Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Ahmad Bawage da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Laraba.

    Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.

  2. Gwamnatin Najeriya ta maka MultiChoice mai DSTV a kotu kan ƙara kuɗi

    DSTV

    Asalin hoton, DSTV Nigeria

    Hukumar kula da ayyukan kamfanoni da walwalar kwastomomi ta Najeriya ta kai ƙarar kamfanin MultiChoice Nigeria da ya mallaki DSTV kotu kan zargin karya dokoki.

    Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC) bayyana matakin ne cikin wata sanarwa a yau Laraba.

    A ranar 24 ga watan Fabrairu kamfanin ya bayar da sanarwar ƙara kuɗin da ake biya na kallon tashoshin tauraron ɗan'adam a layin DSTV da GOtv, inda ya fara aiki ranar 1 ga watan Maris.

    Ƙarin ya jawo suka da nuna ɓacin rai daga 'yan Najeriya, abin da ya sa hukumar ta shiga batun, kuma ta nemi kamfanin ya janye ƙarin har sai an kammala bincike.

    Sai dai sanarwar ta FCCPC ta ce MultiChoice bai bi umarnin ba kuma ya ci gaba da aiwatar da aniyar tasa.

  3. Ƙwayar aspirin na taimakawa wajen daƙile yaɗuwar cutar kansa - Bincike

    Ƙwayar aspirin

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana kimiyya a Birtaniya sun ce sun gano yadda ƙwayar maganin aspirin ke iya taimakawa wajen hana wasu nau'ukan cutar daji ko kuma kansa yaɗuwa.

    Binciken da aka wallafa a mujallar Nature ya gano cewa ƙwayar cutar ta aspirin mai rage raɗaɗi kuma mai sauƙin kuɗi na ƙara wa jiki garkuwa domin yaƙar ƙwayoyin cutar dajin.

    Masu bincike a jami'ar Cambridge sun gano haka ne yayin da suke gwaji a kan ɓeraye.

    Wakilin BBC ya ce shin ya kamata masu fama da cutar daji su sha aspirin, amsar ita ce a'a saboda yin hakan na tattare da manyan illoli cikinsu har da shanyewar ɓarin jiki.

  4. Hukumar zaɓen jihar Rivers ta saka ranar sake zaɓen ƙananan hukumomi

    Fubara

    Asalin hoton, @SimFubaraKSC

    Hukumar zaɓen jihar Rivers a kudancin Najeriya ta saka 9 ga watan Agusta a matsayin ranar sake zaɓen ƙananan hukumomi.

    Rahotonni sun ambato shugaban hukumar Adolphus Enebeli na sanar da hakan yayin wata ganawa a yau Laraba da masu ruwa da tsaki a birnin Fatakwal.

    A ranar Laraba da ta gabata ne Kotun Ƙolin Najeriya ta soke zaɓen da hukumar ta gudanar a ranar 5 ga watan Oktoban 2024.

    A gefe guda kuma, majalisar dokokin jihar ta gayyaci shugaban hukumar ya bayyana a gabanta domin yin bayani game da zaɓen.

  5. A shirye muke mu fafata kowane irin yaƙi da Amurka, in ji China

    China

    Asalin hoton, EPA

    China ta gargaɗi Amurka cewa a shirye take don gwabza "kowane irin yaƙi" bayan ta mayar da martani kan ƙarin kayayyakinta da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba.

    Ƙasashen biyu mafiya girman tattalin arziki a duniya na ƙara kusan yaƙin kasuwanci tun bayan da Trump ya sanar da ƙarin haraji kan kayan China.

    Nan take China ta mayar da martani da ƙarin kashi 10 zuwa 15 cikin 100 kan kayan Amurkar.

    "Idan yaƙi Amurka ke nema, ko na haraji, ko na kasuwanci, ko ma wane irin yaƙi, a shirye mu fafata har ƙarshe," kamar yadda ofishin jakadancin China ya bayyana a dandalin X.

