Me ya jawo tarzomar da ke faruwa a Birtaniya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Rikici ya barke a wasu sassan ƙasar Birtaniya tun daga makon da ya gabata bayan wani harin wuka da aka kai a arewa maso yammacin Ingila, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu 'yan mata uku.

A garin Southport da ke gabar teku, inda al'ummar yankin ke zaman makokin waɗanda suka mutu, ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi sun yi amfani da damar wajen tallata ra'ayoyinsu tare da tsoratar da al'ummomin da ba fararen fata ba.

Tun farko dai ana zaman lafiya a garin amma daga bisani aka fara samun tashin hankali da ɓarna, inda aka ga masu tayar da tarzoma suna jifan 'yansanda da duwatsu da ƙananan bamabamai, tare da kai wa masu neman mafaka hari a otal.

Rikicin ya bazu zuwa wasu sassan Birtaniya, ciki har da Hull da Liverpool da Manchester da Blackpool da kuma Belfast.

Dalilin haka ne ya sa ƙasashen Indiya da Najeriya da Malesiya suka gargaɗi ƴan ƙasarsu kan yin balaguro zuwa Birtaniya.

Firaminista Keir Starmer ya yi tir da rikicin.

Da yake magana da manema labarai a Fadar Downing Street ya ce, "Babu hujjar daukar irin wannan matakin na tayar da rikici."

Wani bincike da BBC Verify ta yi ya nuna cewa ba duk mutanen da ke kan tituna ba ne ko masu wallafa abubuwa game da hare-haren Southport ke da tsattsauran ra'ayi kan rikicin ko kuma ke goyon bayan tarzomar, ko suke da alaka da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin.

Har wa yau, tarzomar ta jawo hankalin mutanen da ke nuna damuwa game da munanan laifuka ta hanyar rashin fahimtar juna da ke nuna cewa harin na da alaƙa da shige da fice ba bisa ka'ida ba.

Labaran ƙarya

Lokacin da aka samu labarin harin da aka kai da wuƙa, labaran ƙarya kan wanda ya kai harin sun fara yaɗuwa a shafukan sada zumunta.

Ƴansanda sun tabbatar da cewa wani matashi ɗan shekara 17 ne ya kai harin kuma suka yi kira ga jama'a da su daina yaɗa labaran ƙarya.

Sai dai kuma, masu tsattsauran ra'ayi da dama sun yi ikirarin cewa maharin Musulmi ne mai neman mafaka da ya shiga ƙasar ta jirgin ruwa.

BBC verify ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin masu tsatsauran ra'ayin mai suna Stephen Yaxley-Lennon na da mabiya da dama a shafin sada zumunta na X kuma yana da alaƙa da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi na English Defence League.

Ikirarin karya game da maharin ya fara yaɗuwa cikin sauri a shafukan sada zumunta, inda ya kai ga dimbin jama'a, ciki har da talakawa da yawa waɗanda ba su da alaka da kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi, a cewar BBC Verify.

Joe Mulhall, shugaban bincike a kungiyar masu yaki da tsattsauran ra'ayi mai suna Hope Not Hate, ya bayyana cewa babu wani karfi ko wani abu daya da ke haddasa irin wadannan ayyukan.

Nuna bambancin wariyar launin fata da kwararar baƙi

Babban zaɓen Birtaniya da aka yi a farkon watan Yuli ya janyo muhawara kan kwararar baƙi da shigowar ƴancirani ta kananan kwale-kwale. Nigel Farage, jigo a yakin neman fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai (Brexit), wanda ya koma siyasa a matsayin jagoran jam'iyar Reform UK, ya yi kira da a dakatar da "kwararar baƙi marasa mahimmanci".

A martaninsa kan tarzomar, ya yi iƙirarin cewa: "Mafi yawan jama'armu na iya ganin wargajewar al'ummominmu sakamakon yawan baƙin da ke shiga ƙasar."

Wannan ya nuna cewa akwai damuwa a Birtaniya kan yawam kwararar baƙi da baƙin haure.

Wani binciken Ipsos da aka gudanar a watan Fabrairu ya gano cewa kashi 52 na mutanen ƙasar na da yaƙinin cewa yawan baƙin da ke shiga ƙasar a yanzu sun yi yawa, amma kuma a shekaru biyu da suka gabata, kashi 42 ne kaɗai suka yarda da hakan.

