An samu raguwar kwararar baƙin haure cikin Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Wasu alƙaluma na Amurka sun nuna cewa an samu gagarumar raguwar kwararar bakin haure tsakanin iyakar ƙasar da Mexico mafi girma a tsawon shekara 50.
Alƙaluman da kafar yaɗa labarai ta CBS ta samu, sun nuna cewa tsakanin 2024 zuwa shekarar 2025, jami'an Amurka sun hana baƙin haure sama da 238,000 tsallakawa kan iyakar ƙasar.
Lokacin ya ƙunshi watanni huɗu na mulkin shugaba Joe Biden.
Bayanan sun nuna cewa watanni takwas na farkon mulkin Trump, an samu baƙin haure da suka tsallako ƙasa da 9000 a duk wata.
Fadar White House ta ce alƙaluman sun tabbatar da alƙawarin shugaba Trump na tabbatar da tsaron iyakar Amurka.



