantar rundunar sojin Isra'ila," in ji Janar Mounir Shehade, tsohon kodinetan gwamnatin Lebanon a dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a Lebanon wato Unifil.
"Idan za ka gwabza da Isra'ila, sai dai ka yi amfani da fasahar yaƙin sari ka noƙe kamar yadda ake yi a Gaza."
Khalil El Helou, wani tsohon janar ne a rundunar sojin Lebanon, ya ce, "aikin sojojin Lebanon shi ne samar da daidaito da kwanciyar hankali a cikin ƙasar. Yadda yaƙin ya tursasa magoya bayan Hezbollah kusan rabin miliyan zuwa yankunan da ba sa ƙaunar Hezbollah ya haifar da zaune-tsaye wanda zai iya jawo rikici har ma ya iya kai ga yaƙin basasa a ƙasar," in ji shi.
Bayan kashe jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah da Isra'ila ta yi, an tura sojojin Lebanon zuwa yankunan da ake tunanin za a samun rikicin tsakanin ɓangarorin a ƙasar.
Ta kuma fitar da sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata, inda take kira ga "ƴan ƙasar su tabbatar da haɗin kan ƙasa."
Shin sojojin Lebanon suna yaƙi da Isra'ila?
Don haka, shin sojojin suna da hannu a wannan yaƙin? a zahiri dai amsar ita ce a'a.
Amma dai akwai sojojin a kudancin ƙasar. Rundunar sojin a kwanakin baya ta sanar da cewa an kashe wani sojan Lebanon guda ɗaya a wani harin jirgi mara matuƙi da Isra'ila ta kai.
Haka kuma idan a gaba aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, dole za a kai sojojin ƙasar da dama zuwa yankin na kudu, kamar yadda firaministan ƙasar da yake yawan ambatawa a ƴan kwanakin nan.
Amma dai wannan lamarin zai zo da wasu ƙalubale. Ana buƙatar ƙarin sojoji da kuɗaɗe.