Babu wata tattaunawa da Iran da ke gudana - Trump
Shugaba Donald Trump ya ce babu wata tattaunawa da ke gudana ko kuma aka shirya yi tsakanin Amurka da Iran.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Shugaban na Amurka ya ce: “Babu wata tattaunawa da ke gudana ko aka shirya yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Mashigar Hormuz a buɗe take kuma ana amfani da ita. An tarwatsa dukkan nakiyoyin da ke cikin teku.”
Kafin nan, Trump ya wallafa wani hoto a shafinsa na Truth Social da ke nuna Mashigar Hormuz da wata da'ira a kanta, tare da cewa “sabon yankin Amurka.”
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya rubuta a shafin X cewa: “Kamar yadda Donald Trump ya koyi rubuta sunan Tekun Fasha daidai, nan ba da jimawa ba za mu gyara kuskurensa game da Mashigar Hormuz.”