Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai - Musa

    Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa

    Asalin hoton, Nigeria Defence Headquaters

    Bayanan hoto, Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa

    Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya shawaraci ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.

    C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a yau Alhamis.

    Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.

    Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar ƙasar.

    Lokacin da aka tambayi Christopher Musa kan ko ya kamata al'umma su koyi dabarun faɗa, ya ce "Ya kamata mutane su ɗauki wannan tamkar koyon tuƙi ne ko iyo, wannan abu ne da ake buƙata a rayuwa, ko da ana fama da yaƙi ko a'a".

    "Ina ganin ya kamata a wayar da kan kowane ɗan Najeriya kan tsaro a kowane mataki. Kare kai na da matuƙar muhimmanci," in ji Musa.

    Ko a ranar Litinin, wasu mahara sun kashe masu ibada aƙalla 28 a wani masallaci da ke karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin ƙasar.

    Haka nan a watan da ya gabata masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago cikin waɗanda suke garkuwa da su a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.

  2. Kotu ta yi watsi da hukuncin biyan tara da aka yanke wa Donald Trump

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kotun ɗaukaka ƙara a jihar New York da ke Amurka, ta yi watsi da tarar dala miliyan 500 aka yanke wa Shugaban ƙasar Donald Trump, bayan kama shi da laifin kambama dunkiyarsa domin yaudarar masu bayar da bashi da kamfanonin inshora.

    Kotun ta ce tarar ta zarce ƙa'ida, duk da dai alƙalan sun amince cewa ya yi laifi, sun ce bai kai girman da za a sanya masa wannan tarar ba.

    Sai dai kuma kotun ba ta yi watsi da karar ba, kamar yadda mista Trump ya buƙata. Duk da haka, mista Trump ɗin ya bayyana hukuncin a matsayin nasara gare shi.

    Alkalin da ya yi shari'ar a bara ya ce Donald Trump da manyan ƴaƴansa maza da kuma wata ƙungiyarsa sun kambama dukiyarsa domin samun basuka masu kauri.

  3. Najeriya ta kori ƴan China 60 bisa laifin damfara

    ...

    Asalin hoton, X/EFCC

    Najeriya ta ce ta mayar da ƴan ƙasashen waje 102 gida daga ƙasar, waɗanda suka haɗa da ƴan China 60 da ƴan ƙasar Philippines 39 bisa kama su da laifin damfara ta intanet.

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasar, EFCC ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis.

    Tun farko hukumar ta bayar da sanarwar korar ƴan China 50, inda a yau kuma mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya shida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an ƙara korar wasu ƴan Chinan 10 da mutanen Kazakhatan biyu daga ranar 15 ga wannan wata na Agusta.

    Haka nan ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da korar bakin da aka kama da irin waɗannan laifuka a kwanaki masu zuwa.

    Waɗanda aka korar na cikin mutane 792 da aka kama a Legas bisa zargin damfara ta Intanet a watan Disamban da ya gabata.

    Aƙalla 192 daga cikin wadanda aka kaman yan asalin kasashen waje ne, inda ake da ƴan China 148.

    Najeriya ta yi ƙaurin suna kan damfara ta intanet, wanda ake wa laƙabi da Yahoo-Yahoo.

    Hukumar EFCC ce ke ƙoƙarin dakile matsalar, sai dai har yanzu matsalar na ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji.

    A kwanakin baya hukumar ta sanar da bankaɗo cibiyoyin koyar da matasa irin wannan damfara ta intanet.

  4. Sama da mutune miliyan 15 suka yi aikin Umara a farkon 2025

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawan al'ummar Musulmai da suka gudanar da aikin Umara a Saudiyya cikin wata ukun farkon shekara ta 2025 ya zarce miliyan 15, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasar Saudiyya, kamar yadda ta bayyana a yau Alhamis.

    Rahoton hukumar ya ce daga cikin waɗannan masu ibada, sama da miliyan shida sun fito ne daga ƙasashen ƙetare yayin da sama da miliyan takwas suke daga cikin gida.

    Hakan ya nuna cewa yawan masu ibada da suka gudanar da Umara a wannan shekara ya ƙaru da kashi 7 cikin ɗari idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a bara, 2024.

    Umara aikin ibada ne da Musulmai kan gudanar a birnin Makka a kowane lokaci na shekara, akasin aikin hajji wanda akan yi shi sau ɗaya a shekara a wani ƙayyadajjen lokaci.

    Masu yin Umara kan yi aikin ne domin neman kusanci da mahalicci da kuma neman gafara.

