Rufewa
Masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa da ke kawo muku labarai kai-tsaye.
A nan za mu dakata a yau Laraba - Tabawa - ranar samu, da fatan kun ji dadin kasancewa da mu.
Sai kuma gobe Alhamis, idan Allah Ya kai mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/10/2025.
Daga Habiba Adamu da Aisha Babangida
Masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa da ke kawo muku labarai kai-tsaye.
A nan za mu dakata a yau Laraba - Tabawa - ranar samu, da fatan kun ji dadin kasancewa da mu.
Sai kuma gobe Alhamis, idan Allah Ya kai mu.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin babban birnin Nijar, Yamai sun haramta wa kananan 'yan kasuwa masu sayar da kaya a kura ko baro ko tarko a kasuwannin birnin da kewaye.
A takardar da ya sanya wa hannu shugaban da'irar Yamai Kanar Boubacar Soumana Garantche ya umarci irin wadanan kananan 'yan kasuwa da su nisanci kasuwanni, su ci gaba da harakokinsu a cikin unguwanni.
Sanarwar ta yi tanadin hukunci daban-daban ga wadanda suka nuna turjiya ga wannan mataki.

Asalin hoton, DSS
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ta saki wasu mutum bakwai da ta kama wata hudu baya yayin da suka koma ƙasar daga aikin Hajjin da ya gabata, bisa zargin zama 'yan ta'adda.
Hukumar ta kuma bai wa kowannensu sallamar naira miliyan 1.
DSS ta ce ta sake su ne bayan kammala binciken da ta gudanar na watanni a kan zarginsu da zama ƴan ta’adda, kuma ba ta same su da laifi ba.
Mutanen wadanda sun kunshi Hausawa da Fulani sun hada da Al’amin daga jihar Oyo da Abdullahi Baba Komi daga jihar Kwara.
Lauyan mutanen Barista Bashir Sabi’u Ahmad, ya sheda wa BBC cewa ya ji dadi mutuƙa da matakin.
Wata majiya a hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin sababbin sauye-sauye da shugaban hukumar Adeola Oluwatosin Ajayi ya samar, a kokarinsu na sauya tunanin al’umma a kan yanda hukumar ke gudanar da binciken wadanda ake zargi da aikata laifi.

Asalin hoton, Reuters
Habasha ta zargi Eritrea da shirin kai mata hari ta hanyar hada kai da wata kungiyar 'yan hamayya.
A alamun baya-baya nan da ke nuni da yadda kasashen biyu da ke makwabtaka da juna ke ci gaba da rikici kan wanda ke da iko da tekun Bahar Maliya.
Zargin na Habasha na kunshe ne a cikin wata wasika da ministan harkokin wajenta Gediyon Timothe-wos ya aike wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yana mai gargadin cewa hadakar ta kara bayyana a 'yan watannin da suka gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan riko na Faransa Sébastien Lecornu, ya ce Shugaba Emmanuel Macron ka iya zabar sabon firaiministan da zai maye gurbinsa nan da sa'a 48.
Mista Lecorno ya bayyana hakan ne bayan ganawa da 'yan jam'iyyarsu, inda kuma ya amince za a iya jingine batun gudanar zaben wuri a kasar.
Ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya yi da gidan talabijin din Faransa bayan ganawa da Mista Macron.
Lecornu ya kara da cewa shirin Shugaba Macron na sauyin tsarin Fansho mai cike da rudani na daya daga cikin abin da zai janyo tarnaki wajen kafa sabuwar gwamnati.
Wani sabon rahoto da asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar, ya yi gargaɗin cewa adadin yaran da tashin hankalin ƴan daba ya raba da muhallansu a kasar Haiti, ya ruɓanya a shekarar da ta gabata zuwa 680,000.
UNICEF ta ce karuwar yaran da tashin hankalin Haiti ya raba da muhallansu ya munanan.
Rahoton ya yi gargadin tashin hankalin na gab da durkusar da kasar da ke yankin Karebiya.
Rahoton ya kara da cewa sama da yara miliyan 3 ne ke tsananin bukatar taimako domin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar 'yansandan Najeriya ta dakatar da aiwatar da dokar kama wadanda ba su da takardar izinin sanya gilashi mai duhu a motarsu, sakamakon umarnin da wata kotu ta bayar kan a dakatar.
Mai magana da yawun rundunar 'yansandan ta babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ne ta bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da tashar talabijin ta AIT a yau Laraba.
Ta tabbatar da hakan ne bayan da ta ce a hukumance 'yansanda sun samu umarnin kotun na dakatar da aiwatar da dokar.
SP Adeh ta ce zuwa yanzu za su bi umarnin kotun har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci a kan karar.
Da take magana a kan dalilinsu na kamen masu bakin gilashin wadanda ba su da izini ta ce, an dauki matakin ne saboda matsalar tsaro.
Ta ce wasu na sanya bakin gilashin motarsu su rika aikata miyagun laifuka, wanda hakan ke sa da wuya a iya gane wadanda ake zargi da aikata laifi.
Haka kuma ta yi watsi da zargin da ake yi cewa an bullo da matakin ne domin samun kudi inda tace duk kudin da ake biya na izinin sanya gilashin mai duhu yana shiga asusun bai daya ne na gwamnatin tarayyar Najeriya, amma ba wajen 'yansanda ba.