    A ranar Laraba Firimiyan China Li Qiang ya sanar cewa ƙasarsa za ta ƙara yawan kuɗin da take kashewa a fannin tsaro da kashi 7.2 cikin 100 a wannan shekarar.

  6. Majalisar Kano ta yi wa dokar tace finafinai garanbawul, Daga Zahraddeen Lawan, Kano

      • Marubuci, Zahraddeen Lawan
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Daga Kano
    Abba El-Mustapha

    Asalin hoton, Facebook/Abba El-Mustapha

    Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da yi wa dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai gyaran fuska.

    Cikin gyare-gyaren har da tilasta wa masu wuraren da ake gudanar da bukukuwa da taruka wato event centres yin rajista.

    Ayyukan hukumar na ɗaukar hankali musamman a arewacin Najeriya saboda yadda ake kai ruwa rana tsakaninta da masu shirya finafinai.

    Majalisar ta amince da gyaran dokar ne wadda aka kafa tun 2001 saboda yadda ɗaukar finafinai ya sauya, abin da ya sa majalisar ta ce tilas sai ana taka wa lamarin birki a wasu abubuwan don kare addini da kuma al’adu.

    "Yanzu hukumar ta kara samun iko a kan abubuwa da dama," a cewar shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Husaini Dala.

    Ya ce daga yanzu babu wanda zai shigo birnin Kano ya yi ta ɗaukar fim ba tare da samun izinin hukumar ba.

    A nasa ɓangare, shugaban hukumar tace fina-finan ta jihar Kano Abba El-Mustapha, ya ja hankalin masu wallafa bidiyo a kafofin sada zumunta waɗanda ake kira da content creators da su guji duk abin da zai taɓa mutuncin addini ko na al'adar bahaushe ko kuma al'ummar jihar Kano.

    Ya ce za su mara wa waɗanda ke bidiyo don nishaɗi ko samun arziki, amma ba zagin mutane ba.

    Bugu da ƙari, El-Mustapha ya ce ƴan social media su sani cewa hukumar tace fina-finai tana da hurumi kan dukkan wani abu da ya saɓa wa addini da al’adu, inda ya ce muddin suka samu korafi akan wani bidiyo ko wani abu da aka saka a shafukan sada zumunta, to za su ɗauki mataki.

    Bayanai na cewa kawo yanzu dai majalisar dokokin jihar ta Kano ta kammala nata aikin na amincewa da gyaran dokar hukumar, abin da ya rage yanzu shi ne gwamnan Kano ya sanya hannu a kai, amma babu tabbas ko zuwa yaushe ne zai yi hakan.

  7. MDD za ta rage yawan abincin da take bai wa ƴan gudun hijirar Rohingya

    Bangladesh ta ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ita cewa za ta rage yawan abincin da ake bai wa ƴangudun hijirar Rohingya daga watan Afrilu sakamakon rashin samun isassun kuɗaɗen ci gaba da tafiyar da shirin.

    Mohammed Mizanur Rahman, babban jami'in da ke kula da sansanonin ƴan gudun hijirar, ya ce za a rage yawan abincin da kowane ɗan gudun hijira ke samu daga kusan dala 13 zuwa dala shida.

    Sabon tsarin zai fara aiki daga 1 ga watan na Afrilu.

    Bangladesh na bai wa kusan ƴan gudun hijirar Rohingya miliyan guda mafaka da tsirarun Musulmai masu fuskantar tsangwama da suka tsere daga Myanmar mai maƙwabtaka sakamakon yaƙi.

  8. Ana zaman ɗar-ɗar a Sudan ta Kudu bayan kama babban hafsan soji

    Ana zaman ɗar-ɗar a Sudan ta Kudu bayan kama babban hafsan sojin ƙasar da kuma ministan albarkatun man fetur.

    Mutanen biyu makusanta ne ga mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar, da dakarun gwamnati suka yi wa gidansa ƙawanya.

