Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 04/04/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu dawo domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila da Turkiyya sun ce ba sa neman juna da rikici

    Isra'ila da Turkiyya sun ce ba sa neman rikici da juna a Siriya bayan Isra'ila ta kai hare-hare ta sama kan wuraren da ta ce soji ne.

    Sai dai ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce matakin na Isra'ila zai iya kawo rashin tabbas a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Akwai rahotannin da ke cewa Turkiyya na fatan jibge sojojinta a wasu sansanonin da Isra'ila ta kai wa hari.

    Wani jami'in Isra'ila ya ce gwamnatinsa ba ta son ganin yadda Turkiyya ta mamaye iyakarta.

  3. An hana tawagar AU da ta je Sudan ta Kudu ganin mataimakin shugaban ƙasar

    An hana tawagar ƙungiyar Tarayyar Afirka AU - da suka je Sudan ta Kudu, inda ake fargabara ɓarkewar yaƙin basasa - ganin mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar.

    Tawagar ta je ƙasar ne da nufin yayyafa ruwa kan rikicin da ke neman ɓarkewa tsakanin shugaban ƙasar Salva Kiir da mataimakin nasa Mista Machar, wanda a yanzu ke ƙarƙashin kamun talala.

    An shaida wa tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Burundi, Domitien Ndayizeye, cewa babu wanda zai iya ganin mataimakin shugaban ƙasar, har sai ya bayyana a gaban kotu.

    Haka ma wani yunƙurin na daban - ƙarƙashin jagorancin shugaban Uganda, Yoweri Museveni da tsohon firaministan Kenya, Raila Odinga - bai samu nasara ba.

  4. Harin Rasha ya kashe mutum 14 a birnin Kryvyi - Zelensky

    Shugaban ƙasar, Volodymyr Zelensky ya ce harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan wani gini a birnin Kryvyi ya kashe mutum 14.

    Rahotonni sun ce shida daga cikin mutanen ƙananan yara ne.

    Shugaba Zelensky ya ce harin na baya-bayan nan hujja ce da ke nuna cewa Rasha ba ta shirya wa yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ke yunƙurin yi ba.

    Mista Zelensky ya wallafa gawarwakin mutanen da aka kashe a wani filin da yaran ke wasa a kusa da ginin.

    Birnin Kryvyi Rih - wanda a baya-bayan nan ya sha fama da hare-hare - ya kasance mahaifar Mista Zelensky.

  5. Firaministan Indiya ya bayyana damuwa kan harin da aka kai wa mabiya Hindu Bangladesh

    Firaministan Indiya, Narendra Modi ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da aka kai kan mabiya addinin Hindu Bangladesh, yayin da yake tattaunawa da shugaban riƙo, Muhammad Yunus.

    Taron - wanda aka gudanar a wani taron yanki a ƙasar Thailand - shi ne na farko tun bayan hamɓarar da gwamnatin firaminista Sheikh Hasina a watan Agustan da ya gabata.

    Sheikh Hasina ta kasance aminiyar Delhi ta kut-da-kut, kuma ana tunanin cewa tana gudun hijira ne a can.

    Shugabannin biyu sun kuma tattauna buƙatar gwamnatin Bangladesh na a taso ƙeyar Sheikh Hasina amma dai ba a bayar da cikakken bayani kan yadda tattaunawar ta gudana ba.

  6. Najeriya ta samu alluran riga-kafin sankarau miliyan guda

    Najeriya ta ƙarbi alluran riga-kafin cutar sanƙarau aƙalla miliyan guda domin yaƙi da cutar a faɗin ƙasar.

    Ƙungiya Gavi mai tallafa wa ƙasashe maso tasowa kan alluran riga kafin ce ta bayyana haka, cikin sanarwar da ta fitar.

    Aƙalla mutum 20 ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar a baya-bayan nan a ƙasar, yayin da aka samu fiye da mutum 800 da suka kamu da ita.

    Ƙungiyar ta ce za a yi wa mutanen da suka kamu da cutar ƴan ƙasa da shekara 30 allurar riga-kafin.

    Ɓarkewar cutar sankarau a Najeriya ba baƙon al'amari ba ne musamman a lokacin zafi.

  7. China ta ƙara wa kayyakin Amurka harajin kashi 34

    China ta mayar wa Amurka martani ta hanyar yi wa kayayyakinta ƙarin harajin kashi 34 cikin 100.

    A ranar Laraba ne Amurka ta bayyana ƙarin haraji ga ƙasashen duniya ciki har da China.

    Shugaban Amurka ya ce gwamnatin China ta kaɗu da matakin nasa.

    Sai dai Gwamnatin Chinan ta ce za ta rage shigar da wasu kayyakin zuwa kasuwannin Amurka.

    Haka kuma Chinan ta lissafa wasu kamfanonin Amurka cikin waɗanda za ta ɗauki mataki a kai.

