Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello Diginza, Aisha Aliyu Jaafar da Ahmad Bawage

  1. 'Ba za mu lamunci ɗabi'ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba'

    Abba kabir Yusuf

    Asalin hoton, Sanusi Bature Dawakin Tofa

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu riƙe da madafun iko a gwamnatinsa.

    A lokacin taron majalisar zartarwar jihar, Abba gida-gida ya buƙaci mambobin majalisar zartarwarsa su yi aiki bisa ƙwarewa da mutunta aikinsu.

    Gargaɗin na zuwa ne bayan ritayar kwamishinan sufuri na jihar, Ibrahim Namadi kan zarginsa da hannu a belin Danwawu, mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

    “Bari na gaya muku gaskiya, ba za mu lamunci duk wata ɗabi'ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba, don haka dole kowane mai riƙe da muƙami ya lura da kyau kan abubuwan da zai yi,'' in ji shi.

    Gwamnan ya ce masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa ba ofishinsu kawai sukee wakilita ba, suna wakiltar duka gwamnatin ne.

    ''Mun zo gwamnati ne da nufin tsaftace tarbiyya da inganta rayuwar al'ummar Kano, don haka ba za mu sauka daga kan layi ba'', kamar yadda ya bayyana.

  2. Ana tsare da Sowore cikin tasku da cin zarafi - Lauyoyinsa

    Sowore sanye da ba kin kwat da farar riga a ciki

    Asalin hoton, Sowore

    Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele Sowore da hukumomin ƙasar ke tsare da shi ya yi kiran sakinsa cikin gaggawa.

    Lauyoyin sun yi zargin cewa ana tsare da Sowore ƙarƙashin kulawar babban sifeton ƴansandan ƙasar, cikin hali maras kyau na tasku da cin zarafinsa, lamarin da suka ce yana barazana ga kariyarsa.

    A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami'an ƴansanda domin amsa wasu tambayoyi.

    Ɗaya daga cikin lauyoyin nasa da ya zanta da sashen Pidgin na BBC, Marshal Abubakar ya ce an gayyacci Sowore ne kan zarge-zargen laufukan bata suna da yin ƙaryar takardun ƴansanda.

    Ya ce ƴansanda sun nuna musu wasu takardu na ƙorafi da aka rubuta kan Soworen, yana mai zargin ƴansanda da rubuta ɗaya daga ciki ƙorafe-ƙorafen.

    Kawo yanzu dai hukumomin ƴansandan ba su ce komai ba game da tsare Soworen ba, kuma ba su mayar da amsar buƙatar da BBC ta gabatar musu na magana kan batun ba.

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da ci gaba da tsare

    Cikin wata sanarwa da ta fitar ta kira ga gwamnatin Najeriya ta saki ɗan gwagwarmayar tare da watsi da zarge-zargen da taje yi masa ba tare da wani sharaɗi ba.

    Ƙungiyar ta kuma zargin gwamnatin Najeriya da tauye haƙƙin ƴan ƙasar maimaikon sauraron ra'ayinsu.

  3. Harajin Trump kan ƙasashe fiye da 90 sun soma aiki

    Harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa gwamman ƙasashe kan kayyayakin da suke shigar wa ƙasarsa sun soma aiki.

    Haraje harajen sun bambanta- daga masu kaso 15 kamar a Koriya ta Kudu, zuwa kaso 50 kan Brazil.

    Sakamakon irin yadda aka sa sharuɗɗa masu rikirkitarwa, gwamnatoci da dama sun shiga ruɗani dangane da haƙiƙanin yawan harajin da aka ƙaƙaba musu.

    Mista Trump ya yi alƙawarin sake ƙaƙaba wasu haraje harajen, ko ƙara wa wasu, ciki har da harajin kaso 100 kan wasu kayayyaki.

  4. Thailand da Cambodia sun amince da kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu

    Shugabannin Malaysia da Thailand da Cambodia

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim (tsakiya), Fira ministan Cambodia Hun Manet (Hagu) sai muƙaddashin fira ministan Thailand's Phumtham Wechayachai (dama)

    Thailand da Cambodia sun amince su cimma matsaya kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu, bayan wani rikicin kan iyaka ya ɓarke a watan da ya gabata.

    A lokacin wani taro a Malaysia, ɓangarorin biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta haɗa da masu sanya ido daga ƙasashen duniya da za su bibiyi tsagaita wutar.

    Gwamman mutane ne suka rasa rayukansu, wasu dubun-dubatar mutane kuma suka rasa matsugunansu bayan faɗa kan iyaka ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu, rikicin da ya samo asali tun kusan shekara 100 baya.

    A makon da ya gabata ne dai aka amince da tsagaita wuta na wucin gadi.

  5. Najeriya da Indiya za su haɗa kai don yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

    Shugaban NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA da takwararta ta India, sun amince da ƙara haɗa kai wajen yaƙi da safarar muyigun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu.

    Hakan na cikin batutuwan da shugabannin hukumomin, Birgediya janar Buba Marwa mai ritaya da Mista Anurag Garg su ka amince da su a lokacin wata tattaunawa da suka yi ta intanet.