    Mista Machar da abokin hamayyarsa shugaba Salva Kiir sun fuskanci ƙalubale wajen aiwatar da yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya ta shekarar 2018 wadda a ƙarshe ta zama yaƙin basasa.

    Kamen nasu na zuwa ne sakamakon rahotannin da aka samu cewa wasu ƙungiyoyin ƴantawaye da suka ƙwace iko da wani muhimmin gari kusa da iyakar Habasha, bayan arangama da sojojin gwamnati.

  9. Mun shirya don samun nasara kan Hamas - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a shirye yake ya samu nasara a kan Hamas a zirin Gaza.

    Da yake magana a daidai lokacin da sabon kwamandan rundunar IDF ya soma aiki, Mista Netanyahu ya ce dole ne Isra'ila ta cimma cikakken burinta.

    Janar Eyal Zamir ya ce 2025 shekarar yaƙi ce. Ya ce IDF ta samu kyawawan nasarori a fagen daga.

    "Mun samu nasarori a yaƙin Gaza da Lebanon. Hamas ta fuskanci gagarumin koma-baya amma ba a kai ga yin galaba a kan ta ba," in ji shi.

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce ƙasarsa za ta koma kai wa Hamas farmaki idan ƙungiyar ta ƙi sakin ragowar mutanen da ke tsare a hannunsu.

    Isra'ila da Amurka sun yi fatali da shawarar da Masar ta bayar game da makomar Gaza inda ta ce ta gaza magance matsalolin da ake gani a Gaza.

  10. Ban taɓa cin zarafin Sanata Natasha ba - Akpabio

    ...

    Asalin hoton, FB/Godswill Akpabio

    Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio ya musanta zargin da ɗaya daga cikin sanatoci mata ta ƙasar, Natasha Akpoti ta yi kan cewa ya taɓa yunƙurin cin zarafinta ta hanyar lalata.

    Akpabio ya bayyana hakan ne a farkon zaman majalisar na yau Laraba.

    Akpabio ya ce "ina son shaida wa duniya cewa ban taɓa cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace ba...mahaifiyata ta yi min tarbiyya mai kyau, saboda haka ina girmama mata".

    Kalaman shugaban Majalisar Dattaijan na zuwa ne bayan Sanata Natasha Akpoti ta gabatar da ƙorafinta ga majalisar game da zargin yunƙurin cin zarafi da take yi wa Akpabio.

    Batun dai ya janyo muhawara mai zafi a faɗin Najeriya, tun bayan da Sanatar ta bayyana a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Arise, cewa Akpabio ya faɗa mata wasu kalamai da ba su dace ba.

    Ƙungiyoyi da dama ne suka buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yayin da wasu kuma ke ganin cewa bai kamata a ci gaba da tattaunawa kan lamarin ba.

    A zaman majalisar na yau Laraba an tafka muhawara inda wasu sanatocin suka mike suka bayyana cewa bai kamata a saurari ƙorafin Natasha ba kasancewar ta shigar da ƙara a gaban kotu.

    Sai dai Natasha ta kare matakin nata, inda ta ce ƙarar da ta shigar a kotu ta shafi batun ɓata suna ne da wani hadimin Sanata Akpabio ya yi, yayin da ƙorafinta ga majalisar kuma ya shafi batun yunƙurin cin zarafin lalata ne da take zargin shugaban majalisar da aikatawa.

  11. An zartar da hukuncin kisa kan ba'indiyar da ake zargi da kashe jariri a Dubai

    ...

    An zartar da hukuncin kisa kan wata mata ƴar Indiya mai aikatau a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - bayan samunta da laifin kashe jariri a gidan da take aiki.

    Shahzadi Khan, wadda ta yi wa wasu ma'aurata ƴan Indiya aiki - an zartar mata da hukuncin ne a watan da ya gabata, a cewar gwamnatin Indiya.