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon rahoto da asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya - UNICEF, ya fitar, ya ce yawan yaran da tashin hankalin 'yan daba ya raba da muhallansu a kasar Haiti, ya rubanya a shekarar da ta gabata zuwa dubu dari 680.
Rahoton ya yi gargadin tashin hankalin na gab da durkusar da kasar da ke yankin Karebiya.
Tashin hankalin ya janyo yaran na gudun hijira akai-akai da iyyaensu.
Wasu kuma an kashe iyayensu abin da ya sa suke ta gararanba.
Rahoton ya kara da cewa sama da yara miliyan uku ne ke tsananin bukatar taimako domin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE
Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta samar da sansanin soji na dindindin a kudancin jihar Kwara.
Majalisar ta buƙaci a samar da sansanin a kusa da dajin Ifelodun wanda ke neamn zama sansanin ƴanbindiga a jihar.
A baya-bayan nan jihar Kwara ta kasance cikin jerin jihohin ƙasar da yanbindiga ke cin karensu babu babbaka.
Matakin na zuwa ne bayan da Sanata Lola Ashiru ya gabatar da kudirin a gaban majalisar.
‘A watan da ya gabata kawai fiye da jami'an tsaron da ke kula da dajin da ƴan bijilan 12 aka kashe a lokacin da ƴanbindiga suka yi musu kwantan ɓauna a garin Oke-Ode''.
“Haka ma an kashe sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma a garuruwan Ogba-Ayo da Babanla, Sagbe da Oro Ago da kuma and Ganmu-Alheri,” kamar yadda sanata Ashiru ya bayyana.

