Rufewa
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/08/2025
Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Federal Polytechnic Bauchi
Mahukuntan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin tarayya da ke jihar Bauchi sun rufe makarantar bayan wata zanga-zanga da ɗaliban makarantar suka gudanar a yau Talata.
Hukumar makarantar ta ce wasu ɓata-gari sun shiga cikin ɗaliban da ke zanga-zangar tare amfani da damar wajen neman tayar da zaune tsaye, kuma saboda hakan ne ta rufe makarantar nan take.
Kungiyar ɗaliban makarantar ta ce sun yi zanga-zangar ne game da yadda ake shiga makarantar tare da sace musu kayayyakinsu, tare da raunata wasunsu.
A daren ranar Litinin ne wasu da ake zargi ɓarayi ne suka kutsa cikin makatarantar tare da yi wa ɗaliban fashi da makami, har ta kai ga an raunata biyu daga cikinsu.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump zai gana da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai ranar Laraba.
Ganawar za ta zo kwana biyu kafin shugaban na Amurka ya gana da Shugaban Rasha, Vladmir Putin a Alaska.
Ofishin harkokin ƙetare na Amurka ya ce za a yi ganawar ne ta yanar gizo, kuma ofishin shugaban na Ukraine ya tabbatar da ganawar.

Asalin hoton, Nigerian Correctionals Service
Ɗaurarru 16 sun gudu daga gidan yarin Keffi da ke jihar Nasarawa.
Wata sanarwa da Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta fitar ta ce lamarin ya faru da safiyar Talata, kamar yadda mai magana da yawun hukumar ya bayyana.
Sanarwar ta ce wasu daga cikin ɗaurarrun da ke gidan sun ci ƙarfin maʼaikatan da ke tsaron shi, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa nan take.
Hukumar ta kuma ce jamiʼanta biyar da ke sun samu raunuka yayin lamarin, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali kuma suna samun kulawa a wani asibitin gwamnati.
Sai dai sanarwar ta ce an yi nasarar kama mutum bakwai daga cikin ɗaurarrun da suka gudu, kuma babban kwanturolan hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche ya ƙaddamar da bincike kan lamarin.

Asalin hoton, Reuters
Birnin Gaza na fuskantar ƙarin hare-hare ta sama a daidai lokacin da Isra'ila ke yunƙurin ƙwace birnin, kamar yadda hukumar tsaron farin kaya na Hamas ta bayyana.
Shugaban hukumar, Mahmud Bassal ya ce an jefa bama-bamai a garuruwan Zeitoun da Sabra, da ma hare-haren jirage marasa matuƙa a kwana uku da suka gabata.
Ya ce hare-haren sun matuƙar ɗaiɗaita gidajen fararen hula, sannan mazauna garuruwan sun kasa shiga domin ciro gawarwakin ƴan'uwansu da waɗanda suka raunata, amma baraguzai sun danne su.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira ga Isra'ila ta bayar da dama a shiga da magunguna Gaza saboda halin ƴan yankin ke ciki na rashin lafiya kafin ta fara yunƙurin mamaye birnin.

Asalin hoton, Aminu Waziri Tambuwal Media Office
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
Wasu makusantan Sanatan ne suka tabbatar wa BBC sakin nasa, kuma yanzu haka yana gidansa na Abuja.
A ranar Litinin ne hukumar ta tsare shi a Abuja, bayan amsa gayyata kan zarge-zargen fitar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 189.
Kamun da aka yi masa ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ƴan hamayya, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ƴan jama'iyyar haɗaka ta ADC.

Asalin hoton, Peter Obi/X
Ɗan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce kamawa da tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta yi, ya nuna matakan da hukumar ke ɗauka na cin karo da manufar kafa ta.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon gwamnan jihar Anambra, Obi ya ce babban abin da ake buƙata don yaƙar cin hanci da rashawa a Najeriya shi ne gaskiya da riƙon amana daga shugabannin ƙasar.
Peter Obi ya kuma ce yana fatan ganin lokacin da doka za ta yi aiki a kan kowa a Najeriya ba tare da amfani da ita "don muzguna wa ƴan adawa da waɗanda ake yi wa kallon maƙiyan gwamnati mai ci."
A ƙarshe Obi ya ce yana fatan ganin hukumomin yaƙi da cin hanci da sauran laifuka sun yi aiki da sanin ya kamata da kuma doka don kakkabe rashawa daga Najeriya.

