Rufewa
Masu bin mu, a nan za mu gintse shafin namu na kai-tsaye a yau.
Sai kuma gobe idan mai duka ya kai mu.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye
Daga Muhammad Annur Muhammad, Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin mu, a nan za mu gintse shafin namu na kai-tsaye a yau.
Sai kuma gobe idan mai duka ya kai mu.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Hukumar yaƙi da yaɗuwar cututtuka ta Afirka ta ce nan ba da jimawa ba, za ta ayyana cutar ƙyandar biri da ta ɓarke a nahiyar, a matsayin wata matsala da ke buƙatar kulawar gaggawa.
Daraktan hukumar ya ce ya kaɗu da yadda aka samu ƙaruwar mutanen da ke ɗauke da cutar da kashi 160 cikin 100 a shekarar da ta gabata.
Wani nau'in cutar na yaɗuwa sosai a jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo inda cutar ta fi ƙamari.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da rahoton bazuwar cutar a sassan Afirka a wannan shekarar.
Ƙasashe 16 ciki har da Rwanda da Burundi da Uganda da Kenya duk sun sanar da ɓarkewar cutar.
Mutum biyar sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a yankin ƙaramar hukumar Taura ta jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Alhamis, lokacin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji 20 ya kife yayin da yake ƙoƙarin tsallake kogin Gamoda a kusa da ƙauyen Nahuce.
Kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Lawan Shiisu ya tabbatar wa da BBC Faruwar lamarin, inda ya ce jami'an 'yansadan da masu nutso da ƙwararrun ninƙaya na kan ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin da ba a gani ba.
''Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kuma kawo yanzu an ciro gawarwakin mutum biyar daga ciki, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman sauran fasinjojin kwale-kwalen 15'', in ji DSP Shiisu.
Lamarin dai na zuwa ne watanni bayan wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya janyo asarar rayuka a yankin ƙaramar hukumar Tauran.
An rantsar da Muhammad Yunus a matsayin shugaban riƙon ƙwaryar Bangladesh, kwanaki uku bayan hamɓarar da gwamnatin Sheikh Hasina sakamakon makonnin tarzoma.
A bikin rantsarwar da aka yi a Dhaka, Mista Yunus wanda ya taɓa samun lambar yabo ta Nobel, yake kuma samun goyon bayan sojoji da ƙungiyoyin ɗalibai da suka yi zanga-zanga, ya ce zai kare kundin tsarin mulkin ƙasar.
Tun farko ya ce abin da zai sa a gaba shi ne maido da doka da oda.
Bangladesh ta fuskanci makonnin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati inda aka kashe daruruwan mutane a arangama da jami'an tsaro.
Ƴansandan Kenya sun harba hayaƙi mai sa ƙwalla domin tarwatsa masu zanga-zangar neman inganta tsarin mulkin ƙasar, yayin da shugaban ƙasar ya rantsar da sabbin ministocinsa.
Mutane da dama har da ƴan jarida ne suka jikkata a arangamar da aka yi tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga a Nairobi, babban birnin ƙasar.
Kasuwanni sun kasance a rufe sannan harkokin sufuri suka fusknaci tsaiko, yayin da 'yansanda suka rufe manyan titunan birnin domin hana masu zanga-zangar isa tsakiyar birnin.
Ƙungiyar ƴan jarida ta gabashin Afirka ta yi tir da yadda ake muzgunawa ƴan jarida.
Masu zanga-zangar da suka fara don nuna adawa da matakin ƙarin kuɗin haraji, a yanzu na son shugaba Ruto ya yi murabus.
Zanga-zangar wadda matasa suka jagoranta ta tilasta wa shugaban ƙasar janye matakin tare da rusa majalisar ministocinsa.
