Yadda ɗora harajin Amurka ta kassara kasuwar hanun jarin Asia
An sake samun koma-baya a kasuwannin hannayen jarin Asiya sakamakon harajin da Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta kan ƙasashe a ranar Laraba.
Kamfanin Nikkay na Japan ya yi ƙasa da fiye da kashi biyu da rabi cikin 100 yayin da Hang Seng da ke Hong Kong ya faɗi da kashi ɗaya da rabi cikin 100.
A jiya Alhamis ne, kasuwar hannayen jari ta Wall Street ta fuskanci koma-baya mafi muni da ta taɓa gani tun farkon watannin annobar korona, Dow Jones ma ta yi ƙasa da kusan kashi huɗu cikin 100.
Sai dai Shugaba Trump ya shaida wa ƴanjarida cewa al'amura na tafiya daidai kuma tattalin arzikin Amurka zai haɓaka.
Trump ya ƙara da cewa kasuwanni za su bunƙasa, hannun jari zai samu tagomashi, Amurka kuma za ta haɓaka.