Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya hana APC ƙwace jihar Osun duk da tura babbar tawaga zaɓen jihar?
Zaɓen gwamnan jihar Osun ya sake tabbatar da Gwamna Ademola Adeleke a kan kujerarsa, duk da ƙoƙarin da jam'iyyar APC, mai mulki a matakin tarayya ta yi na ƙwace jihar.
APC ta sanya jihar Osun cikin jerin jihohin da ta yi muraɗin ƙwacewa gabanin zaɓen 2027 da ke tafe.
Masana siyasa sun daɗe suna kallon Osun a matsayin muhimmin jihar da ke da tasiri a siyasar yankin Yarabawa, saboda matsayinta a tarihin zaɓuɓɓukan ƙasa da kuma rawar da yankin yake takawa a zaɓen shugaban ƙasa.
Wannan ne ya sa fafatawar tsakanin APC da Adeleke ta ɗauki hankulan 'yan siyasa da masu sa ido a faɗin ƙasar.
APC ta tura manyan jiga-jiganta zuwa jihar, ciki har ga gwamnoni masu yawa da nufin sanya idanu a zaɓen, don taimaka wa jam'iyyar samun nasara.
Sai dai duk da ƙarfin kamfen, yawan tarurruka da kuma goyon bayan manyan jiga-jigan APC, masu zaɓe a Osun sun sake bai wa Adeleke dama ya ci gaba da mulki.
Wannan sakamako ya haifar da tambayoyi kan irin abubuwan da suka rinjayi zaɓen da kuma ko jam'iyyar APC ta yi kuskure wajen fahimtar yanayin siyasar jihar.
A wannan muƙala mun duba abin da ya hana APC ƙwace jihar, duk kuwa da tura jiga-jiganta zuwa jihar.
Yunƙurin amfani da ƙarfi a zaɓen
Dr Kabiru Sa'id Sufi, malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a, kuma mai sharhi kana al'amuran siyasar Najeriya, ya ce ɗaya daga cikin dalilan da suka hana APC samun nasara a jihar Osun shi ne yadda ta riƙa nuna alamun ƙwace jihar ƙarfi da yaji.
Masanin siyasar ya ce bayar da misalin ga yunƙurin kama sakataren gwamnatin jihar da hukumomi suka yi.
Ga kuma yunƙurin hukumomi na kama kakakin majalisar dokkin jihar.
Masanin siyasar ya kuma ce EFCC ta sanar da rufe asusun gwamnatin jihar, wanda wasu ke ganin kamar da sanin APCn aka yi hakan.
''Waɗannan abubuwa duka sun tunzura al'ummar jihar, inda suka ɗauka kamar APC na amfani da hukumomin gwamnati ne wajen muzguna wa ƴan hamayya'', in ji shi.
Matsala a zaɓen fitar da gwani
Masanin kimiyyar siyasar ya ce wani babban dalilin rashin nasarar APC shi ne tsayar da ɗantakarar da ba shi ƴan jam'iyyar jihar suke so ba.
''Akwai zargin da ake yi cewa wanda APC bayyana a matsayin ɗantakarar ba shi ne ƴan jam'iyyar jihar suke so ba'', in ji shi.
Dr Sufi ya ce tun da farko ma an yi raɗe-raɗin cewa Adeleke APC zai koma bayan ficewarda daga PDP, amma sai masu ruwa da tsakin jam'iyyar suka nuna cewa sun fi son ɗantakarar da suka tsayar.
Kalaman Sanata Francis Fadahunsi
Dr Sufi ya ce wani dalilin shi ne kalaman da Sanata Fadahunsi na jam'iyyar APC ya yi cewa ''a kashe duk ɗan Accord Party da aka gani a Ilesha.
Kalaman na Sanata Fadahunsi sun haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin jihar, lamarin da ya sa rundunar ƴansandan jihar gayyatarsa domin ƙarin bayani a ofishinta.
''Waɗannan kalamai sun janyo wa jami'iyyar Accord Party tausayawa daga masu zaɓe'', kamar yadda masanin siyasar ya yi ƙarin haske.
Farin jinin Adeleke
Dr Sufi ya ce shi ma gwamnan jihar Adeleke na da farin jini tare da samun goyon bayan jihar.
''Gwamnan ya yi amfani da dabara irin ta siyasa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta kammala a daidai lokacin da ake taka da yaƙin neman zaɓe, wanann ta ƙara masa farin ji tsakanin masu zaɓe'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ƙara da cewa matsayin da gwamnan ya ɗauka wajen samar da daidaito tsakanin manyan addinan jihar ya taimaka masa wajen samun karɓuwa tsakanin duka addinan biyu.