A yanzu shugaba Ruto ya naɗa 'yan hamayya manyan ministoci, ciki har da ministan kuɗi da na makamashi, a wani mataki na yayyafa wa rikicin ruwa.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta lalata wani sansani da take zargin mayaƙan Boko Haram na ƙera abubuwan fashewa a tsaunukan Mandara da ke jihar Borno.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce, sakamakon yadda a baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram ke amfani da abubuwan fashewa wajen kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba, musamman a jihar Borno, ya sa jami'anta suka tsananta bincike domin gano inda mayaƙan ƙungiyar ke ƙera abubuwan fashewar.
Sanarwar ta ce wasu bayanan sirri da sojojin suka samu sun bayyana mata cewa akwai wata masana'anta da ake ƙera abubuwan fashewar da kuma adana su a tsaunin Mandara.
Sojojin saman na Najeriya sun ce bayanan sun tabbatar mata cewa an sauya wa masana'antar matsuguni daga Gwoza zuwa Timbuktu a dajin Sambisa kafin dagabisani a mayar da shi yankin Grazah da ke tsaunin Mandara.
''Sakamakon tsananta hare-hare kan mayaƙan da sojoji ke yi a baya-bayan nan ya sa aka mayar da ɗauke masana'antar daga dajin Sambisa zuwa tsaunukan na Mandara'', in ji sanarwar sojojin.
Sojojin sun ce sun shafe tsawon makonni suna sanya ido kan wurin ƙera abubuwan fashewar da sauran ayyukan mayaƙan a yankin.
''A lokacin da muka ƙaddamar da harin, mun hangi wasu manyan motocin dakon makamai guda biyu a kusa da masana'antar, tsaye ƙarƙashin bishiya'', in ji sanarwar.
''Hakan ne ya sa ba mu yi wata-wata ba muka ƙaddamar da hare-hare a yankin, da nufin lalata masana'antar tare da kashe mayaƙan ƙungiyar''.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sojojin sun samu nasarar lalata masana'antar.
Hotunan bayan harin sun nuna yadda wurin ya turnuƙe ta hayaƙi, bayan da masana'antar ta ƙone tare da motocin dakon makaman guda biyu.
'Yar takarar sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu ta janye daga takarar saboda ce-ce-ku-ce kan asalinta.
Chidimma Adetshina ta bayyana a shafinta na Instagram cewa ba za ta shiga matakin ƙarshe na gasar da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa ba.
Hakan na zuwa ne bayan zargin da ma'aikatar cikin gida ta ƙasar ta yi cewa mahaifyarta ta tafka almundahana a lokacin da take ƙoƙarin samun takardun izinin zaman Afirka Kudu.
Ms Adetshina na fuskantar bincike kan asalin ƙasarta.
Mai shekara 23 - wadda ɗalibar koyon aikin lauya ce - ta bayyana cewa mahaifinta ɗan asalin Najeriya ne yayin da mahaifiyarta 'yar Afirka ta Kudu ce asalin Mozambique.
Fafatawar da ake yi a yanzkin Kursk na Rasha ta shiga kwana na uku, yayain da dakarun ƙasar ke "yunƙurin" fitar da sojojin Ukraine da suka kutsa ƙasar, kamar yadda ma'aikatar tsaron ƙasar ta bayyana.
Rasha ta ce aƙalla sojojin Ukraien 1,000 ne suka kusat ƙasar cikin manyan tankunan yaƙi da motocin sulke a ranar Talata.
Aƙalla mazauna yankin 3,000 aka kwashe daga yankin, yayain da gumurzu soji ya kashe fararen hula huɗu, kamar yadda mataimakin gwamnan yankin, Andrei Belostotsky ya yi ƙarin haske.
Kawo yanzu rundunar sojin Ukraine ba ta ce komai ba kai-tsaye game da batun, to amma shugaban ƙasar, Volodymyr Zelensky, wanda bai yi magana kai tsaye game da lamarin ba, ya ce ''kowa zai ga yadda sojojin Ukraine za su bayar da mamaki wajen cin nasara''.
