Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye da muke kawo muku daga nan sashen Hausa na BBC.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Laraba, 04-12-2024
Muhammad Annur Muhammad
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye da muke kawo muku daga nan sashen Hausa na BBC.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta dakatar da wasu manyan jami’anta guda huɗu da aka samu da zargin sun saci kuɗin da yawansu ya kai naira miliyan arba’in da uku na wani ma’aikacin wani kamfani da suka kama ba tare da an ba su umurni ba a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Bincike ya tabbatar da cewa sun kama mutumin ne a shekarar 2023 da ta gabata lokacin da zai fita da kuɗin a madadin kamfanin da ya ke yi wa aiki.

Asalin hoton, Handout
Ƙungiyar tarayyar turai ta yi kakkausar suka ga matakin Taliban na dakatar da mata a Afghanistan shiga makarantun koyon aikin ungozoma da aikin jinya.
Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin take haƙƙn ɗan'adam da kuma mataki mara hujja na hana mata samun ilimi. Daga nan ƙungiyar ta buƙaci Taliban ta soke matakin.
Taliban dai ba ta ce uffan ba game da hukuncin, to amma dalibai sun shaida wa BBC cewa jami'an Taliban ɗin sun ba cibiyoyin bayar da horo umarnin cewa su dakatar da horar da mata har sai yadda hali ya yi.
Sabrina Saqeb, tsohuwar mamba ce a majalisar dokokin Afghanistan wadda yanzu ke zaune a Canada ta shaida wa BBC cewa, ta ce matsalar ba wai ta ƴanci samun ilimi ko yin aiki ba ce, inda ta ƙara da cewa matakan za su shafi yanayin rayuwar ƴanƙasar a nan gaba.
Batun matsin tattalin arzikin da kasar Ghana ta shiga a baya-bayan nan ya kankane ajandar yakin neman zaben shugaban ƙasar da ke tafe ranar Assabar.
Yanzu haka ƴan takarar manyan jam’iyyun NDC da NPP kowanensu na amfani da halin da ƙasar ta shiga na matsin tattalin arziki domin jan hankalin masu kaɗa ƙuri’a.
Ƴanƙasar da dama sun bayyana takaicinsu kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Aƙalla mutum 12 ciki har da ƙananan yara ne suka mutu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza.
Likitoci sun ce harin ya faru ne a sansanin al Mawassi, wato wani yanki da Isra'ila ta keɓe a matsayin tudun mun tsira. Dubban Falasɗinawan da suka rasa muhallansu ne ke neman mafaka a wajen.
Har kawo yanzu babu wani martani daga Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images
'Yanmajalisa a Faransa sun kaɗa ƙuri'ar yanke-ƙauna, wadda ta yi sanadiyar tsige firaministan ƙasar Michel Banier.
Jam'iyyun hamayya ne suka yi kira da aka kaɗa ƙuri'ar bayan da Mr Banier ya yi amfani ƙarfin ikonsa wajen tilasta garambawul a harkokin tsaro.
Mafiya rinjayen ƴanmajalisar sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige shi - ƙuri'a 331 - kimanin wata uku bayan Shugaban Ƙasa Emmanuel Macron ya naɗa shi.
Yanzu dai Barnier ne zai ci gaba da riƙe muƙamin kafin shugaban ƙasar ya naɗa wanda zai maye gurbinsa.

Asalin hoton, Tinubu/Facebook
A safiyar yau Laraba ne tsoffin sojojin Najeriya suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja, kan rashin biyansu haƙƙokinsu.
Ɗaruruwan tsoffin sojojin waɗanda suka ɗaura baƙaƙen ƙyallaye a damatsansu, sun yi cincirindo a bakin kofar shiga ma'aikatar kuɗi ta Najeriya suna rera waƙoƙi tare ɗaga kwalaye.
Tsofaffin sojojin na neman a biya su kashi 20 zuwa kashi 28 cikin ɗari na ƙarin albashi, sannan a ba su cikon kuɗin da aka biya su tun daga Watan Janairu zuwa Nuwambar 2024.

A jihar Kano, ya yin da yanayin sanyi da kaɗawar iska ke ƙaruwa, hukumar kashe gobara ta ce an yi asarar dukiya ta fiye da naira miliyan ɗari da talatin sanadiyar tashin gobara.
Hukumar ta ce a cikin watan Nuwamban da ya gabata, an samu tashin gobara har arba’in da uku kuma a ciki mutum uku suka rasa rayukansu.
A irin wannan lokaci na sanyi dai ana samun ƙaruwar amfani da wuta don ɗumama jiki ko tafasa ruwan zafi lamarin da ke haddasa gobara idan aka yi sakaci.