Asalin hoton, Reuters
Wakilan Amurka sun isa Masar domin shiga tattauanwar da ba ta kai tsaye ba tsakanin wakilan Isra'ila da Hamas.
Jakadan Amurka na musamman, Steve Witkoff da mashawarcin shugaban ƙasa, kuma surukin shugaba Trump, Jared Kushner sun isa wurin tattaunawar da nufin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Cikin waɗanda suke halartar zaman har da Firministan Qatar da shugaban hukumar leƙen asirin Masar, domin tabbatar da an cimma matsaya a yarjejeniyar.
Wani babban jami'in ƙungiyar Hamas ya bayyana kyayyawan fata game da tattaunawar domin cimma matsaya.
Can a Gaza mutum biyu kawai aka bayyana cewa sun mutu tun bayan tsakiyar daren jiya, adadi mafi ƙanƙanta cikin watanni.
Majiyoyin lafiya a Sudan sun ce an kashe mutum 20 cikin kwana guda sakamakon hare-hare a kan asibiti ɗaya tilo da ke aiki a birnin El-Fasher da aka yi wa ƙawanya.
Majiyoyi a yankin sun zargi dakarun RSF da ƙaddamar da hare-haren.
Mayaƙan na RSF sun zafafa hare-hare kan El-Fasher - birni ɗaya da ya rage a hannun mayaƙan gwamnati a yammacin yankin Darfur.
Rikicin da ya ɓarke tsakanin bangarorin biyu a Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Asalin hoton, Reuters
Wata ƴar Japan, Susumu Kitagawa da wani haifaffen Burtaniya, Richard Robson da ɗan Amurka da Jordan Omar Yaghi sun samu kyautar Nobel ta Chemistry ta bana.
Masana kimiyyar uku za su raba kyautar ta Nobel kusan dala miliyan 1.2 tukwicin samar da wani abu na musamman da ba kowa ne ya yi ba a fannin Chemistry.
Masanan sun ƙirƙiro wata kimiyya wadda zata taimaka wurin magance wasu manyan matsaloli da ake fuskanta a duniya.
Sabuwar kimiyyar zata killace iskar Carbon dioxide domin magance matsalar sauyin yanayi da rage lalata muhalli da robobi ke yi.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a Bengal ta Yamma da ke Indiya, sun ce dabbobi da dama sun mutu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya haddasa, a dazuka biyu masu tarin dabbobi.
Cikin dabbobin da suka mutu a gandun dajin Gorumara da Jaldapara da ke tsaunin Himalaya sun haɗa da ɓauna da karkanda da damusa.
Yayin da gwamman giwaye suka samu wurin da suka fake.
An yi ƙoƙarin aikin ceton wasu karkanda da giwaye da suka maƙale a wani kogi.
A makon da ya wuce ma aƙalla mutane 36 ne suka mutu, a ambaliyar ruwan da ta afku a jihar.

Asalin hoton, Getty Images
Nazarin da ake yi duk shekara kan noman damuna na 2025, wato (APS) ya nuna cewa an samu ƙaruwar takin zamani maras inganci a kasuwannin Najeriya a damunar bana.
Nazarin ya nuna cewa yawan kuɗaɗen da manoman ƙasar suka kashe wajen samar da abinci a damunar ta bana ya ƙaru da fiye da kashi 36% a wasu wuraren.
Hukumar kula da bincike kan harkokin noma da ayyukan malaman gona ta ƙasar ta NAERLS ce ke gudanar da binciken a ɗaukacin jihohin kasar 36 da kuma birnin Abuja.
Hukumar ta ce ƙananan manoma su suka fi amfani da takin mara inganci na NPK, wanda aka fi samarwa a cikin gida.
Hakan na zuwa ne yayin da manoma ke kokawa kan tsadar taki da maganin kashe ƙwari da sauran muhimman abubuwan da ake buƙata na harkar noma.

Asalin hoton, ORTN
A jamhuriyar Nijar yayin da ya rage ƴan kwanaki a koma karatun shekarar 2025- 2026, gwamnatin ƙasar ta yi wasu gyare-gyare ga tsarin ilimin ƙasar.
Hakan ya sanya ta dakatar da amfani da wasu litattafai 64 da ake aiki da su wajen koyarwa a makarantun ilimin boko na ƙasar.
Wani kwamitin ƙwararru mai mambobi 32 da aka kafa domin tantance ingancin litattafai aƙalla 128 da ake amfani da su a makarantun boko na ƙasar ne ya gabatar da sakamakon aikinsa.
Kwamitin ya ce litattafan 64 basu dace da al'adu da kuma tarbiyyar al'umar ƙasar ba.
Yayin da kwamitin ya amince da a ci gaba da amfani wasu litattafai 13 da suka cika dukkan sharuɗɗan da aka buƙata.
Sai dai litattafai 51 daga cikin 128 na buƙatar gyaran fuska kafin a ci gaba da amfani da su a ƙasar, a cewar kwamitin.
kungiyoyi a ƙasar sun bayar da shawarar horar da malaman makaranta don kyautata harkar karatu da litattafan da aka amince da su.

Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa
Hukumomin lafiya a jihar Kano sun yi ƙarin haske kan dakatar da wasu jami’an da ke kula da harkokin lafiya, a karamar hukumar Kabo bisa zarginsu da yiwa aikin riga-kafin cutar ƙyanda zagon kasa.
Hakan na zuwa ne a yayin da jihar ta bi sahun sauran jihohin Najeriya wajen gudanar da gangamin yi wa jarirai sabbin haihuwa zuwa shekara 15 allurar riga-kafi.
Gangamin na fatan kare su daga cututtuka da dama ciki har da sarƙe haƙora da ƙyanda da kuma cutar mashaƙo.
Dakatarwar ta kuma shafi wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da ake aikin gangamin da su.
Ana zargin ma'aikatan da rashin zuwa aiki.

Asalin hoton, EPA
Falasɗinawa na wallafa hotuna da bidiyon ƴan'uwansu da aka kashe a ƴakin, da na waɗanda suka tsere daga gidajensu da aka lalata suka zama kufai da yadda yaƙin ya lalata rayuwarsu.
Abubuwan da suka mamaye kafafen sada zumunta ke nan daga Falasɗinawa da ke tuna yadda yaƙin Gaza ya shafi rayuwarsu, tun bayan da Hamas ta kai hari Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023.
Lamarin da ya kai yaƙin ke ta ruruwa har ya zuwa yanzu, kuma ya lalata rayuwar al'umomi miliyan biyu da ke Gaza.
"A shekaru biyun nan na yi asara sosai," in ji Emaan al-Wahidi, wadda ke zaman haya a wani gareji, tana fafutukar neman abinci da ruwa mai tsafta a kullum, kuma ta sha sauya matsuguni a dalilin yaƙin.
Ɗanta Jehad, mai shekara 17 na tafiya a kan titin Gaza a bara, lokacin da harin da Isra'ila ta kai ta sama ya same shi.
Ya mutu bayan kwana biyu sakamakon jinin da ya dinga taruwa a cikinsa saboda raunukan da ya samu.
"Na rasa ɗana Jehad," in ji ta. "Na rasa gidana, wanda aka lalata. Mun yi asarar kyakkyawar rayuwar da muke yi gabannin yaƙin.
A duk wata tattaunawar da za ka ji a Gaza, tambayar da kusan kowa ke yi ita ce: "Yaushe za a kawo ƙarshen yaƙin?"

Asalin hoton, Northeast Reporters
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da kyautar gidaje ga ma'aikatan jinya da malaman makaranta 72 a ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar Borno a Najeriya.
Cikin waɗanda suka samu kyautar sun haɗa da wata ma'aikaciyar jinya ƴar ƙabilar igbo da ta kwashe fiye da shekara 24 tana aiki a jihar, Marbel Ijeoma Duaka.
Haka kuma gwamnan ya ɗauki ɗanta, Anthony aiki a jami'ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri.
Gwamnan ya miƙa gidan da kayan da ke cikinsa ga ma'aikaciyar, wadda ƴar asalin jihar Anambra ce, a ranar Talata.
Inda ya ƙara da cewa bata taɓa barin garin na Mafa ko da a lokacin da ake fuskantar hare-haren Boko Haram. Inda ya nemi ta ci-gaba da zama a jihar ko da bayan ta yi ritaya.
Nas ɗin ta miƙa godiyarta ga gwamnan kan abubuwan alherin da ya yi mata da kuma ɗanta.