To sai dai Mykhailo Podolyak, wanda ya jima a matsayin hadimin Shugaba Zelensky, ya wallafa a shafinsa na X cewa: "Yaƙi duk yaƙi ne, ta hanyar amfani da ƙa'idojinsa, duk wanda ya takali wani shi zai ɗanɗana kuɗarsa."
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta musanta kai samame ofishin hedikwatar ƙungiyar ƙwadago ta NLC.
A ranar Laraba da daddare ne dai wasu jami'an tsaro ɗauke da manyan makamai suka kai samame ofishin ƙungiyar, tare da yin waon gaba da wasu takardu.
Ƙungiyar ta NLC ta zargi jami'an tsaron farin kaya na DSS ta ƙaddamnar da samamen.
Kungiyar ta ce jami'an sun isa ginin hedikwatar tata ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30
To sai dai cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukanta na sada zumunta ta musanta zargin
''Muna a fahimci cewa jami'an DSS ba su kai kowane irin samame kan ofishin NLC da ke Abuja ba'', in ji sanarwar.
Tun da farko cikin wata sanarwa da kakakin NLCn, Benson Upah ya fitar, ya ce jami'an da suka kai samamen sun ƙarya kofar ɗakin ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suka ɗebe ɗaruruwan littattafai da wanu takardu.
Sanarwar ta ce, jami'an sun yi iƙirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.
Ƙungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami'an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami'an daga hedikwatar tata.
Ƴansanda a Catalonia sun dakatar da aikin rufe manyan tituna yayin da suke neman jagoran ƴan aware wanda ya koma Spaniya bayan shekara bakwai yana gudun hijira.
Mista Puidgemont na fuskantar sammacin kama shi da ke da alaƙa da yunƙurin da ya yi na samar wa yankin Catalonia ƴancin kai a 2017.
Da safiyar yau ya yi ɓatan-dabo bayan yi wa magoya bayansa jawabi kusa da majalisar dokokin Catalonia.
Mista Puidgemont ya ce a yau mutane da dama za su yi murna da cewa za a kama ni, cewa ƙarya dokar da suka amince da ita a majalisarsu za ta sa mu ɗanɗana kuɗarmu amma sun yi kuskure.
An kama wani ɗan sanda kan zargin ya taimaka wa jagoran ƴan awaren wajen tserewa.
Majalisar dokokin Spaniya ta amince a yi wa jagororin ƴan aware afuwa sai dai kotun ƙolin ƙasar ta ce afuwar ba ta shafi tuhumar almubazzaranci da mista Puigdemont da sauran mutanen ke fuskanta ba.
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta fara gudanar da bincike kan sanadin mutuwar, wani mutum da aka ga gawarsa, sanye da kayan mata a Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce, a yau Alhamis ne 8 ga watan Agusta, 2024, da misalin 07:40 na safe, aka sanar da rundunar ta waya cewa an ga wata mata da ba a sani ba kwance ba ta motsi a titin Katampe - Mabushi, inda nan da nan aka tura ƙwararrun masu bincike zuwa wajen.
Sanarwar ta ce, binciken farko-farko ya nuna cewa namiji ne sanye da kayan mata, kuma babu wata alama da za ta nuna ko wane ne shi.
Ta kara da cewa daga nan ne aka tafi da shi asibitin Gundumar Maitama (Maitama District Hospital), inda likitoci suka tabbatar ya rasu.
Sanarwar ta ce, nan da nan kwamishinan 'yansandan Abuja, CP Benneth C. Igweh, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan sanadin mutuwar mutumin.
Ƙungiyar kare hakkin bil'Adama ta Musulunci, a Najeriya, (MURIC) ta buƙaci a gudanar da addu'o'i a masallatai da coci-coci a ƙasar kan abubuwan da ta kira da munanan alamu a harkokin siyasar Najeriya.
Babban Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya gabatar da buƙatar a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.
