Mali na binciken zargin sojojinta da kashe fararen hula 24

Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin ƙasa na Mali ta ƙaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa jami'anta na kashe fararen hula aƙalla 24 a arewan ƙasar a ranar Litinin.
Zargin ya fito ne daga ƙungiyar ƴantawayen Azawad Liberation Front da ke rigima da gwamnatin ƙasar, inda ta zargi sojojin ƙasar tare da haɗin gwiwar sojojin haya na Wagner da kama motoci biyu na fasinja a ranar 17 ga Fabrairu, sannan suka kashe fararen hula da ke cikin motar, ciki har da mata da ƙananan yara waɗande suke hanyarsu ta zuwa Algeria daga birnin Gao na ƙasar.
A wata sanarwa da babban hafsan sojin ƙasar Mali, Janar Oumar Diarra ya fitar, ya ce zargin, "wanda ƴanta'adda da masu goyon bayansu suka fitar, yunƙurin ɓata wa ƙasar suna ne."
"Rundunar sojin ƙasar za ta buɗe bincike kamar yadda take gudanar da wani binciken kan zargin sojojinta da kashe wasu mutum bakwai fararen hula a wata mota ƙirar Hilux a yankin Doma a ranar 2 ga Janairun 2025," in ji shi.
An dai daɗe ana gwabzawa tsakanin gwamnatin Mali da ƴan tawayen Tuareg da ke arewacin ƙasar.

