Asalin hoton, State House
Najeriya da Afirka ta Kudu sun fara aiki da kwamatin da suka kafa a tsakaninsu na inganta harkokin zuba jari da kuma tattalin arziki, a cewar gwamnatin Afirka ta Kudun.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyrill Ramaphosa ne ya sanar da hakan ranar Talata a birnin Cape Town yayin tattaunawa da 'yankasuwar manyan ƙsashen mafiya girman tattalin arziki a Afirka.
Yayin ganawar, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da tabbacin cewa ƙasarsa za ta tabbatar da tsaro, da kwanciyar hankali, da dokokin da hajojin Afirka ta Kudu za su samu tagomashi a Najeriya.
Tinubu ya kuma nemi Afirka ta Kudu da ta yi hakan ita ma.
A yau Laraba ake sa ran Tinubu zai koma Najeriya bayan shafe kwana uku a ziyarar aikin, da kuma wasu kwana huɗun a Faransa.

Asalin hoton, Abdulmumin Jibrin
Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar Ƙiru da Bebeji na jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce ba ɗari bisa ɗari yake goyon bayan ƙudurorin gyara haraji ba, sannan ya ƙara da cewa yana bayar da haƙuri.
Kofa ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba, inda a ciki ya ce, "babu wurin da ko sau ɗaya na ce ina goyon bayan sababbin dokokin haraji ɗari bisa ɗari."
A cewarsa, "Abin da na ce (shi ne) akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga yankin arewa da ma Najeriya. Kuma mu ƴan majalisa na yankin arewa mu yi amfani da rinjayen da muke da shi a majalisa mu yi tsayin-daka mu goyi bayan duk wasu ƙudurorin da za su amfani arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankinmu da suke cikin kudurorin. Sannan mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu, ko mu gyara su ta yadda ba za su cutar da mu ba."
A cikin rubutun ya ƙara da cewa yana so ne yankin arewa su yi amfani damar dokar wajen bijiro da wasu sabbin hanyoyi, "mu shigar da su a cikin kundin ƙudirorin," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "ban taɓa ba, kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata ko Arewa da ma Najeriya ba."

Asalin hoton, ORTN
Kamfanin makamashin nukiliya na Faransa Orano, ya ce gwamnatin soji ta Nijar yanzu ta ƙwace ayyukan da ake yi na haƙo Uranium a ƙasar.
A watan Yuni ne mahukuntan ƙasar suka soke lasisin aikin kamfanin na Orano a Nijar, ƙasar da take ɗaya daga cikin mafiya arziki Uranium a duniya, inda daga lokacin Orano ya dakatar da aikinsa.
Wakilin BBC ya ce kamfanonin haƙar ma'adinai a Nijar sun jima a ƙasar fiye da shekaru 50, inda ake yawan samun rikici da gwamnatocin ƙasar dangane da ayyukan wasu kamfanonin haƙar ma'adinan.
Tun bayan da suka yi juyin mulki a ƙasar a watan Yuli, sojojin suka ce za su yi garambawul a dokokin ayyukan kamfanonin da suke haƙar ma'adinai a ƙasar.
Nijar ce take fitar da kusan kashi biyar da uraniun da ake amfani da shi a duniya, wanda hakan ya sa ta shiga cikin ƙasashen 10 da suka fi fitar da ma'adinin wanda ake amfani da shi wajen sana'anta nukiliya.
Kafin juyin mulkin, Nijar ce take samar da kashi 15-20 na uraniun da Faransa ke amfani da shi.
Orano ta kwashe watanni tana ƙorafin cewa ana kawo mata tangarɗa a harkokinta na haƙo ma'adininin a Somair, wanda kashi 36.6 na wurin mallakin Nijar ne.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, AFP
Kusan dai za a ce dukkannin ‘yantakarar guda 12 na da muradai masu kama da juna a fannin lafiya da tattalin arziki da ilimi da samar da ayyukan yi ga al’ummar kasa musamman matasa.
To sai dai an fi mayar da hankali kan alkawurran manyan ‘yantakarar guda biyu wato mataimakin shugaban kasa, Mahamudu Bamuwua na jam’iyyar NPP da tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahma na jam’iyyar NDC kasancewarsu gaba-gaba a takarar.
Ƙasar Ghana dai na cikin yanayin matsin tattalin arziƙi inda a yanzu haka take da nauyin bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 51.67, baya ga rashin aikin yi da kuma rashawa da cin hanci da suka yi wa ƙasar kakatutu.
Bisa waɗannan alƙawurra ne da manufofin 'yantakarar, masu zaɓe a Ghana kimanin miliyan 19 za su yi zaɓe su darje domin duk inda ka je tattaunawar da ake yi ke nan.