Ƙungiyar ta nuna cewa yin adduo’i a masallatai da majami'u bukata ce da ta zama dole bisa la’akari da yadda baƙin al’amuran ke neman zama barazana ga makomar kasar baki ɗaya.
Saboda haka MURIC ta yi kira ga dukkan limaman Musulmi da su jagoranci mabiya a masallatansu a gobe Juma’a 9 ga watan Agusta, su yi addu'o'in, kamar yadda su ma limaman Kiristoci, su jagoranci mabiyansu wajen yin addu'ar a ranar Lahadi mai zuwa, 11 ga Agustan.
Farfesa Akintola ya ce waɗannan abubuwa na tashin hankali da suka lullube matasa a duniya, munanan alamomi ne da suke matuƙar buƙatar yi wa Najeriya addu'o’i.
Shugaban ya kuma ce su ma masu mulki akwai buƙatar yi musu addu'a ta samun kariya da kuma sanya tausayin talakawa wajen gudanar da mulkinsu.
Ƙungiyar ta MURIC, ta yi kiran ne sakamakon zanga-zangar lumana da ta rikiɗe ta zama tarzoma -ta kashe-kashe da lalata dukiyar al’umma wanda ta ce, ƙasar na cikin mawuyacin hali.
Baya ga wahalhalun da ke tattare da durƙushewar tattalin arziƙi, zanga-zangar matsin rayuwa na ci gaba da fito da wasu al’amura marasa daɗi, ga ƙasar in ji ƙungiyar ta MURIC.
Sanarwar ta kara da cewa hatta masu shirya zanga-zangar ba su yi tsammanin irin wannan mummunan lamari zai faru ba.
Wata sabuwar ƙungiyar 'yan tawaye, mai suna, Mouvement Patriotique du Niger, MPN, ta ɓulla a yankin arewacin Jamhuriyar Nijar.
Ƙungiyar tawayen ta Tubawa ta zama ta huɗu ke nan daga cikin jerin kungiyoyin tawaye masu faɗa da makamai da suka bayyana a ƙasar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Waɗannan ƙungiyoyi na tawaye da suka bayyana daga yankin Agadez, da ke arewacin ƙasar na fafutuka ne don ganin an saki Mohamed Bazoum, wanda sojoji suka hamɓarar daga kan mulki, tare da mayar da ƙasar kan mulkin dumukuraɗiyya.
Wasu kungiyoyin ƙasar ta Nijar na ganin daukar makami ba mafita ba ce ga matsalolin siyasa kasar.
A watan Agusta na 2023, wani tsohon jagoran 'yan tawaye kuma ɗan siyasa a ƙasar ta Nijar ya ce ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.
Rhissa Ag Boula ya ce ƙungiyar tasa mai suna Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya (Conseil de la Résistance Pour la République) za ta tallafa wa ƙoƙarin mayar da gwamnati mai aiki da tsarin mulki a Nijar.
Yanzu dai bayanai na nuna cewa shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahmane Tchiani, a kwanakin nan yana ta ganawa da shugabannin ƙabilun yankin arewacin ƙasar da suka ɗauki makamai domin shawo kan matsalar, ta yadda za a sama wa ƙasar mafita - ta a gudu tare a tsira tare.
Wata kungiyar agaji ta Yahudawa ta ce rahotanni kan ƙyamar Yahudawa a Biritaniya a wata shida na farkon wannan shekara ya yi karuwar da ba a taɓa gani ba.
Ƙungiyar, (Community Security Trust (CST)) ta ce daga watan Janairu zuwan watan Yuni na wannan shekara ta 2024, ta samu rahoto 1,978 na ƙyamar Yahudawa, ƙari kan 964 da ta samu a wata shida na farko na 2023.
CST ta ce, a faɗin Birtaniya ta samu rahotanni 121 na kai hari a wata shida na farko na shekarar nan, kari a kan kashi 41 cikin ɗari a cikin watan shida na farko na shekarar da ta wuce.