    A cewar takardun kotu a Abu Dhabi, Khan ta kashe jaririn ne ta hanyar hana shi shakar iska, amma wani likita wanda ya ba da bahasi a kotun bai iya tabbatar da hakan ba saboda ba a ba shi damar yi wa gawar gwaji ba.

    Iyalan Khan sun ce ba ta da laifi kuma jaririn ɗan wata huɗu ya mutu ne sakamakon ba shi riga-kafin da bai kamata ba ranar da ya mutu. Sun ce Khan ba ta samu wakilcin da ya kamata ba lokacin sauraron ƙarar. BBC ta tuntuɓi hukumomin UAE domin ji daga gare su.

    An zartar da hukuncin kisan ne ranar 15 ga watan Fabrairu, amma sai ranar 3 ga watan Maris hukumomin Indiya suka tabbatar da labarin bayan da mahaifan Khan suka shigar da ƙara a wata babbar kotu a Delhi - inda suke neman bayanai kan inda ƴarsu take.

    Ɓoye batun zartar da kisan ya janyo ce-ce-ku-ce a Indiya, wadda ke da alaƙa ta kut-da-kut da UAE. Dubun-dubatar ƴan Indiya na rayuwa da kuma aiki a ƙasar.

    A cewar ƙarar da iyalan Khan suka shigar, ƴarsu ta je Dubai ne a watan Disamban 2021 domin yi wa mutanen ƴan Indiya aiki a matsayin mai reno.

    An ba ta alhakin kula da jaririn, wanda aka haifa a watan Agustan 2022. A cewar mahaifin Khan, ta riƙa kiran ƴan uwanta waɗanda ke zaune a jihar Uttar Pradesh ta waya don nuna musu jaririn.

    Ƴan sanda sun kama Khan watanni biyu bayan nan. Ta ce an tilasta mata yin bidiyon cewa ita ta kashe jaririn, kuma ba a ba ta lauya ba a karar.

    An yanke mata hukuncin kisa ne a watan Yulin 2023. An yi watsi da buƙatarta a watan Fabrairun 2024.

    Iyalan Khan sun ce lokaci na karshe da suka ji ɗuriyarta shi ne ranar 13 ga Fabrairun wannan shekara lokacin da ta kira su daga gidan yari, inda ta ce za a kashe washegari.

    "Ta yi ta kuka sannan ta ce an saka ta cikin wani ɗaki na daban, kuma ba za ta fito da rai ba sannan kiran zai kasance na karshe," Mahaifinta Shabbir Khan ya faɗa wa BBC.

  12. Ƴansandan Serbia sun kaddamar da bincike bayan hargitsi a majalisar dokokin ƙasar

    Serbia

    Asalin hoton, AFP

    Ƴansanda a Serbia sun kaddamar da bincike bayan da aka samu hargitsi a majalisar dokokin ƙasar da ke Belgrade.

    A yayin da majalisar ke zaman tabbatar da murabus ɗin Firaiminista Milos Vucevic, ƴan jam'iyyar adawa a majalisar sun saki hayaki mai saka hawaye, suka kuma jefi ƴan jam'iyya mai mulki da kwai.

    Ƴan majalisar da dama ne suka jikkata sakamakon hargitsin.

    Ƴan adawar dai na zargin gwamnatin ƙasar da cin hanci da rashawa, bayan wani gini ya rufta a tashar jirgin ƙasa ta Novi Sad a watan Nuwamban da ya gabata, inda mutane 15 suka mutu.

  13. 'Alamu sun nuna Rasha shirye take don kulla yarjejeniyar zaman lafiya'

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce alamun da ya ke gani sun tabbatar masa cewa Rasha a shirye ta ke ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Ukraine.

    Mista Trump na fadi hakan ne yayin da ya ke jawabi a zauren majalisar dokokin Amurka, karon farko tun bayan da ya koma kan karagar mulki makonni shida da suka gabata.

