Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Hare-hare shida da ƴanbindiga suka kai kan masu sallah a Najeriya

    Mummunan harin da ƴanbidiga suka kai wa wasu masallata a masallacin jihar Katsina tare da kashe masu ibada na ci gaba da tayar da hankali a Najeriya.

    Maharan sun far wa masallatan a lokacin da suke tsaka da sallar asuba a garin Unguwar Mantau cikin ƙaramar hukumar Malumfashi tare da buɗe musu wuta.

    Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28 tare da jikkatar wasu da dama.

    Wasu garuruwan yankunan arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren ƴanbindiga waɗanda a wasu lotukan kan tilasta wa mazauna garuruwa da ƙauyuka tserewa.

    Latsa nan don karanta cikakken labarin...

  2. Muna kira a gaggauta tsagaita wuta a Gaza - MDD

    Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya sake sabunta kiran da a gaggauta tsagaita wuta a Gaza, bayan Isra'aila ta ce ta fara kai farmaki domin ƙwace birnin Gaza.

    Mista Guterres, ya ce yana da matukar muhimmanci a kiyaye da kashe-kashe da kuma lalata duƙiyar da wannan farmaki zai haddasa.

    Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da fara kai matakin farko na farmakin a Gaza, inda firaiministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya ce yunkuri ne na ganin ya ƙwace abin da ya kira waje na karshe a Gaza.

    Jami'ai a Gaza sun ce dubban Falasɗinawa na tserewa birnin wanda Mutane fiye da miliyan guda ke rayuwa a cikinsa.

  3. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai kasance da ku a wannan safiya!