Ƙungiyar ta kuma ce hare-hare kan kadarorin Yahudawa sun ninka tun daga watan Janairu, inda ta bayyana hakan da abin takaici.
Ta ce rahotanni 1,037 na ƙyamar Yahudawan sun kasance ne a yankin Greater London sai kuma yankin Manchester (Greater Manchester), wanda ya kasance na biyu da rahotanni 268, yayin da yankin West Yorkshire ya kasance na uku da rahotanni 115.
An dai samu wannan ƙaruwa ne tun bayanharin da Hamas ta kai Isra'ila a watan Oktoba, da kuma yaƙin da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza, bayan harin na Hamas.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba shi da ƙwarin gwiwar cewa za a samu sauyin shugabanci cikin lumana idan har Donald Trump ya faɗi zaɓen shugaban ƙasar na watan Nuwamba.
A hirarsa ta farko tun bayan da ya janye daga takarar, Mista Biden ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS cewa bai kamata a manta barazanar da ɗan takarar Republican ɗin ya yi ba cewa sai an zubar da jini .
Mita Biden ya ce da gaske yake abin da ya fada, kada mu dauka wasa ne.
Shugaban ya kuma ce tsohon shugaban ƙasar, Donald Trump na jam'iyyar hamayya ta Republican zai iya yin koken cewa an yi masa fashi a zaɓen kamar yadda ya yi a 2020.
Yayin da ya rage ƙasa da wata uku a gudanar da zaɓen na Amurka, Donald Trump da Kamala Harris, 'yar takarar zaɓen ta jam'iyyar Democrat na ƙara zage damtse a yaƙin neman zaɓensu a jihohin da ke zama raba-gardama a zaɓen shugaban na Amurka.
Shugaban Tunisia Qais Saied ya tuɓe firaministansa Ahmed Hachani tare da maye gurbinsa da Kamel Madouri.
Babu wani dalili da aka bayyana na tuɓe, Hachani, wanda aka naɗa a watan Agusta, bayan tuɓe Najla Bouden wadda ita ma aka tuɓe ba tare da bayyana dalilin tuɓe ta ba a hukumance.
A 2019 aka zaɓi Shugaba Saied kuma tun lokacin yake ci gaba da ƙarfafa ikonsa.
A 2022 ƙasar ta koma tsarin shugaban ƙasa mai cikakken iko bayan sake kundin tsarin mulkinta wanda ya rage wa majalisar dokokin Tunisia ƙarfi.
Shugaban na Tunisia na neman ta-zarce a zaɓen kasar na watan Oktoba, duk da sukar ƴan hamayya a tsarin tafiyarsa da mulkinsa da suka kira na kama-karya.
An gano gawarwakin wasu ƴan ci-rani ƴan Senegal, su 14 a cikin wani ɗan karamin jirgin ruwa na leda da ake hura wa iska, a jamhuriyar Dominikan.
Shafin jaridar Press Afrik, ya ruwaito cewa, labarin ya bayyana ne bayan da ƙungiyar Horizon Sans Frontieres (Horizon Without Borders), mai kare haƙƙin ƴan gudun hijira da ƴan ci-rani ta gane gawarwakin mutum biyu daga ciki.
Ko a watan da ya wuce na Yuli, an gano gawarwakin mutum aƙalla 89, yawanci ƴan Senegal da Gambiya a gaɓar tekun Mauritaniya, bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mutum 170 ya kife a tekun Atalantika.
Dubban mutane da ke tsere wa yaƙi da fatara da talauci da tashe-tashen hankali a ƙasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara na ƙoƙarin shiga Sifaniya ta hanyar tekun Atalantika a duk shekara, inda da dama ke mutuwa a hanya.
Senegal ta kasance wata hanya ta masu neman shiga Turai inda suke bi ta teku da jirgin sama daga ƙasashen na Afirka.
Kungiyar kare haƙƙin bil’Adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadarai da samamen da jami’an tsaro suka kai hedikwatar ƙungiyar kwadago ta Najeriya, ta NLC.