  5. Inec ta miƙa wa ƴan majalisar Tarayya da suka lashe zaɓen cike gurbi takardun shaida

    Ɗan takarar da ya lashe zaɓen cike gurbi na majalisar wakilan Najeriya daga mazaɓar Ɓaɓura/Garki a jihar Jigawa, Mukhtar Rabiu Garki lokacin da ya karbi takardar shaidar lashe zaɓe daga Inec a yau Alhamis

    Asalin hoton, X/Inecnigeria

    Bayanan hoto, Ɗan takarar da ya lashe zaɓen cike gurbi na majalisar wakilan Najeriya daga mazaɓar Ɓaɓura/Garki a jihar Jigawa, Mukhtar Rabiu Garki

    Hukumar zaɓen Najeriya Inec ta miƙa takardun shaidar lashe zaɓe ga ƴan takarar jam'iyyu daban-daban waɗanda suka yi nasara a zaɓen cike gurbi na sanatoci da majalisar wakilan Tarayya da aka gudanar ranar Asabar 16 ga watan Agusta.

    A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, Inec ta ce bisa dogaro da sashe na 71(1) wajibi ne baturen zaɓe ya gabatar da takardar shaidar lashe zaɓe ga ɗan takarar da ya yi nasara a cikin kwana 14 bayan gudanar da zaɓe.

    Dalilin haka ne a yau Alhamis wakilan hukumar suka miƙa wa ƴan takara bakwai da suka yi nasara takardun nasu.

    Biyu daga cikinsu sanatoci ne daga jihohin Anambra da kuma Edo.

    Sai kuma ƴan majalisar wakilan tarayya ɗaɗɗaya daga jihohin Edo da Jigawa da Kaduna da Ogun da kuma Oyo.

    A ranar Asabar 16 ga watan Agusta ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta gudanar da zaɓukan cike gurbi a mazaɓun majalisar dattijai biyu da na wakilai biyar da kuma na ƴan majalisar dokokin jiha tara.

    Hukumar ta sanar da sakamakon zaɓukan a dukkanin mazaɓu duk kuwa da hargitsi da kuma kiraye-kirayen soke zaɓen a wasu jihohi.

    Saƙon da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fitar na taya ƴan takarar da suka yi nasara murna ya nuna cewa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta lashe mazaɓu 12, APGA ta lashe kujeru biyu, PDP ta lashe kujera ɗaya, ita ma NNPP ta lashe ɗaya.

    Sai dai an ayyana zaɓen majalisar dokokin jihar Zamfara a mazaɓar Ƙauran Namoda ta kudu a matsayin wanda bai kammala ba sanadiyyar hargitsin da ya yi sanadin soke sakamako rumfunan zaɓe biyar.

  6. Fursunoni 80 sun tsere daga gidan yari mai cike da matakan tsaro a Habasha

    Ethiopia

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kafar yaɗa labaran Habasha mai goyon bayan ƴan adawa ta ce fursunoni aƙalla tamanin sun tsere daga wani gidan yari mai cike da matakan tsaro a babban birnin ƙasar Addis Ababa ta hanyar haɗa kai da masu tsaron su.

    Rahoton da kafar mai suna Anchor Media da ke Amurka ta fitar, ya ce su ma masu tsare da su ɗin sun tsere daga gidan yarin Aba Samuel.

    Rahoton ya kuma ce sauran masu tsaron fursunonin sun yi ta harbin mutanen da suka guda, inda suka jikkata wasu.

    Zuwa yanzu dai gwamnatin ƙasar ba ta ce komai ba.

    A farkon watannan ma fursunoni aƙalla 150 sun tsere daga gidan yari a ƙasar bayan wasu ƴan tawaye ƴan ƙabilar Oromo sun kai hari kan gidan yarin.

  7. Ukraine ta kai hari kan matatar man fetur a Rasha

    Matatar fetur

    Asalin hoton, Telegram/Astra

    Ukraine ta ce ta kai sabbin hare-hare zuwa cikin ƙasar Rasha.

    Sojojin ƙasar sun ce harin ya faɗa kan wata matatar man fetur a yankin Rostov - wadda ke iyaƙa da birnin Luhansk na Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wuta ke tashi a masana'antar da ke Novoshakhtinsk kusa da iyaƙa da Ukraine ɗin.

    Kyiv ta kuma ce ta harba wani jirgi mara matuki na Rasha a gabashin birnin Donetsk da aka yi ƙawanya.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce hare-hare da ta kai Ukraine cikin dare - sun faɗa kan gine-ginen soji da masana'antu da kuma na makamashi.

    Sai dai babu wasu hujjoji kan iƙirarin na Rasha ba.

