Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 15/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba da Aisha Babangida

  1. Tinubu zai kafa rundunar masu tsaron dazuka a faɗin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron dazuka a ƙasar baki ɗaya, domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a Najeriya.

    A karkashin wannan shiri, za a ɗauki sama da masu tsaro 130,000 da za su kasance da kayan yaƙi da horo na musamman domin kare dazukan ƙasar guda 1,129.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, wanda ya wallafa ta a shafinsa na X.

    Sanarwar ta ce "Wannan mataki na tsaro an amince da shi ne yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar ranar Litinin.'

    "A cikin wannan tsari, shugaba Tinubu ya umurci kowace jiha da ta ɗauki ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 domin zama masu tsaron daji, dangane da ƙarfin kuɗin jiharsu." in ji sanarwar.

    Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma ma’aikatar kula da muhalli ne za su sa ido kan aikin ɗaukar masu tsaron da horar da su domin tabbatar da cewa sun samu cikakken shiri da kayan aiki na zamani da ya kamata.

    Babban aikin da ake sa ran masu tsaron dajin za su yi shi ne fatattakar masu tayar da ƙayar baya da miyagu da suka fake a cikin dazuka suna aikata laifuka.

    Sanarwar ta ce "Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dole ne a horas da su sosai kuma a ba su makamai masu ƙarfi domin su iya kare ƙasar."

  2. Sabbin hare-haren Isra'ila sun halaka fiye da mutum 40 a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Fiye da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a sassa daban-daban na Gaza, a cewar majiyoyin asibiti.

    Rahotanni sun nuna cewa an kai gawarwakin aƙalla mutum 36 zuwa asibitoci a kudancin yankin, inda Isra’ila ta ƙara tsananta luguden wuta da daddare.

    Tun daga farkon watan Maris ne dai Isra’ila ta hana kowanne irin kayan agaji shiga Gaza – ciki har da abinci da kayan magani.

    Wannan matakin ya fuskanci suka daga ƙasashen duniya, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda ta gargaɗi cewa akwai "babban haɗarin yunwa" da ke fuskantar Falasinawa miliyan 2.1 da ke zaune a yankin.

    Wani rahoto da UN ta fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa rabin miliyan – ko mutum ɗaya cikin biyar – na fuskantar matsananciyar yunwa a Gaza.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa ana sa ran kusan yara 71,000 ƙasa da shekara biyar za su kamu da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki daga yanzu har zuwa watan Afrilu na shekarar 2026.

  3. Rasha ta ce Putin ba zai halarci tattaunawar zaman lafiya a Istanbul ba

    ...

    Asalin hoton, EPA

    A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya, – amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar.

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban Amurka Donald Trump shima ba zai halarci taron ba – duk da cewa ya nuna sha’awar halarta jiya idan har Putin zai je.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, zai kuma kasance a babban birnin Turkiyya, Ankara a yau don ganawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan inda ya ce zai je taron tattaunawar da Rasha a Istanbul ne kawai idan Putin ya halarta.

    Tun daga watan Disamba na shekarar 2019 ne ba a sake ganawa a zahiri tsakanin Putin da Zelensky ba.

  4. An kashe fiye da shanu 100 a sabbin hare-hare a Filato

    ...

    Asalin hoton, AFP

    An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da fiye da shanu 100 a jerin hare-haren da aka kai kan makiyaya a ƙauyuka biyu da ke cikin Kananan Hukumomin Jos na Kudu da Jos na Arewa na Jihar Filato.

    Hare-haren, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga ne suka kai ta hanyar buɗe wuta kan makiyayan da ke kiwo, sun sake jaddada yadda tsaro ya taɓarɓare a yankunan da ke fama da rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, rikice-rikicen da a kullum ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

    Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi matasa ‘yan kabilar Berom daga ƙauyukan da abin ya shafa da hannu a hare-haren.

    Sai dai shugabancin ƙungiyar matasan Berom ya musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin farfaganda kawai.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin farko ya faru ne da yammacin Talata a kauyen Gero da ke Jos na Kudu, yayin da na biyu ya faru da safiyar Laraba a kauyen Darwat da ke cikin ƙaramar hukumar Riyom.

    A cewar Babayo, makiyaya uku sun jikkata a harin da aka kai a Gero inda ɗaya daga cikinsu yana karɓar magani a asibiti da ke Jos, yayin da sauran biyun ke jinya a asibitin Sojoji na Rukuba Barracks, Jos.

    • Me ya sa aka gaza warware rikice-rikicen jihar Filato?
    • Me ya jawo ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya?
  5. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Alhamis

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran

    Ku kasance tare da mu.