Asalin hoton, @officialEFCC
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta musanta zargin zama ƴar amshin shatan jamʼiyyar APC mai mulkin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Talata, shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce zargin da jamʼiyyar adawa ta ADC ta yi cewa EFCC na harin ƴan adawa a ƙasar ba shi da makama kuma abin mamaki ne.
Olukoyede ya ce duk "wani mai bibiyar abubuwan da ke faruwa a Najeriya zai shaida cewa hukumar na gudanar da ayyukanta ba tare da son kai ba''.
''Kazalika iƙirarin ADC cewa ƴan tafiyar haɗaka sun samu sammaci daban-daban daga EFCC ba gaskiya bane'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Hukumar ta kuma nemi ADC da sauran jamʼiyyun siyasa su mayar da hankali kan siyasarsu tare da bai wa hukumar damar yin aikinta.
A ranar Litinin ne jam'iyyar haɗakar da ADC ta zargi EFCC ta far wa ƴan haɗakar da nufin tsoratar da su.
Haka shi ma, Atiku Abubakar - jigo ne a tafiyar ta ADC - ya zargi hukumar da zama karen farautar jam'iyyar APC mai mulki.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Aƙalla mutum 40 aka kashe a wani hari da aka kai wani sansanin ƴangudun hijira da ke yankin Darfur a yammacin ƙasar Sudan, kamar yadda ma'aikatan agaji a ƙasar suka bayyana.
Ƙungiyar agaji ta Abu Shouk ce ta bayyana haka, inda ta zargi dakarun RSF da kai harin a ranar Litinin da ta gabata a sansanin wanda ke ɗauke da mutane da dama.
Rikicin Sudan dai ya jefa ƴan ƙasar da dama cikin mawuyacin hali, lamarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ya yi sanadiyar jefa iyalai da dama cikin matsananciyar yunwa, sannan ta ce ƙasar na tsananin buƙatar agaji.
Wasu kafofin sadarwa a Sudan sun ce sansanin ya faɗa tasku a lokacin da ɓangarorin biyu suke musayar wuta a el-Fasher.
Sai dai ƙungiyoyin agaji sun ce akwai waɗanda aka bi su har inda suke aka harbe su, sannan akwai waɗanda aka kashe a bainar jama'a.

Asalin hoton, Getty Images
Wani binciken da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar ya gano yadda gwamnatin sojin Myanmar ke cigaba da aikata laifuffukan da ta ce take haƙƙin bilʼadama ne.
Daga cikin abubuwan da zargi ƙasar da aikatawa akwai kisan gilla da azabtarwa da kuma cin zarafi ta hanyar lalata.
Rahoton da wani sashe na majalisar mai biciken ƙwaƙwaf kan Myanmar ya fitar, ya dogara kan shaidun da ganau kusan 600 suka bayar.
Tawagar da ta yi binciken ta ce ta kuma yi nasara wajen gano waɗanɗa ke azabtar da mutane a wuraren da ake riƙe da su, kuma ta aika shaidar ta ga wasu kotunan ƙasa da ƙasa.
Wakiliyar BBC ta ce rahoton baya bayan nan ya nuna cewa ayyukan take haƙƙin bilʼadama ba wai kawai suna ci gaba bane, suna ƙara yawaita ne.