Sauran ƙungiyoyi, ciki har da Patriotic Alternative ta masu tsattsauran ra'ayi waɗanda suka shirya zanga-zangar adawa da ƴancirani, sun ta'azzara tarukan da ke haifar da fushin jama'a game da hare-haren Southport da ya haddasa rikici.

Wasu karin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi sun yi kira da a kori ƴancirani da bakin haure daga ƙasashensu.

Hare-haren masu wariyar launin fata sun kai har a masallatai a sassan Ingila, lamarin da ya sa aka ƙara yawan 'yansanda a wasu yankunan.

Otal din da ke dauke da masu neman mafaka sun kuma zama wuraren da ake kai hare-hare na nuna wariyar launin fata da na bakin haure.

A garin Aldershot, danjaridar BBC Paddy O'Connell ya shaida wasu masu zanga-zanga a wajen wani otal da ke da masu neman mafaka, inda ya yi magana da wasu 'yan'uwa mata biyu daga Afganistan masu neman mafaka kuma suka faɗa masa cewa:

“Masu tayar da tarzomar sun zo kwatsam sun ajiye motocinsu, sai suka yi kokarin kutsawa cikin otal din inda suka fasa tagogi. Yanayin mai ban tsoro ne kwarai da gaske,” in ji matashiyar mai shekara 22.

Yar’uwarta mai shekara 17 ta ƙara da cewa: “Suna ta yin zage-zage, da yin bidiyo, tare da nuna halaye marasa kyau.”

Wawason kaya

Masu zanga-zanga da dama sun yi amfani da damar zanga-zangar wajen aikata laifuka da suka haɗa da sata da wawason kayayyaki daga manyan shaguna.

A Sunderland da ke arewa maso gabashin Ingila, masu zanga-zanga sun fasa wani gidan burodi na Greggs Bakery da kuma wani banki a NatWest, yayin da kuma aka samu rahotannin wawason kaya a wani babban shago a Blackpool da ke arewa maso yamma, wanda tuni ƴansanda suka fara gudanar da bincike.

A Hull kuma da ke arewa maso gabas, wakilin BBC ya shaida yadda aka yi wawason kaya a shaguna da dama da suka lalace, da kuma wani da ya kama da wuta, da yadda aka ƙona kayayyaki a tituna wanda ya kai ga rufe shaguna da ke tsakiyar gari, da kuma dakatar da motocin sufuri na jama'a.

Majalisar Sunderland ta fada a shafin sada zumunta ta X cewa: "Sunderland waje ne da aka sani da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙarɓar baƙi hannu biyu-biyu, abubuwan rikicin da ke faruwa a yanzu ba shi ne ainihin halin garin da mutanensa ba.

'Za mu haɗa kai da gwiwa yadda muka saba domin dawo da kwanciyar hankali ga al'ummarmu" in ji magajin garin.

Mohammed Idris, wani mai shago ne a kudancin Belfast, kuma ya ce ba zai sake buɗe shagonsa ba bayan an farfasa shi a lokacin zanga-zangar da aka yi ranar Asabar.

Idris ya faɗa wa BBC cewa dama an taba kai wa shagonsa da ke garin Sandy Row hari a shekarar da ta gabata.

Dakatar da ayyukan walwalar al'umma

Wasu ƙungiyoyin sun kuma zargi matsalolin matse bakin aljihu na gwamnati da aka daɗe ana yi game da ayyukan raya al'umma.

Bayan fara boren a Southport, ƙungiyar Hope Not Hate ta ce "an raba kan al'ummomi tsawon shekaru saboda rage kashe kuɗi da kuma yin watsi da ɓangaren" da gwamnatocin baya suka yi.

"Abu ne mai muhimmanci sabuwar gwamnati ta ɓullo da sababbin tsare-tsare da za su inganta rayuwar al'ummai, da kuma tsara yadda su ɓullo wa lamurra irin waɗannan," a cewarta.

A shekarun matsin tattalin arziki na Birtaniya daga 2010 zuwa 2019, tsohon sakataren kuɗi George Osborne da waɗanda suka gaje shi sun rage sama da fan biliyan 30 na kuɗaɗen daɗaɗa wa al'umma, da tallafin muhalli, da na walwala.

Ƙwararru sun yi gargaɗi cewa matsin rayuwa kan sa matasa faɗawa cikin tsaurin ra'ayi. Tasirin annobar korona ma da har yanzu ake jin sa zai iya ta'azzara wannan lamari.