Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. Fubara ya kutsa hukumar zaɓen jihar Rivers yayin da 'yansanda ke 'yunƙurin ƙwace iko' da shi

    Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya ce ya daƙile yunƙurin ƴansandan jihar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ƴansandan jihar na ƙwace iko da ofishin hukumar zaɓen jihar da tsakar dare.

    Cikin wani bidiyo da Gidan Talbijin na Channels ta wallafa, gwamnan ya ce ya je ofishin ne bayan da ya yi zargin cewa wasu jami'an ƴansanda sun yi yunƙurin shiga cikin harabar hukumar zaɓen tare da zargin su da watsa wasu muhimman takardun zaɓen da aka shirya gudanarwa ranar Asabar.

    Rahotonni sun ce jami'an tsaron da ke gadin hukumar ne suka sanar da jami'an hukumar da wasu hukumomin gwamnati yunƙurin 'yansanda, waɗanda su kuma nan take suka sanar da gwamnan, wanda shi kuma bai yi wata-wata ba ya garzaya shalkwatar hukumar da tsakar daren.

    'Yansandan dai sun ce suna biyayya ga umarnin kotun tarayya da ke Abuja da ta hana gudanar da zaɓen, yayin da shi kuma Gwamnan Fubara ya kafe cewa sai an gudanar da zaɓen.

  2. Khamenei ya ce harin da Iran ta kai wa Isra'ila 'ɗan ƙaramin hukunci ne'

    Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yaba da hare-haren da Iran ta ƙaddamar kan Isra'ila ranar Talata, inda ya kira su da cewa hare-hare da ke kan 'ƙa'ida''.

    Yayin da yake gabatar da huɗumar Juma'a a birnin Tehran, Mista Khamenei ya ce abin da suka yi ''ɗan ƙaramin hukunci'' ne kan Isra'ila saboda ''laifukan ban mamaki da take aikatawa''

    Dangane da harin da Hamas ta kai kan Isra'ilar a ranar 7 ga watan Okotoba, Khamenei ya fito fili ya yaba da harin wani abu da ƙasashen Musulmi da dama suka kasa fitowa fili su bayyana, inda ya nanata aniyar Iran wajen amfani da ƙawayenta domin yaƙar Isra'ila.

    Ya kira Isra'ila da mulkin “masu shan jini” da Amurka a matsayin “mahaukacin kare'' a yankin.

    Mista Khamenei - wanda ke gabatar da huɗubar Juma'arsa ta farko cikin kusan shekara biyar - ya ce Jamhuriyar Musulunci za ta ɗauki ''matakin da ya dace'' kan Isra'ila da ''ƙarfin tuwo''.

    Ya jaddada cewa Iran ba za ta lamunci ''sassauci'' ko ''ɗaga ƙafa'' kan Isra'ila ba.

    Ayatollah Khamenei wanda ya yi jawabin nasa a harshen Farsi ya jaddada cewa "haɗin kan" Musulmin duniya bisa tafarkin Alƙur'ani shi ne abin da ya zamanto wajibi a tsakanin Musulmi.

    "Maƙiyan Iran su ne dai maƙiyan Falasɗinawa da Lebanon da sauran ƙasashen Musulmin duniya." In ji Khamenei.

    Kafafen watsa labaran ƙasar ta Iran sun rawaito cewa Ayatollahi Khamenei zai yi wani jawabi da harshen Larabci domin al'ummar Lebanon da Falasɗinu.

    Jawabin shugaban addinin na ƙasar Iran dai na zuwa ne kwana uku kafin cikar hare-haren da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, sannan kuma kwanaki uku bayan harin makamai masu linzami da Iran ɗin ta kai Isra'ila.

    Daga ƙarshe kuma ya yi watsi da maganganun da ake cewa hare-haren Isra'ila na baya-bayan a kan "ƙungiyoyin ƴan gwagwarmaya" zai shafi ayyukansu.

    Wannan dai ita ce huɗuba da Khamenei ya yi karo na biyu tun bayan wadda ya yi lokacin da aka kashe Janar Qasem Soleimani a 2020.

