'Tattaunar Trump da Putin ba tare da Ukraine ba, ba za ta yi tasiri ba'

Asalin hoton, Getty Images
Babbar jami'ar harkokin ƙetare a ƙungiyar Tarayyar Turai, Kaja Kallas, ta ce duk wata yarjejeniyar zaman lafiya kan Ukraine da za a kulla, matuƙar ba a sa ƙasar a ciki ba, to ba za ta yi tasiri ba.
A lokacin da take tattaunawa da BBC, Ms Kallas ta sake jadadda kiranta na a sa shugaban Ukraine a tattaunawar ranar Juma'a da za a yi tsakanin shugaba Trump da Putin a Alaska.
Ta yi gargaɗin cewa ba ɓoyayya abu ne burin Mista Putin na haifar da rabuwar kawuna da babakere a tattaunawarsa da Trump.
Mista Trump dai na ganin shawararsa ita ce mafita a wannan yaƙi