Kungiyar ta ce samamen da aka kai jiya Laraba da daddare ya yi kama da wata mummunar manufa ta hantarar ƙungiyar ƙwadagon.
A cewar Amnesty International, samamen da jami'an tsaron suka kai ya tauye ƴanci da damar ma'aikata na gudanar da zanga-zanga.
A yayin samamen, jami’an tsaron sun yi awon gaba da littattafai na kungiyar NLC, tare da kwace kayayyakin da suka ce an yi amfani da su wajen tada zaune tsaye da kuma shirya zanga-zangar baya-bayan nan.
Ƙungiyar ta Amnesty ta bayyana matukar damuwarta game da tsaron jami’an NLC.
Sannan ta jaddada cewa a karkashin dokokin kare hakkin bil’Adama na ƙasashen duniya, ba a harin ƙungiyoyin ƙwadago saboda gudanar da ayyukansu.
An ɗaure wani fitaccen ƙwararren masanin kada, ɗan Birtaniya shekara goma da wata biyar a Australia, bayan da ya amince da tuhumar da aka yi masa ta yin jima'i da karnuka.
A shari'ar wadda ta tayar wa da jama'a da dama hankali, an samu Adam Britton, mai shekara 56 kwararre kan dabbobi, wanda ya yi aiki da BBC da kuma tashar nuna fim ɗin dabbobi ta National Geographic, ya amsa laifinsa na lalata da dabbobi da kuma azabtar da su.
Haka kuma Mista Britton ya amince da tuhumar da aka yi masa ta mallakar wasu hotuna da bidiyo na muzgunawa da ci da gumin yara.
Kotun ƙolin Australiya, (Northern Territory (NT) Supreme Court), ta saurari ƙarar da aka shigar gabanta cewa mutumin ya ɗauki hoton kansa a lokacin da yake azabtar da dabbobin, har kusan dukkaninsu suka mutu, sannan ya sanya hoton bidiyon da wani suna na daban ba nasa ba.
Britton ya yi shekaru yana yin wannan abu ba tare da an gano ba, har sai da asirinsa ya tonu a wasu hotunan bidiyo.
An kama shi ne a watan Afirilu na 2022, bayan da aka gudanar da bincike a gidansa a Darwin, inda daga nan aka kuma gano wasu hotunan bidiyo na cin zarafin yara.
Alkalin kotun da ya yanke masa hukunci, Chief Justice Michael Grant, ya ce bayanin miyagun laifukan da Britton ya aikata abu ne da zai iya tayar da hankali sosai, wanda ba za a iya nunawa jama'a hotunan ba.
Yayin da ake karanta laifukansa a kotun wasu mutanen da ke wajen sun rika kuka, suna la'antar Britton, wasu kuma sun ma fice daga cikin kotun ne domin ba za su iya ma saurare ba.
Babban daraktan kula da kare haƙƙin jama'a na jamhuriyar Nijar ya bayar da rahoton cewa, ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ta kashe aƙalla mutum 77 a fadin kasar cikin makonnin da suka gabata, kamar yadda amfanin dillancin labaran kasar ANP ya ruwaito
Mutum 85 ne kuma suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwan.
Ambaliyar ta kuma raba kusan mutane 75,711 da muhallansu, tare da lalata gidaje 9,703, sannan ta tafi da dubban shanu da tan na kayan abinci.
Yankunan da lamarin ya fi kamari sun hada da Maradi, inda aka samu rahoton mutuwar mutum 25, sai Zinder inda mutum 18 ne suka mutu, sai Tahoua, gurin das mutum 15 suka mutu.
Sauran yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Agadez da Dosso da Niamey da kuma Diffa.
Damina a Nijar dai ta yi kaurin suna wajen haddasa mummunar ambaliya.
A watan Satumban 2023, irin wannan ambaliyar ruwan ta yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 50 a faɗin kasar