    Ya ce "Da safiyar yau na sami wata muhimmiyar wasiƙa daga shugaban ƙasar Ukraine Zelensky, inda ya ke cewa Ukraine ma a shirye take ta hau teburin tattaunawa da don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

    Mista Zelensky ya aike da wasikar ne bayan da Amurka ta dakatar da duk wani tallafin kayan aikin soji zuwa Ukraine.

  14. Ƴansanda sun kama wata mata bisa zargin kashe kishiyarta a Bauchi

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed kan zargin kashe kishiyar mai suna Hajara Isa hanyar shaƙeta a gidan mijinsu.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, Ahmed Wakil ya fitar ranar Talata ya ce tuni rundunarsu ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.

    Ya ce mijin matan - Sale Isa - ne ya kai ƙorafi wajen ƴansanda a ranar Talata.

    Wakil ya ce bayan fara gudanar da bincike ƴansanda suka kama matar mai suna Fatima Mohammed mai shekara 28, wadda daga baya ta amsa laifinta a lokacin ƴansanda suke tuhumarta.

    “A lokacin da ake tuhumarta ta amsa laifinta inda tace shaƙe kishiyartata ta yi, har sai da ta mutu'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ''bayan ta kashe ta, ta yi ƙoƙarin yin ɓadda-bami, ta yadda ba za a zarfgeta ba, inda ta watsa mata ruwan zafi, sanna ta ƙonata da wasu buhun da ya fara lalacewa''.

    Tuni dai aka mayar da binciken ofishin kula da manyan laifuka da ke jihar domin faɗaɗa bincike.

    A baya-bayan nan jihar Bauchi na fuskantar matsalolin kisan kai, wani da ke ƙara haifar da fargaba.

    A farkon makon nan ma an kama wani matash bisa zargin kashe mahaifiyarsa, bayan da a farkon azumi aka zargi wani miji da kashe matarsa.

  15. Shugabannin China na taron kyautata tattalin arzikin ƙasar

    Shugabannin China

    Asalin hoton, Getty Images

    Jogororin ƙasar China na gudanar da taro a birnin Beijing damin lalubo hanyoyin kyautata fata kan tattalin arzikin ƙasar yayin da take fuskantar yaƙin kasuwanci da Amurka.

    Yayin da yake jawabi a wurin buɗe taron, Firimiyan ƙasar, Li Qiang ya yi gargaɗin cewa ''sauye-sauyen da ba a taɓa gani da cikin ƙarni guda'', na haifar da karyewar tattalin arzikin duniya cikin sauri.

    Mista Li ya amince cewa cimma haɓakar tattalin arziki da kashi biyar na buƙatar ''cikakken jajircewa''.

    Manufar shirin shi ne ƙara yawan abin da ƴanƙasa ke buƙata, da rage zaman banza tsakanin matasa, da magance faɗuwar farashin gidaje da kuma maraba da masu zuba jari daga ƙetare.

  16. An samu gawar tsohon shugaban hukumar Shige da fice a cikin otal - Ƴansanda

    tsohon shugaban Immigration

    Asalin hoton, Others

    Rundunar ƴansandan birnin tarayya Abuja ta ce an samu gawar tsohon shugaban hukumar Shige da Fice ta Najeriya, David Parradang a cikin ɗakin wani otal.

    Cikin wani saƙo da kakakin rundunar ƴansandan birnin, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafinta na X, ta ce an samu gawar Parradang mace a wani ɗakin otal da ke yankin Area 3 a Abuja, cikin wani yanayi da yake buƙatar bincike.

    Ƴansandan sun ce bayanan da suka samu sun nuna cewa a ranar Talata, 3 ga watan Maris, Parradang ya kama ɗaki a otal ɗin da nufin yin kwana guda inda ya biya naira 22,000.

    ''Bayan kama ɗakin, wata mace ta ziyarce shi a ɗakin - wadda daga baya ta fice daga ɗakin bayan ƙwace wasu sa'o'i, inda shi kuma aka ame shi a mace bayan haka'', kamar Yadda SP Josephine ta wallafa a shafinta na X.

