Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 04/04/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage

  1. Yadda ɗora harajin Amurka ta kassara kasuwar hanun jarin Asia

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    An sake samun koma-baya a kasuwannin hannayen jarin Asiya sakamakon harajin da Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta kan ƙasashe a ranar Laraba.

    Kamfanin Nikkay na Japan ya yi ƙasa da fiye da kashi biyu da rabi cikin 100 yayin da Hang Seng da ke Hong Kong ya faɗi da kashi ɗaya da rabi cikin 100.

    A jiya Alhamis ne, kasuwar hannayen jari ta Wall Street ta fuskanci koma-baya mafi muni da ta taɓa gani tun farkon watannin annobar korona, Dow Jones ma ta yi ƙasa da kusan kashi huɗu cikin 100.

    Sai dai Shugaba Trump ya shaida wa ƴanjarida cewa al'amura na tafiya daidai kuma tattalin arzikin Amurka zai haɓaka.

    Trump ya ƙara da cewa kasuwanni za su bunƙasa, hannun jari zai samu tagomashi, Amurka kuma za ta haɓaka.

  2. Rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi babban rashi ne - Atiku

    Dutse

    Asalin hoton, FACEBOOK/DUTSEN TANSHI MASJID BAUCHI

    Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya aike da saƙon jaje na rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

    A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya bayyana marigayin da mutum mai kira da a zauna lafiya.

    Ya ce, "Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi fitaccen malami ne kuma mai kira da a zaua lafiya a tsakanin musulmi. Kalamansa na ƙarshe a filin idi a Bauchi ma nanata kira ya yi ga al'umma musulmi da su zauna lafiya.

    "Iliminsa da hikimarsa sun matuƙar amfanar da al'umma da dama," in ji Atiku, wanda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, "ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma da al'umma baki ɗaya."

    "Ina addu'ar Allah Ya sa ya huta, ya saka hi a aljanna. Sannan ina addu'ar Allah ya ba iyalansa haƙurin rashi."

  3. Ba mu da hannu a kashe-kashen Filato – Fulani

    Gan Allah

    Asalin hoton, Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria/Facebook

    Ƙungiyar makiyaya ta Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN), ta musanta zargin fulani da hannu a kashe-kashen da aka yi na kwana-kwanan nan a jihar Filato.

    Shugaban ƙungiyar, Garba Abdullahi ne ya ƙaryata zargin, inda ya ce an ƙirƙira maganar ce domin a ɓata sunan fulani.

    "Muna jajanta wa waɗanda suka rasa ƴanuwansu, kuma muna Allah wadai da kashe-kashen. Dabbanci ne, kuma bai dace ba. Amma mu fulani muna faɗa da babbar murya cewa zargin ƙungiyar ci gaban al'adun mutanen Bokkos babu tushe, zargin da suke yi na fulani na da hannu a kisan shaci-faɗi ne kawai.

    "Muna kira ga ƴan Najeriya da gwamnati da jagororin al'umma da su yi watsi da wannan zargin, domin babu hannun al'ummar fulani a ciki," kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

  4. Kotu ta tabbatar da tsige shugaban Koriya ta Kudu

    Koriya ta Kudu

    Asalin hoton, AFP

    An tsige shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol daga muƙaminsa, bayan da kotun tsarin mulki ta amince da matakin da majalisar dokoki ta ɗauka a kansa a baya.

    An sauke Mista Yoon daga muƙaminsa ne bayan yunƙurin da ya yi na ayyana dokar soji a watan Disamban bara, wanda ya haifar da rikicin siyasa mafi muni a ƙasar.

    Za a gudanar da zaɓe cikin kwana 60 domin zaɓar wanda zai maye gurbinsa.

    Masu zanga-zangar adawa da Mista Yoon sun yi ta murnar hukuncin da kotun ta yanke a kan titunan babban birnin ƙasar.

    Wakiliyar BBC ta ce dubban mutane sun haɗu domin murnar abin da suke ganin shi ne adalci, alƙalai takwas da suka kaɗa ƙuri'ar tsige tsohon shugaban ƙasa Yoon.

    Sai dai lamarin bai yi wa magoya bayansa daɗi ba, amma hukumomin ƙasar sun buƙaci su amince da hukuncin kuma su kwantar da hankalinsu.

  5. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin namu na labaran kai-tsaye na yau Juma'atu babbar rana.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.