    Hukumomin na China sun ce matakin zai fara aiki daga ranar Alhamis mai zuwa.

  8. Trump ya kori shugaban hukumar tsaron Amurka

    Gwamnatin Donald Trump ta kori shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Amurka Janar Timothy Haugh.

    Sauke Janar Haugh na zuwa ne yayin da ake ci gaba da korar shugabanni a ma'aikatar tsaron da kuma fadar White House.

    'Yan jam'iyyar adawa ta Democrat sun ce sun "damu matuƙa" da matakin kuma suka ce hakan yana kawo wa tsaron ƙasar cikas.

    Babu tabbas kan dalilin da ya sa aka cire janar ɗin, amma an ɗauki matakin ne bayan ganawar Shugaba Trump da wata 'yar fafutika mai ra'ayin riƙau Laura Loomer a ranar Laraba.

    Rahotonni sun ce Ms Llomer ce ta bai wa Trump shawarar korar wasu ma'aikata bayan ta zarge su da ƙin yi wa shugaban ƙasar biyayya.

  9. Mutuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi babban rashi ne - Gwamna Inuwa Yahaya

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ya bayyana alhinin rasuwar malamin addinin Musulunci Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi yana mai kwatanta ta da "babban rashi".

    Cikin wata sanarwa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana marigayin a matsayin "wanda ake girmamawa wanda kuma ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen gina imanin al'umma".

    Kazalika, gwamnan ya bayyana rasuwar malamin a matsayin "babban rashi ba ga iyalansa da jihar Bauchi kawai ba, har ma da fannin koyar da addinin Musulunci".

    "A madadin gwamnati da al'ummar Gombe, da gwamnonin Arewa 19, ina miƙa ta'aziyya ga iyalan mamacin da gwamnatin Bauchi da al'ummar Musulmi," in ji gwamnan.

    Shehin malamin ya mutu ne a daren Juma'a yana da shekara 68 bayan jinyar da ya yi fama da ita.

  10. Kotu ta haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai

    Mai shari'a Binta Nyako na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio da kuma wasu mutum uku daga tattauana batun shari'arsu da manema labarai.

    Mai shai'a Nyako ta yanke hukuncin ne ranar Juma'a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari'arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu.

    Kotun ta ce daga yanzu babu ɓangaren da zai tattauna da manema labarai dangane da batun.

    Nyako ta kuma haramtawa Akpabio da Natasha da kuma lauyoyinsu daga yaɗa zaman shari'ar kai-tsaye a shafukan sada zumunta.

  11. Darajar naira ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba a baya-bayan nan

    Darajar kuɗin naira a Najeriya ta yi faɗuwar da aka daɗe ba a gani ba a kan dala a wannan makon a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje.

    Ana alakanta hakan da ƙarin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba wa ƙasar.

    Bayanai kan hada-hadar canji daga babban bankin ƙasar CBN, sun nuna darajar ta faɗi zuwa N1,552.53 a kan duk dala 1 a ranar alhamis, saɓanin N1,531.25 duk dala da aka samu ranar Laraba.

  12. Jarumin fina-finan India Manoj Kumar ya rasu

    Fitaccen Jarumi da kuma mai shirya fina-finan Indiya, Manoj Kumar, ya mutu yana da shekara 87.

    Jarumin ya mutu ne a birnin Mumbai bayan fama da jinya da ke da alaƙa da tsufa, a cewar Dr Santosh Shetty na asibitin Kokilaben Dhirubhai Ambani, inda aka kwantar da shi.

    Ɗan fitaccen jarumin, Kunal Goswami, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa Kumar ya shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya.

    Kumar dai ya bar gagarumin tarihi a masana'antar shirya-shirya fina-finai ta Indiya, inda ya haska a fina-finai da dama ciki har da Dus Numbari - waɗanda suka shi shahara a shekarun 1960 zuwa 1970.

    Ƴan siyasa da taurari da kuma masoyansa na ta alhinin rasuwar tasa a shafukan sada zumunta.

    Firaiminista Narendra Modi ya kira shi da "shahararren jarumi da ya haska sinimun Indiya".

    "Muna alfahari da ayyukan Manoj kuma za su ci gaba da ƙara wa masu tasowa ƙwarin gwiwa," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

  13. Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Tinubu

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya ajiye aikinsa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon kakakin na ƙungiyar dattawan arewa ya ajiye aikin ne kimanin mako biyu da suka gabata.

    Sai dai bai bayyana daliinsa na ajiye aikin, inda da ya ce kawai ya ajiye aikin ne saboda wasu dalilai nasa.

    A watan Satumban shekarar 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu na naɗa Hakeem a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

    Ƴan arewa musamman matasa a kafofin sadarwa suna yawan caccakar Hakeem Baba-Ahmed a duk lokacin da aka yi wani abu da suke gani ba a kyautawa arewa ba, musamman saboda tsohon muƙaminsa, inda yake yawan fitowa yana magana a kan abubuwan da suka shafi yankin.