Asalin hoton, Rundunar ƴan sandan jihar Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi gargaɗi game da yadda yara ƙanana ke tuƙa babur mai ƙafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu a birnin Kano.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Litinin ta bayyana damuwa kan yadda ƙaruwar yara ƙananan da ke tuƙa babur mai kafa ukun ke jefa rayukan mutanen jihar cikin haɗari.
Sanarwar ta ce a cikin watan Agustan nan kaɗai, an samu manyan haɗurra 16 sanadiyyar tuƙin da yaran suke yi, lamarin da yayi sanadin jikkatar mutane da dama da kuma asarar dukiya mai yawa.
‘Yan sandan sun gargaɗi jama’a da su riƙa bin ƙa’idojin tuƙi tare yin biyayya a duk lokacin da fitilar kan hanya ta nuna a tsaya ko a tafi.
Rundunar ƴan sandan ta kuma ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamawa da hukunta duk wanda aka samu da karya dokokin don tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’umma.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Kula da Kafofin Sadarwa ta Ghana, NCA, ta sanar da rufe gidajen rediyo guda tara a ƙasar, ciki har da wasu fitattun gidajen rediyon da ake tunanin suna da alaƙa da jam'iyyun hamayya, bisa zarginsu da karya dokokin watsa labarai na ƙasar.
A cewar NCA, masu gidajen rediyon sun gaza wajen ɗaukar matakin gyare-gyaren da aka su wa'adin kwana 30 su yi.
Hukumar ta ce gidajen rediyo shida daga cikin taran, "sun ƙi, ko kuma sun yi watsi da wa'adin da aka ba su ta hanyar ƙin ɗaukan matakin da suka dace kan abin da aka buƙata daga gare su."
Sanarwa ta ƙara da cewa gidajen rediyon guda uku, waɗanda mallakar shugaban yankin Ashanti na jam'iyyr New Patriotic Party ne, an rufe su ne bisa karya wasu dokoki, ciki har da yaɗa shirye-shirye daga wuraren da doka ba ta amince ba.
Wannan matakin na zuwa ne bayan sanarwar NCA a watan Yuni cewa ta rufe gidajen rediyo 62 saboda laifuka daban-daban, wanda ya biyo bayan umarnin da ministan sadarwa na ƙasar, Sam George, inda ya umarci hukumar ta ɗauki mataki kan gidajen rediyon da suka karya doka.
A lokacin ne shugaban ƙasar, John Mahama ya shiga tsakani, inda ya buƙaci a ba gidajen rediyon wa'adin kwana 30 domin su gyara abubuwan da ake zarginsu.
Daga cikin abubuwan da ake zarginsu akwai ƙin sabunta lasisi, wuce ƙa'aidar yaɗa labarai da aiki ba tare da cikakken izini ba.

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Ivory Coast sun tuhumi magoya bayan tsohon Shugaban Ƙasa Laurent Gbagbo su 11 da zarigin aikata laifin ta’addanci.
Ana tuhumarsu ne sakamakon wani sabon rikici da ya ɓarke a babban birnin ƙasar, Abidjan, bayan Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar a karo na huɗu.
Masu shigar da ƙara na zargin ƴan jam'iyyar ta PPA ta Mista Gbagbo da ƙona wata motar haya da motar ƴansanda.
Sai dai jam'iyyar PPA ta musanta zargin, kuma ta zargi hukumomi da ƙoƙarin kawar da ƴanadawa gabanin zaɓen na shugaban ƙasa da za a yi a watan Oktoba.
Wani jami'i a yankin kudu maso yammacin Pakistan ya ce ƴanbindiga sun kashe sojojin ƙasar aƙalla guda tara a lardin Balochistan na ƙasar.
Jami'in ya ce gomman ƴanbindigar ne suka kai harin kan jami'an tsaro na ƙasar a daidai lokacin da suke gudanar da aikinsu.
Haka kuma ya ƙara da cewa ƴanbindigar sun kai hari kan sojojin da aka tanada domin kai ɗaukin gaggawa ga jami'an tsaro da suke fuskantar ƙalubale.
Har yanzu dai babu tabbacin wace ƙungiya ce ta kai harin, kuma sojojin ƙasar ba su fitar da sanarwa ba a hukumance a game da harin.
Sai dai tun da farko, sojojin ƙasar sun yi ikirarin kashe kusan ƴanbindiga masu ikirarin jihadi guda 50 a ƴan tsakakanin nan a lardin.

Asalin hoton, AFP
Ƴantawayen M23 na ƙasar Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo, wadda ke samun goyon baya daga Rwanda ta zargi gwamnatin ƙasar da cigaba da yaƙi, wanda ta ce karya alƙawarin tsagaita wuta ne da suka shiga a tsakanin su.
M23 ba ta bayar a hujja ba da ke nuna gwamnatin ta karya alƙawarin, amma ta ce an tura sojoji da makamai manya zuwa kudanci da arewacin Kivu da kuma Bujumbura da ke maƙwabtaka da Burundi daga Kinsasha.
Gwamnatin ƙasar dai ba ce uffan ba kan wannan zargin na M23.
Kakakin rundunar sojin ƙasar, Janar Sylavin Ekenge ya shaida wa BBC cewa, "zai kira" a lokacin da BBC ta tuntuɓe shi.
A makon jiya ne dai gwamnatin ta fara suka tare da zargin ƴantawayen da karya yarjejeniyar ta tsagaita wuta ta hanyar kai wasu hare-hare.