    Sun ce za su fi mayar da hankali ne kan yadda ake shigar da haramtattun magunguna kamar tramadol da magunguna masu hodar ibilis cikin Najeriya daga Indiya.

    Buba Marwa ya ce irin waɗannan ƙwayoyi na da illa matuƙa kan lafiya da tsaro a ƙasashen biyu, ya kuma ce akwai buƙatar hukumomin biyu su ƙara ƙarfafa alaƙarsu bisa la'akari da yarjejeniyar fahimta da suka sanya wa hannu a 2023.

    Ya kuma buƙaci hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Indiya NCB ya taimaka wajen bai wa jami'ansa horo na musamman.

    Najeriya na daga ƙasashen duniya da suka yi ƙaurin-suna wajen sha da safarar miyagun ƙwayoyi, abin da ya sa gwamnatin ƙasar ɗaukar matakai daban-daban ciki har da kafa ita hukumar ta NDLEA.

    TARON NDLEA DA NCB

    Asalin hoton, NDLEA

    Bayanan hoto, A lokacin taron da shugabannin hukumomin suka yi ta intanet
  6. Trump ya ce zai gana da Putin da Zelensky don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    shugabannin Amurka da Rasha da Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce akwai alamun nan ba da jimawa ba zai gana da shugabannin Rasha da Ukraine domin tattauna yarjejeniyar tsagaita wuta da ka iya kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe shekara 3 da rabi ana gwabzawa.

    Ya shaidawa manema labarai a fadar White House cewa ana ci gaba da fahimtar juna a tattaunawa tsakanin manzon da ya aika Steve Witkoff da kuma Vladimir Putin.

    Sai dai mista Trump ɗin bai tabbatar da ko an sami wata nasara zuwa yanzu ba.

    Amurka ta sanya wa'adin ranar Juma'a ga Rasha da ta amince da yarjejeniyar ko kuma ta fuskanci takunkumai.

  7. Indonesia za ta gina asibiti domin kula da Falasɗinawa 2,000

    Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata cibiyar kula da lafiya domin kula Falasɗinawa 2,000 da suka jikkata lokacin yaƙin Gaza.

    Wani mai magana da yawun gwamnati Hasan Nasbi ya musanta cewa shirin ba wai na kwashe Falasɗinawa bane.

    Ya ce da zarar waɗanda ake kula da su a asibitin da ke Galang sun warke, za su koma Gaza.

    Yankin Galang, wanda ke kusa da Singapore, ya taɓa kasancewa wani sansanin ƴan gudun hijira na Majalisar ɗinkin duniya da kuma cibiyar kula da Corona.

    Sai dai zuwa yanzu ba a tabbatar da yadda za a kai Falasɗinawa yankin ba.

  8. Sojojin Sudan sun ce sun harbo jirgin UAE da ke ɗauke da sojojin haya

    Rundunar sojin Sudan ta ce ta harbo wani jirgi na ƙasar haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ta yi zargin yana ɗauke da sojojin haya na Columbia da kuma makamai da za a kai wa dakarun RSF.

    Kafar talabijin ta Sudan ta ce aƙalla sojojin haya 40 ne ke cikin jirgin da aka harbo a lokacin da yake sauka a yankin Darfur da ke ƙarƙashin ikon RSF.

    An ɗade Rundunar sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Burhan na zargin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na ba dakarun RSF makamai.

    Duk da cewa Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sha musanta zargin.

  9. Ana sa ran harajin da Trump ya sanya wa ƙasashe fiye da 90 zai soma aiki ranar alhamis

    TRUMP

    Asalin hoton, Reuters

    A yau Alhamis ne harajin Amurka ke soma aiki kan kayayyakin Ƙasashe da dama da suka ƙunshi har da Tarayyar Turai da Afrika ta kudu da Japan da Koriya ta kudu.

    A ranar Laraba, Trump ya sake lafta wa India kashi 25 na haraji sakamakon ci gaba da sayen man Rasha, inda yanzu haraji kan kayayyakin India zai kai kashi 50 zuwa ƙarshen wata.

    Donald Trump ya ce zai iya ɗaukar irin wannan matakin kan China, a wani mataki na tilasta wa Rasha dakatar da yakinta a Ukraine.

  10. An kama sojan da ya buɗe wuta a wani sansanin soji a Amurka

    An tsare wani sojan Amurka mai mukamin sajent bayan ya buɗe wuta a wani sansanin soji a Georgia tare da raunata sojoji biyar.

    Sojojin da suka ji rauni yanzu haka suna kwance a asibiti.

    Nan take jami'an soji suka ɗauki mataki tare da kama jami'in sojin da ya yi harbin.

    Fort Stewart sansani ne da ke cike da dubban sojoji da iyalansu.

  11. Buɗewa

    Masu bibiyarmu, barka da safiyar Alhamis. Da fatan mun wayi gari lafiya.

    A yau ma za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya a wannan shafi namu na Kai Tsaye daga BBC Hausa.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta inda a nan ma za ku iya karanta ƙarin labarai har ma da kallon hotuna da kuma bidiyo.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.