    Ta ƙara da cewa yanzu haka ƴansanda sun faɗaɗa bincike da nufin gano matar domin gano aihinin abin da ya faru har tsohon babban jami'in na shge da fice ya rasa ransa.

  17. An kashe mutum 70 a hari kan sansanin ƴangudun hijira a Sudan

    bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotonni daga Sudan na cewa Aƙalla mutum 70, ciki har da mata da ƙananan yara aka kashe a wani harin atilare kan sansanin ƴangudun hijira a jihar Darfur ta Arewa.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce dakarun RSF sun harba makamai kan wata kasuwa mai cike da jama'a a sansanin ƴangudun hijira a Abu Shouk a kusa da birnin El-Fasher da maraicen ranar Talata.

    Tuni dai aka ayyana bala'in yunwa a sansanin ƴangudun hijira na Abu Shouk da wasu sansanoni biyu a yankin.

    Fiye da mutum miliyan 12 ne aka raba da gidajensu tun bayan ɓarkewar yaƙin Sudan kusan shekara biyu da suka gabata.

  18. EFCC ta kama tsohon gwamnan Akwa Ibom bisa zargin zambar naira biliyan 700

    Tsohon gwamnan Akwai Ibom, Udom Emmanuel

    Asalin hoton, Udom Emmanuel/X

    Jami'an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, sun kama tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel bisa zargin almundanar naira biliyan 700.

    An kama Mista Emmanuel bayan ya amsa gayyatar hukumar a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da cin hanci ta yi masa.

    Ƙungiyar ta zargi tsohon gwamnan ta karɓar naira tiriliyan uku daga asusun gwamnatin tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan kuɗin wasu ayyuka na naira biliyan 300 bayan ya sauka.

    Haka kuma ƙungiyar ta zargi Mista Emmanuel da kasa yin bayani kan yadda aka kashe wasu maƙudan kuɗi har naira biliyan 700, kamar yadda gidan talbijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

    Emmanuel ya kasance gwamnan jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya daga 2015 zuwa 2023, ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ma da hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji da wasu mutum huɗu a gaban kotu, bisa zargin ɓarnatar da kusan naira biliyan 47.

  19. Shugabannin ƙasashen Musulmi na neman goyon bayan sake gina Gaza

    arab

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen Larabawa na neman goyon bayan ƙasashen duniya kan shirinsu na sake gina Gaza wanda zai bai wa mazauna yankin miliyan biyu damar ci gaba da zama a yankin.

    Da yake jawabi a birnin Alkahira, shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce za a tattauna batun a wani babban taron ƙasashen musulmi da za a yi a Saudiyya ranar Juma'a.

    Ya ce “Masar ta kuma yi aiki tare da ƴan'uwanmu Falasɗinwa wajen kafa kwamitin gudanarwa na kwararru masu zaman kansu, waɗanda za a bai wa amanar tafiyar da zirin Gaza bi sa ƙwarewar mambobinsa.

    Hamas dai ta yi maraba da ƙudurin kafa wannan kwamitin amma Fadar White House da Isra'ila sun yi watsi da ƙudirin, suna masu cewa ba a yi la'akari da asalin yadda abubuwa suke a ƙasa a Gaza ba.

  20. Rasha ta shirya kawo ƙarshen yaƙin Ukraine - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce alamun da ya ke gani sun tabbatar masa cewa Rasha a shirye ta ke ta ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da Ukraine.

    Yayin da yake jawabi a zauren Majalisar Dokokin Amurka - karon farko tun bayan da ya koma kan karagar mulki makonni shida da suka gabata Mista Trump ya ce ta samu wata muhimmiyar wasiƙa daga shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky.

    A Cikin wasiƙar Shugaba Zelensky ya ce Ukraine a shirye take domin hawa teburin tattaunawa don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

    Mista Zelensky ya aike da wasikar ne bayan da Amurka ta dakatar da duk wani tallafin kayan aikin soji zuwa Ukraine.