Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Badriyya Tijjani Kalarawi, Usman Minjibir da Ahmad Tijjani Bawage

  1. Falasdinawa sun fara komawa arewacin Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Falasdinawa sun shafe kwanaki a iyakar arewacin Gaza domin komawa gidajensu

    Falasdinawa sun fara komawa arewacin zirin Gaza, bayan Isra'ila ta sanar da cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas, kan sako karin Isra'ilawa shida da ta ke tsare da su a cikin makon nan.

    Cikin wadanda za a saki har da Arbel Yehud da wasu karin farar hula. A ranar Lahadi Hamas ta saki sojojin Isra'ila hudu, amma babu Yehud a cikinsu, lamarin da ya fusata Isra'ila ta ce an saba sharuddan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

    Tun da fari an amince a yarjejeniyar a fara sakin farar hula, ayi musayarsu da farar hular Falasdinawa da ake tsare da su gidajen kason Isra'ila.

    Tun dai bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita wutar, Hamas ta saki 'yan Isra'ila bakwai da ta ke tsare da su, ya yin da ita ma Isra'ilar ta sako Falasdinawa kusan 300 da ke hannunta.

  2. Budewa

    Masu bibiyar mu Barkan mu da safiyar ranar Litinin.

    Wannan shafi zai kawo mu ku labarai da rahotanni kan wainar da ake toyawa a Najeriya da wasu sassan duniya, kamar yadda muka saba a kullum.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara, domin sanin halin da duniya ke ciki.