Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 11/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Muhammad Annur Muhammad

  1. Mummunar ambaliya ta janyo gurɓatar muhalli a Sudan ta Kudu

    Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, David Bojo Leju

    Wani bincike da BBC ta gudanar ya ga shaidun da ke nuna cewa mummunar ambaliyar ruwa a Sudan ta Kudu ta haifar da gurɓatar muhalli daga masana'antar mai ta ƙasar.

    A shekaru biyu da suka wuce, matsananciyar ambaliya da ke da nasaba da sauyin yanayi ta nutsar da kashi saba'in cikin ɗari na jihar Unity.

    Wani tsohon injiniyan ƙungiyar da ke kula da rijiyoyin mai na jihar ya zargi kamfanin da rashin yin abin da ya dace tare da gurɓata muhalli.

    Mazauna yankin sun ba da rahoton cewa an samu ɓarkewar cutuka tsakanin ƙananan yara.

    BBC ta tuntuɓi ofishin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu da kuma kamfanin G-POD, sai dai ba su ce uffan ba kan wannan batu.

  2. An tsige Firaministan ƙasar Haiti

    Garry Koniyal

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin majalisar zartarwa ta Haiti ya tsige firaministan ƙasar, Garry Koniyal, wata shida bayan hawa kan kujerar.

    Kafar watsa labaran ƙasar ta wallafa Umarnin zartar da hakan da mambobi takwas daga cikin tara da kwamitin riƙon ƙwaryar suka sanyawa hannu.

    Haka kuma kwamitin ya sanar da sabon wanda ya naɗa muƙamin, Alix Didier wani ɗan kasuwa wanda ya isa ƙasar jiya Lahadi daga ƙasashen ƙetare.

    Wakilin BBC ya ce mista Koniyal ya bayyana wa kwamitin cewa ba su isa su tsige shi ba, majalisar ƙasar ce kadai za ta iya yin haka, kuma babu ita a yanzu.

  3. Yaƙin Gaza da Lebanon: Shugabannin ƙasashen Musulmi na taro a Saudiyya

    Gaza and Lebanon

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabannin ƙasashen Musulmi na haɗuwa a Saudiyya domin gudanar da taron gaggawa kan batun yaƙin Gaza da Lebanon.

    Wakilan ƙasashen na son ganin Isra'ila ta kawo ƙarshen yaƙin ta da Hamas da Hezbollah.

    Sai dai batun nasarar Trump ne zai mamaye taron saboda yana matuƙar goyon bayan Isra'ila, kuma akwai yiwuwar ya ɗauki mataki kan Iran.

    Iran dai ta sha alawashin mayar da martani kan hare-haren Isra'ila.

  4. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Litinin.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.