Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba ma goyon bayan kara albashi ga masu rike da mukaman siyasa — ADC
Sabuwar jam'iyyar hadakar 'yan adawa a Najeriya ta ADC ta bayyana damuwa a game da shirin kara albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar.
Jam'iyyar ta bayyana shirin da cewa ''yin biris ne'', kuma cin fuska ne ga al'ummar kasar da ke fama da katutun matsalolin rayuwa da suka hada da hauhawar farashin kaya da tashin farashin mai da kwauron albashi mafi kankanta da dai sauran matsaloli.
Daya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar hadakar ta ADC, Faisal Kabiru, ya shaida wa BBC cewa, duba da halin da talakan Najeriya ke ciki wanda abinci ke gagararsa ballantana magance wasu matsaloli na rayuwa, ace za a karawa mutanen da suke rayuwa yadda suke so saboda suna da hali albashi.
Ya ce," Mu a matsayinmu na jam'iyya munyi alawadai da wannan mataki na karawa 'yan siyasa albashi, domin suna samun alawus su yi duk abin da suke bukata, sannan gashi gwamnati na dauke musu yawancin bukatunsu a don haka ya za a hadashi da mutumin da ke daukar albashin naira dubu 70."
Faisar Kabiru, ya ce:: " Wannan mataki gaskiya ya nuna cewa ita wannan gwamnati bata damu da halin da talakawan Najeriya ke ciki ba."
" Su fa wadannan 'yan siyasar babu wani da suke bukata abinci suna da shi sannan lafiyarsu ma kasashen waje suke fita don a dubasu, to amma shi talaka bashi ma da kudin da zai je asibiti haka cin abinci sau uku ma ba kowa ba ne a wannan yanayi da ake ciki."In ji dan adawar.
Ya ce," Talaka fa ya kamata a rinka dubawa a kodayaushe ba 'yan siyasa da kowacce kasa suke son zuwa zasu je ba."
Faisal Kabiru, ya ce," Babban abin dubawa ma shin su wadannan 'yan siyasa duk da talakan Najeriya suke yi wa aiki, ya kamata a duba a gani shin sun sauke nauyin da aka dora musu?, misali har yanzu a Najeriya ana fama da matsalar rashin tsaro ga yunwa ana fama da ita a ko ina, to ta yaya kuma za a ce wai za a kara musu albashi, to akan me?."
"Sam basu cancanci wannan karin albashi ba domin ba sa yin abin da ya dace, ya kamata su fara sauke nauyin da ke kansu kafin ayi batun kara musu albashi."In ji Faisal.
Dan adawar ya ce, " Ba batu na adawa muke ba, abin damuwarmu shi ne wannan tsari da aka dauko sam bai dace ba kuma son kai ne tsagwaronsa."
Batun sake nazarin albashin masu riƙe da mukaman siyasa a Najeriya na ci gaba da tayar da ƙura a ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar raba arzikin ƙasa ta Najeriya (RMAFC) ta sanar da cewa ta fara shirin sake nazarin yadda ake rarraba arzikin ƙasa tsakanin matakan gwamnatin tarayya da jihohi da kuma ƙananana hukumomin ƙasar.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, shugaban hukumar ta RMAFC Mohammmed Shehu ya yi iƙirarin cewa albashin da masu riƙe da mukaman siyasa ke karɓa bai taka kara ya karya ba, yayin da kuma ake fama da matsin tattalin arziki a ƙasar.
Shugaban ya ce a halin da ake ciki yanzu shugaba Bola Tinubu na karɓar naira miliyan 1.5 ne kowanne wata, yayin da abin da ministoci ke karɓa bai kai naira miliyan ɗaya ba.