Asalin hoton, Atiku Abubakar
Tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce kamawa da tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi na da alaƙa shigarsa cikin haɗakar jam'iyyun hamayya.
Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da yunƙurin cin zarafi da tsoratarwa da nufin murƙushe jam'iyyun hamayya a ƙasar.
"Abun da muke gani a yanzu shi ne yadda gwamnatin Tinubu ke amfani da yaƙi da cin hanci a matsayin karen farauta domin daƙile jagororin jam'iyyun hamayya tare da jan su zuwa jam'iyya mai mulki."
Ya ce abin da ke faruwa ba ya cikin, "manufarmu a lokacin da muka yi aiki tuƙuru domin assasa hukumar EFCC. Yanzu abubuwa na fitowa fili cewa duk wani ɗansiyasa da ke da alaƙa da jam'iyyun adawa yana fuskantar barazanar zargin cin hanci da rashawa, amma da zarar sun koma jam'iyya mai mulki, sai a 'yafe' musu."
Atiku ya ce duk da cewa yaƙi da cin hanci da rashawa lamari ne da ke buƙatar goyon bayan ƴan Najeriya, ya ce haɗa yaƙin da wata manufa ta daban abu ne da ya cancanci suka daga ƙungiyoyi gwagwarmaya da ma ƙasashen duniya masu ƙawance da Najeriya.
A ƙarshe Atiku ya ce yana ba ƴan Najeriya tabbacin cewa za ba su yi shiru su zura ido suna gani ana ɗaukar matakai da suke barazana ga dimukuraɗiyyar ƙasar ba, wadda ya ce ana yunƙurin mayar da ita siyasar jam'iyya ɗaya.

Asalin hoton, AP
Ana gudanar da taruka a Japan domin juyayin cika shekara 40 da afkuwar hadarin jirgin sama mafi muni da ya faru a duniya.
A lokacin mutum 520 ne suka mutu bayan jirgin na Japan ƙirar Boeing 747 ya yi bindiga 'yan dakikai da tashinsa daga Tokyo a watan Disamban 1985, inda ya fada kan wani tsauni.
'Yan'uwa da iyalan fasinjojin jirgin su rika kai ziyara kan tsaunin domin tunawa da addu'o'i ga wadanda suka rasa, kana daga bisa aka gudanar da taron juyayi da yamma.
Mutane hudu ne kadai suka tsira daga haɗarin.

Asalin hoton, Getty Images
Ambaliya, wadda mamakon ruwan sama ya janyo, ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum takwas, ciki har da ƙananan yara uku a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Haka kuma ambaliyar ta shafi aƙalla gidaje dubu uku, tare da ilata gonaki da dama a jihar, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Tuni dai masu aikin ceto suka bazama domin nemo wasu mutanen da ake tunanin sun ɓace a sanadiyar ambaliyar.
Hukumomi dai a Najeriya sun ayyana ɗaruruwan garuruwa a jihohin ƙaar da suke fuskantar barazanar ambaliya a sanadiyar mamakon ruwan sama da aka yi hasashen za a samu a damunar bana.

Asalin hoton, REUTERS/KCNA
Jami'an leken asiri a Koriya ta Kudu sun ce suna da tabbacin an tura leburori 'yan Koriya ta Arewa sama dubu 50 Rasha inda suke aiki kamar bayi kuma galibinsu a wuraren da ake aikin gini.
A tattaunawarsu da BBC, jami'an sun ce Rasha na sake dogara da leburorin Koriya ta Arewa saboda karancin ma'aikata sakamakon yaƙinta a Ukraine.
Wakiliyar BBC ta zanta da wasu mutane shida da suke ƙasar, inda suka ba da labarin yadda suke aikin sa'o'i 18 a rana kan kuɗi ƙalilan, wasu ma ba a biya.
Sannan sun ce abin da suka samu suna aika wa ne ga gwamnatin ƙasarsu Koriya ta Arewa.
Moscow dama dai ta dogara ne da sojojin Koriya ta Arewa da makamai

Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi dala miliyan 300 domin gudanar da wasu ayyukan da ya ce zai inganta rayuwar ƴangudun hijira a arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito, bankin ya ce a shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ƴangudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.
Bankin ya ce rikice-rikice da suka daɗe suna addabar yankin sun raba sama da mutum miliyan 3.5 da muhallinsu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.
"Daga cikin ɓangarorin da za mu mayar da hankali akwai rage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa."
"Muna matuƙar farin ƙaddamar da wannan aikin domin taimakon Najeriya wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta," in ji Mathew Verghis, daraktan Bankin Duniya a Najeriya.