  14. China ta mayar wa Amurka martani ta hanyar ƙarin haraji kashi 34

    China ta mayar wa Amurka martani ta hanyar saka mata ƙarin haraji kashi 34.

    Haka na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban ƙasar Donald Trump ya sanar da sabbin haraje-haraje kan ga ƙasashe a faɗin duniya - inda na China ya kai kashi 54, amma ba a lokaci ɗaya zai yi aiki ba.

    Dukkan kamfanoni da ke son shiga kasuwannin Chia, za su fuskanci ƙarin haraji kashi 34 daga ranar Alhamis ɗin mako mai zuwa.

    Hakan na nufin harajin ramuwa da China ta yi, ya zarce wanda Trump ya sanar.

    Tun bayan komawa fadar White House a watan Janairu, Trump ya ƙara haraji kan kayayyakin China zuwa kashi 20, kafin na ranar Alhamis da ya kai kashi 54.

  15. Pentagon za ta binciki sakataren tsaron Amurka kan kai hari Yemen

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce za ta binciki Sakataren tsaron ƙasar, Pete Hegseth, kan amfani da wani dandalin sada zumunci wajen tattauna batun kai hare-hare Yemen.

    A makon da ya gabata ne aka saka wani sanannen ɗan jarida cikin dandalin sada zumuncin, bisa kuskure.

    Manyan jami'an gwamnati har da mataimakin shugaban ƙasa JD Vance sun wallafa bayanan lokutan kai hare-haren kan Houthi da kuma nau'in makamai masu linzami da jiragen da za a yi amfani da su wajen ƙaddamar da hare-haren.

    Pentagon ta ce binciken zai duba ko Mista Hegseth da sauran mambobin da ke dandalin sun mutunta dokokin amfani da manhajar wajen gudanar da ayyukansu na ofis.

  16. Labarai da dumi-dumi, De Bruyne zai bar Man City a karshen kakar bana

    Kevin de Bruyne ya tabbatar da cewa zai bar Manchester City idan kwantiraginsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana.

    De Bruyne, mai shekara 33, ya lashe kofuna 16 tun bayan komawa City daga Wolfsburg a 2015 - ciki har da kofin Premier shida da gasar zakarun Turai a 2023.

    Ya zura kwallo 106 a wasanni 413 da ya buga wa ƙungiyar, sai dai an fara da shi a wasanni 19 kaɗai a bana.

    "Komai yana da farko da kuma karshe, amma zama na a City ya kasance wani babi mafi kyau a rayuwata," kamar yadda ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Belgium ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

  17. Babu batun sauya Kashim Shettima a zaɓen 2027 - APC

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce maganar da ake yaɗawa cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu na shirin canja mataimakinsa, Kashim Shettima a zaɓen 2027 ba gaskiya ba ce.

    Daraktan watsa labarai na APC na ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim ne ya bayyana hake a wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust, inda ya ce ko kaɗan babu wannan maganar.

    "Raɗe-raɗi ne kawai. Maganganu ne na teburin mai shayi da bai kamata a ɗauka da muhimmanci ba. Don haka a yi watsi da maganar," in ji shi.

    "Ko da ma kuwa Shugaba Tinubu zai canja mataimaki, ba zai ɗauki matakin shi kaɗai ba. Dole sai an tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaju,"

  18. Me ya sa Iran ke bayyana rumbunan makamanta na sirri da ke ƙarƙashin ƙasa a yanzu?

    "Idan muka fara buɗe biranen makamai a kullum tsawon shekara biyu ba za mu gama ba har nan da shekara biyu..."

    Da irin wannan kalaman Iran ta fara bayyana wasu jerin unguwanni na ƙarƙashin ƙasa da ke ɗauke da makamanta masu linzami da za ta yi amfani da su wajen abin da ta bayyana a matsayin ramuwar hare-hare kan Isra'ila da Amurka.

    An ce Amurka ta fara tura jiragen yaƙinta shida a makon da ya gabata masu ƙarfin kai hari da manyan bamabamai a Iran da Yemen, kamar yadda wasu majiyoyi suka faɗa wa kamfanin klabarai na Reuters.

  19. Kotun Ƙoli ta soke shugabancin Abure na jam'iyyar LP

    Kotun ƙolin Najeriya ta jingine shari'ar kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour na ƙasa.

    A wata shari'a da alƙalan kotun guda biyar suka yanke, kotun ƙolin ta ce kotun ɗaukaka ƙara ba ta da hurumin tabbatar tabbatar da sahihancin shugabancin jam'iyya.

    Kotun ta ce batun shugabanci, lamari ne da ya shafi jam'iyya, kuma kotu ba ta da hurumin yin katsalandan.

  20. Hotunan jana'izar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

    A yau Juma'a ne aka gudanar da sallar jana'izar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi a filin Games Village da ke cikin Bauchi.