Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Zelensky zai je Turkiyya domin farfaɗo da tattaunawar zaman lafiya da Rasha

    Zelensky da Erdogan

    Asalin hoton, EPA

    Volodymyr Zelensky ya ce zai yi tafiya zuwa Turkiyya a ranar Laraba a ƙoƙarinsa na sake farfaɗo da tattaunawar zaman lafiya da Rasha.

    Sanarwar shugaban Ukraine ɗin na zuwa ne a yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da kai hare hare da ƙasa, yayin da hare hare ta sama da jirage marasa mataka da makamai masu linzami ke lalata wasu cibiyoyin samar da makamashi na Ukraine.

    A baya Turkiyya ta karɓi baƙuncin tawagogin Ukraine da Rasha a tattaunawar da suka yi a baya, sai dai zuwa yanzu ba a tabbatar da ko da wa Zelensky zai gana ba a wannan karon, amma majiyoyi daga Turkiyya sun ce wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff zai masa rakiya.

  2. Yara biyu cikin ƴan matan da aka sace a Kebbi sun kuɓuta

    Yara biyu daga cikin ɗalibai fiye da ashirin da ƴan bindiga suka sace a makarantar sakadire da ke garin Maga a karamar hukumar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi sun yi nasarar kuɓuta.

    Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Hussaini Aliyu Bena ya shaidawa BBC cewa ƴan matan sun zille ne daga hannun ƴan bindigar kafin su yi nisa cikin dajin.

    Ya kuma ce ƴan matan na cikin ƙoshin lafiya, kuma tuni aka miƙa su wurin iyayen su.

    Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa jam'ian tsaro na ci gaba da aikin neman sauran ɗaliban.

  3. Jami'an tsaron Najeriya sun bazama neman ɗaliban da aka sace a Kebbi

    sojoji a jere rike da bindiga

    Asalin hoton, NIGERIAN ARMY

    Hukumomi a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wata tawagar sojoji da ƴan sanda da ƴan sa kai sun bazama dazukan da ke yankin domin farautar ƴan bindigar da suka sace ƴan mata fiye da ashirin a wata makarantar kwana a ranar Litinin.

    Wani mai magana da yawun gwamnan jihar ya ce gwamnan na tsara wani shiri domin tabbatar da an ceto ƴan matan.

    Jihar Kebbi dai na samun ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.

  4. 'Za mu yi aiki tare da jami'an tsaro wajen dawo da ƴan matan da aka sace'

    gwamnan jihar Kebbi

    Asalin hoton, Dr Nasir Idris Kauran Gwandu/facebook

    Gwamnan jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya, Nasir Idris ya tabbatarwa da iyayen ɗaliban da ƴan bindiga suka sace a jihar cewa gwamnatinsa za ta yi aiki da jami'an tsaro wajen dawo da ƴan matan gida lafiya.

    Gwamnan wanda ya katse ziyarar aiki da ya kai babban birnin ƙasar Abuja, ya kai ziyara garin Maga da ke karamar hukumar Danko Wasagu, inda lamarin ya faru domin jajantawa iyalan wadanda abin ya rutsa da su.

    '' Mun tattauna da iyayen ƴan matan, mun basu tabbaci da ƙwarin gwiwar cewa za muyi duk mai yiwuwa wajen ceto ƴaƴansu,'' a cewar shi.

    Ya kuma ce ya gana da masu ruwa da tsaki domin neman shawarar su kan yadda za a kaucewa sake faruwar lamarin.

    A jiya Litinin ne dai wasu ƴan bindiga suka kai hari kan makarantar kwana ta yan matan da sanyi safiya, suka kwashe yara aƙalla 25, tare da kashe malami ɗaya da mai gadin makarantar.

  5. Najeriya ta soma tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi

    Ministan harkokin wajen Najeriya

    Asalin hoton, @YusufTuggar

    Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce ƙasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a ƙasar.

    A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa a kai shi ne yadda za su haɗa kai wajen magance matsalolin tsaro don amfanin duniya.

    A farkon watan Nuwamban nan Trump ya ce ya bai wa ma'aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za ta kai hari Najeriyar.

    Sai dai ministan ya ce ba ya tunanin Amurka za ta yi hakan, '' muna ci gaba da tattaunawa, kuma ana samun ci gaba a tattaunawar, mun wuce nan yanzu'', kamar yadda ya bayyana.

    Trump ya ce addinin Kirista na fuskantar barazana a ƙasar da ke yammacin Afirka.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa idan Najeriya ba ta kawo ƙarshen kashe kashen ba, Amurka za ta kai hari.

    Najeriya mai yawan al'umma kusan miliyan 230, ta rabu kusan daidai tsakanin kudancin ƙasar da akasari kiristoci ne, da kuma arewacin ƙasar mai rinjayen musulmai.

    Akan samu hare-hare da rikice-rikice da dama da kan shafi dukkanin ɓangarorin biyu.

  6. Trump ya yaba wa MDD kan amincewa da shirinsa na zaman lafiyar Gaza

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da amincewa da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya, da ke goyon bayan shirinsa na zaman lafiya a Gaza da kuma share fagen fara aiwatar da mataki na biyu na shirin.

    Shirin ya ƙunshi batun kwance damarar Hamas da kuma tura dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa zuwa Gaza.

    Tuni dai Hamas ta yi watsi da kudurin.

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce yanzu kamata ya yi a inganta ayyukan jin kai a yankin.

    Wasu Falasdinawa a zirin Gaza dai sun yi Allah wadai da shirin suna masu cewa zai ci gaba da dawwamar da su karkashin mulkin kasashen waje.

  7. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Aisha Aliyu Ja'afar ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa da kuma kallon bidiyo.