Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad, Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Masu zanga-zanga a Kenya sun yi barazanar tsige shugaban ƙasar

    A yau, Alhamis, matasan Kenya suka ci gaba da zanga-zangar da suka fara ta ƙin jinin gwamnati, wadda ta faro sanadiyyar ƙin yarda da ƙarin haraji, wadda ta rikiɗe zuwa buƙatar shugaban ƙasar William Ruto ya yi murabus daga muƙaminsa.

    Masu shirya zanga-zangar sun yi barazanar yin tattaki har zuwa fadar shugaban ƙasar da nufin "tsige Shugaba William Ruto," a cewar wani rahoto da gidan talabijin na Citizen TV mai zaman kansa ya fitar.

    Ɗaya daga cikin manyan masu jagorantar zanga-zangar, Kasmuel McOure, ya bayyana zanga-zangar ta yau a matsayin "mafi girman zanga-zanga a cikin duk zanga-zangar da aka yi a 'yan kwanakin nan," a wata hira da Citizen TV.

    Matasan sun shafe wata uku suna gudanar da zanga-zangar da tuni ta tilasta wa gwamnati janye ƙudirin ƙarin harajin da kuma rusa majalisar ministocin ƙasar.

    Jaridar Capital News ta ba da rahoton gagarumin gangami a shafukan sada zumunta, tare da yin kiraye-kiraye a mamaye cibiyoyin gwamnati don nuna adawa da "mummunan shugabanci.

    A martanin da ya mayar, Shugaba Ruto ya yi gargaɗi game da tashe-tashen hankali, yana mai jaddada ƙudurin ƙasar na samar da zaman lafiya.

    Zanga-zangar ta yau ta zo daidai da rantsar da sabuwar majalisar ministocin Shugaba Ruto, wadda ta ƙunshi 'yan siyasa hudu na adawa.

    Sai dai masu zanga-zangar sun ƙi amincewa da sabuwar majalisar ministocin, saboda shigar da tsofaffin ministocin da ake zargi da "rashin ƙwarewa da rayuwa ta wadaƙa."

    haka kuma akwai wani ƙudurin doka da ke gaban majalisar dokokin ƙasar, wanda idan an zartar da shi, zai dora alhakin duk wata ɓarna a lokacin zanga-zanga kan masu shiryata.

  2. Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana fita

    Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita da ta sanya sakamakon tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar matsin rayuwa, inda yanzu jama'a za su iya fita daga karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma.

    A sanarwar da kwamishinan kula da harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce bayan nazarin yanayi da majalisar tsaro ta jihar ta yi a yanzu ta rage lokacin dokar ta sa'a 24, wadda aka sanya ranar Litinin 4 ga watan Agusta, 2024.

    Da wannan sassauci sanarwar ta ce daga yanzu jama'a za su ci gaba da kasancewa a gida daga karfe 6 na yamma har sai karfe takwas na safe sannan su fito su ci gaba da gudanar da harkokinsu.

    Kwamishinan ya jadda cewa jami'an tsaro za su ci gaba da tabbatar da ganin jama'a sun kiyaye tare da bin umarnin da aka bayar na bin dokar, da tabbatar da tsaro.

  3. Jami'an tsaron Najeriya sun yi wa hedikwatar ƙungiyar ƙwadago ta NLC dirar-mikiya

    Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce gungun jami'an tsaro dauke da tarin makamai ya yi wa hedikwatarta da ke Abuja, dirar-mikiya.

    Kungiyar ta ce jami'an sun isa ginin hedikwatar tata ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30

    A sanarwar da shugaban sashen hulda da jama'a na kungiyar Benson Upah ya fitar ya ce jami'an sun karya kofar dakin da ke zaman ma'ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suke debe daruruwan littattafai da wanu takardu

    Sanarwar ta ce, jami'an sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.

    Kungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami'an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami'an daga hedikwatar tata.

    Kungiyar ta bayyana yau a matsayin wata bakar rana a dumukuradiyyar Najeriya, inda ta ce ko da a lokacin bakin mulkin sojoji ba a taba yi wa hedikwatarta abin da aka yi mata a wannan lokacin ba na kutse.

  4. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Alhamis.

    Ni Muhammad Annur Muhammad da Aisha Babangida za mu kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba. A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Duk abin da ya samu moɗa a tambayi randa