  3. Hatsarin kwale-kwalen Neja: An gano gawarwaki aƙalla 141

    Hukumomi a Najeriya sun ce sun tsamo aƙalla gawarwaki 141 daga cikin mutanen da kwale-kwale ya kife da su ranar Talata a kogin Niger.

    Kawo yanzu akwai ragowar mutum 52 da ba a gani ba, waɗanda ake fargabar cewa sun mutu.

    Kwale-kwale ta tashi ne daga ƙauyen Gwajibo Mudi, na ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara ɗauke da fasinjoji aƙalla 300 da ke kan hanyarsu ta zuwa maulidi a garin Gwajibo na jihar Niger mai maƙwabtaka.

    Jirgin ya kife ne da fasinjoji fiye da 150 galibinsu mata da ƙananan yara, lamarin da ya jefa al'ummar yankin da dama cikin mawuyacin hali da fargaba.

    Tuni dai shugaban Najeriya Bol Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbain hatsarin.

    Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarni ga jami'ai su tabbatar masu tuƙa kwale-kwalen ba su saɓa dokar haramcin tafiye-tafiye cikin dare.

  4. 'Yansandan Rivers sun nesanta kansu daga zaɓen ƙananan hukumomin jihar

    Rundunar ƴansandan jihar Rivers ta ce ba za ta bari a yi zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka tsara gudanarwa gobe Asabar ba.

    Cikin wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar, SP Grace Iringe-Koko ta fitar, ta ce rundunar ta samu umarnin kotu da ya hana su bayar da tsaro a lokacin zaɓukan.

    Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar 30 ga watan Satumba babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramta wa rundunar barin gudanar da zaɓen da kuma bayar da tsaro a lokacin zaɓen.

    ''Kan haka ne sashen shari'a na rundunar ƴansandan ya shawarci rundunar cewa ta yi biyayya ga umarnin kotun'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Shi dai gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya dage cewa sai an gudanar da zaɓen duk da wannan umarni na kotu.

  5. Kifewar kwale-kwale ta yi ajalin aƙalla mutum 78 a DR Congo

    Aƙalla mutum 78 ne suka mutu a sanadiyar kifewar kwale-kwale a tekun Lake Kivu da ke gabashin Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo, kimanin mita 500 daga masaukinsa.

    Kwale-kwalen, wanda ya kife a ranar Alhamis ya taso ne daga birnin Minova da ke kudancin Kivu, sannan ya kife a gaɓar Goma.

    Rahotanni sun nuna cewa akwai aƙalla fasinjoji 278 a cikin kwale-kwalen, kamar yadda gwamnan yankin ya bayyana.

    "Zai ɗauki aƙalla kwana uku kafin a gano asalin adadin mutanen saboda har zuwa yanzu ba a gama aikin ceto ba," in ji gwamna Jean Jacques Purisi a zantawarsa da Reuters.

    Wani mai fafutika a yankin, Aaron Ashuza ya bayyana wa BBC cewa ya ga lokacin da ake ciro gawarwaki daga tekun, sannan aka riƙa kai wasu asibiti.

    Aƙalla yara biyu sun rasu bayan an kai su asibiti.

    Wani dattijo mai shekara 51 da ya tsira mai suna Alfani Buroko Byamungu ya bayyana wa Reuters cewa, "na ga lokacin da mutane suke nutsewa, nima dai Allah ne ya ceci ni."

  6. Ministan harkokin wajen Iran ya isa Lebanon

    A daren jiya Alhamis ne rahotanni suka nuna cewa ministan harkokin wajen Iran ya isa babban birnin Beirut na Lebanon.

    Kafofin watsa labarai na ƙasar Lebanon ne suka ruwaito hakan.

    "Jirgin saman Iran ya sauka a filin jirgin Rafic Hariri Internation tare da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi," kamar yadda kafar dillancin labarai na NNA ta ruwaito.

    Wannan ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila take ƙara zafafa hare-hare a birnin Beirut, ciki har da wani filin jirgin ƙasar.

  7. Assalamu Alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a daga nan BBC Hausa, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.