Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya - Laraba, 04-12-2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Laraba, 04-12-2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. 'Yanbindiga sun sace kansila da mutum 8 a jihar Kogi

    Hoton 'yanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu rahotanni na cewa 'yanbindiga sun sace wani sabon kansila da kuma mutum takwas a yankin ƙaramar hukumar Kabba-Bunu da ke jihar Kogi a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa 'yanbindigar sun kai hari ne a cikin daren da ya gabata da misalin ƙarfe 1:00, inda suka sace mutanen daga gidajensu, ciki har da sabon kansilan da ke wakiltar mazaɓar Odo-Ape Hon. Alaba Ope.

    Wani da ya ga yadda lamarin ya faru, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce 'yanbindigar sun buɗe wuta ne da suka shiga garin da misalin ƙarfe ɗaya na dare, kafin su bi gida-gida su kamo waɗanda suka yi garkuwa da su.

    Kusan mako uku baya, aka sace mutum uku da suka haɗa da wani yaro mai shekara takwas a garin.

    Jaridar ta ce ta kakakin 'yansanda na jihar SP William Anya, bai bayar da amsar saƙon da ta aika masa ba na samun bayani game da lamarin, amma ta ce wani babban jami'in tsaro na gwamnati ya tabbatar mata da labarin.

  2. Fargabar tsaro ta sa Firaministan Isra'ila zai bayar da bahasin kotu a ɗaki

    Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, AP

    Alƙalai a shari'ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Benjamin Netanyahu, sun amince cewa Firaministan na Isra'ila na iya bayar da shaida a cikin wani ɗaki na musamman a Tel Aviv idan ya gurfana gaban kotu a mako mai zuwa.

    Jami’an tsaro sun bayar da shawarar hakan ne ga kotun da ke birnin Ƙudus.

    Mista Netanyahu ya buƙaci a samar da tsare-tsaren tsaro na musamman don sauraron ƙarar, inda zai bayar da shaida kan zarge-zargen da ake yi masa a wasu ƙararraki daban-daban guda uku inda ɗaya daga cikinsu ta shafi batun cin hanci.

    Har kullum Mista Netanyahu na kafewa cewa babu wani abu na laifi da ya aikata.

  3. Lauyoyin Trump sun nemi a soke hukuncin ɗaurin da ke gaban shugaban

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Lauyoyin da ke kare Donald Trump sun miƙa buƙata a hukumance ta a soke hukuncin da ke kan shugaban na Amurka mai -jiran-gado kan zargin da aka yi masa na biyan kuɗin toshiyar baki kafin komawarsa fadar White House.

    Jagoran lauyoyinsa, Todd Blanche - wanda Trump ɗin ya zaba a matsayin mataimakin babban lauyan gwamnati - ya ce rashin soke hukuncin zai daburta shirin karɓar mulkin shugaban na Amurka mai -jiran-gado.

    Ya kuma kawo masa cikas wurin gudanar da al'amuran mulkin Amurkar.

    A watan Mayu ne aka samu Mista Trump da laifin jirkita bayanan kasuwanci domin ɓoye kuɗaɗen da ya biya wata fitacciyar mai fina-finan batsa.

    Laifin dai na ɗauke da hukuncin ɗaurin shekara huɗu a gidan yari.

  4. A yau ake sa ran majalisar Faransa za ta tsige Firaministan ƙasar

    Michel Barnier

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Faransa Michel Barnier na fuskantar ƙuri'ar yanke-ƙauna a majalisar dokokin ƙasar, a yau Laraba.

    Jam'iyyun hamayya sun nemi a kaɗa ƙuri'ar ne bayan da Mista Barnier ya tilasta amincewa da kasafin kuɗinsa na walwalar al'umma a farkon makon nan, duk da cewa bai samu cikakken goyon bayan majalisar ba.

    Mista Barnier dai bai kai kwanaki ɗari da fara aiki a matsayin firaministan ƙasar ba.

    Idan har 'yan majalisar suka rushe gwamnatinsa, lamarin zai jefa ƙasar ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Turai cikin ƙarin rikicin siyasa.

    Muddin ba wani abu ne ya sauya ba, gwamnatin ta Barnier za ta kasance ta farko da aka kawar ta hanyar ƙuri'ar yanke-ƙauna a sama da shekara 60, kuma a lokacin da Faransar ke faman yadda za ta shawo kan gagarumin giɓin kasafin kuɗi.

  5. An fara yunƙurin tsige shugaban Koriya ta Kudu

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, OTHERS

    Jam'iyyun hamayya a Koriya ta Kudu sun gabatar da ƙudirin tsige shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol bayan da ya yi yunƙurin kafa dokar soji a ƙasar.

    Mista Yoon ya janye ƙudurin ne bayan 'yan majalisar dokokin sun kaɗa ƙuri'ar daƙile matakin.

    Ƙungiyoyin ƙwadago, har da ma jam'iyyar Mr Yoon, duk sun yi kira gare shi da ya yi murabus.

    Wani ɗan majalisa na babbar jam'iyyar hamayya ta Democratic Party, Kim Byung Joo ya ce jam'iyyarsu za ta kare al'ummar ƙasar har sai inda ƙarfinsu ya ƙare.

    Ya roƙi 'yan kasar da su tsaya tare da jam'iyyar kuma su taimaka wajen kare Jamhuriyar Koriya

  6. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Laraba - Tabawa ranar samu

    Ni, Muhammad Annur Muhammad, zan kasance da ku, domin kawo muku labaran, daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku yi muhawara.

    A yi jimirin kasancewa da mu - Mu fara da wannan karin maganar : Harbi ga ɗan jaki gado ne