An tsananta bincike a kan kasuwar sayar da magungunan tari na ƙasar Indiya, bayan mutuwar yara da dama.
A farkon watan Satumbar data wuce, an samu mace-macen yara da ba a san musabbabinsa ba, a wani ƙaramin ƙauye da ke Madhya Pradesh, lamarin da ya tayar da hankalin ma'aikatan lafiya.
Yara 11 ne suka mutu, waɗanda shekarunsu suka kama daga ɗaya zuwa shida a cikin ƴan kwanaki, bayan sun sha wani maganin tari.
Jami'ai sun yi ta bincike kan ruwan sha har su sauro, kafin daga baya gaskiya ta bayyana cewa sun samu matsalar ƙoda ne.
Makonni biyu bayan nan ne wani ɗakin bincike da ke birnin da ke kudancin Chennai, ya tabbatar babban abun tashin hankalin.
Ruwan maganin tarin na ƙunshe da fiye da kashi 48 cikin ɗari na diethylene glycol, wani sinadari mai guba da ake amfani da shi a masana'antu da bai kamata a same shi a cikin magani ba.
An sha samun matsalar ƙoda bayan mutane sun sha giya mai ɗauke da shi.
Matsalar ba ta tsaya a Madhya Pradesh ba, har makwabciyar jihar ta Rajasthan, inda can kuma yara biyu suka mutu, bayan shan wani maganin tarin da aka haɗa na gida.
Lamarin da ya fusata al'umma kuma ya kai ga gwamnati ta fara bincike.
A shekarun da suka wuce magungunan tarin da aka sarrafa a Indiya masu ɗauke da diethylene glycol sun kashe yara masu yawa.
A 2023, irin waɗannan magunguna sun kashe yara 70 a ƙasar Gambia da kuma wasu 18 a Uzbekistan.

Asalin hoton, Others
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ɗora alhakin naɗa mutane masu takardun bogi a muƙamai.
Atiku wanda ya tsaya wa jam'iyyar adawa ta PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya bayyana hakan ne a shafinsa na X.
Ya yi kira da cewa "a yi cikakken bincike mai zaman kansa na gaskiya wanda ya ƙunshi komai kan takardun karatun duka mambobin majalisar zartarwa, farawa da shi kansa shugaba Tinubu"
Ya kuma zargi majalisar zartarwar da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da alhakin naɗa masu takardun bogi a muƙamai.
Inda ya ce murabus ɗin da ministan kimiyya da fasaha na ƙasar, Uche Nnaji, ya yi a ranar Talata ya ƙara nuna munin rashin sanin ya kamata na gwamnatin Bola Tinubu.
Ya yi nuni da cewa abin da ya kamata a ɗauka a matsayin abun kunya ga ƙasa, amma an ɗauke shi a matsayin 'ajiye aiki bisa raɗin kai,' a wani yunƙuri na tsarkake wata badaƙala "a gwamnatin da ɗabi'un bogi suka yi mata katutu".
"Bai kamata a ce an bar Uche Nnaji ya yi murabus a raɗin kansa ba. Kamata ya yi a ce an kore shi, kuma a hukunta shi kan yaudara da kuma ƙarya a kan abun da bai mallaka ba. "
Abun da ya ƙara mai da lamarin ya zama abun kunya shi ne " Hukumar DDS ɗin da ta ƙi amincewa da Mallam Nasir el-Rufai saboda zargin 'damuwar kan batun da ya shafi tsaro,' ita ce ta amince da Uche Nnaji."
Atiku ya kuma yi tsokaci kan zarge-zargen da ake yi wa shi kansa shugaba Tinubu kan shekarunsa da takardun karatunsa. Inda ya ɗora ayar tambaya cewa, dama ya za a yi barewa ta yi gudu ɗanta yayi rarrafe?
Inda ya ƙara da cewa ƴan Najeriya sun cancanci su san gaskiya kan mutanen da ke jagorantarsu.
A cewarsa, lokaci ya yi da za a tsamo ƙasar daga dagwalon rashin gaskiya, a maido da martabar al'umarta.
Sai dai a wani binciken da BBC ta yi a baya ta gano cewa, babu wasu ƙwararan shaidun da ke nuna cewa takardun karatun Shugaba Tinubu na jami'ar Chicago na bogi ne.