  8. An tsare mawaƙin Ghana Shatta Wale bisa zarginsa da alaƙa da masu aikata zamba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Ghana sun ce an tsare shahararren mawakin nan Shatta Wale a wani bincike da ake yi kan sayan wata mota ta alfarma.

    An kama motar mawaƙin ƙirar Lamborghini mai launin rawaya a farkon wannan watan bisa buƙatar Amurka, wanda ta yi zargin cewa an sayi motar ne kuɗaɗen da aka samu ta haramracciyar hanya.

    Ofishin yaƙi da msau yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa na Ghana (Eoco) ya ce Wale ya miƙa wuya bisa radin kansa ranar Laraba kuma daga bisani aka yi masa tambayoyi kan motar.

    Hukumar FBI da ma’aikatar shari’a ta Amurka ce ta bayyana cewa motar nau'in Lamborghini Urus na da alaƙa da ne da wani zamba da aka yi na dal miliyan huɗu da ta shafi wani Nana Kwabena Amuah, ɗan Ghana da ke zaman gidan yari a Amurka”.

    Wale ya musanta cewa yana da wata alaƙa da Amuah, wanda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai bisa laifin zamba a shekarar 2023.

  9. BBC ta gano Birtaniya ta yi kuskure wajen sakin bayanan ƴan Afghanistan

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    BBC ta gano cewa ma'aikatar tsaron Birtaniya ta yi kuskure wajen sakin bayanan ƴan ƙasar Afghanistan din da a baya suka yi aiki tare da sojojin Birtaniya a karo da dama a cikin shekaru fiye da 4.

    Bayanan sun fito ne daga cikin wani shiri da ake yi wa wasu ƴan ƙasar waɗanda ke cikin haɗarin fuskantar barazanar ƴan Taliban na sake musu matsugunni.

    A cikin shirin an samar da wata takarda wadda ke ɗauke da cikakken bayanan mutane kusan dubu guda da suke son a sake musu matsugunnin.

    Lauyoyin waɗanda abin ya shafa sun soki shirin inda suka ce an yi abin da bai dace ba a yayin kuɓutar da mutanen da suke karewa.

  10. M23 sun musanta kashe fararen hula a Kongo

    M23

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan tawayen M23 da ke gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo sun musanta zargin da ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta yi cewa sun kashe aƙalla fararen hula 140 a ƙasar a watan da ya gabata.

    Sun yi watsi da rahoton na ƙungiyar.

    Human Rights Watch ta ruwaito cewa ƴan tawayen sun zartas da hukuncin kisa kan mazauna ƙasar, yawanci waɗanda suka fito daga kabilar Hutu da ke yankin Rutshuru a arewacin Kivu.

    M23 ɗin ta zargi HRW da gaza shigar da wasu ƙungiyoyi a tattaunawa da ake yi a yankin, inda ta ce rahoton ba shi da cikakkun bayanai.

    Sun yi watsi da rahoton bincike da HRW ta yi da cewa babu gamsassun hujjoji kawai caci faɗi ce.

  11. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Zaidu na Gidan Badamasi

    A cikin shirin ...Daga Bakin Mai Ita da muke kawo muku a kowane mako, a yau mun kawo muku hira da Muhammad Aminu Shehu da aka fi sani da Mallam Zaidu na Gidan Badamasi.

    Mallam Zaidu ya ce ya fara harkar film tun a 1997, amma sai a 1999 aka fara haska shi a fina-finan Hausa, kodayake ya ce sai a shekarar 2000 zuwa 2001 ya fara fice a masana'atar a lokacin da ake kiransa da Aminu Mirror.

    Ya ce ya yi amintaka da tsohon jarumin Film marigayi Ahmad S Nuhu, da ya ce sun yi zumunci mai zurfi kafin Allah ya yi sama cikawa.

    Ya ce Darakta film ɗin Gidan Badamasi ne ya ba shi matsayin Mallam Zaidu a ciki film ɗin, bayan ya burge shi a wani film.

    Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
  12. Fafaroma Leo ya buƙaci al'umma su tashi da azumi ranar Juma'a don rokon zaman lafiya

    Pope Leo XIV

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Robert Prevost ya buƙaci al'umma su tashi da azumi ranar Juma'a don rokon samun zaman lafiya a duniya.

    Fafaroma Leo na 14 ɗin ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

    Ya ce ya kamata al'uma su yi azumi don rokon Allah ya kawo wa al'umma sauki daga rikice-rikice da ake fama da su a faɗin duniya.

    "Al'umma su tashi da azumi ranar Juma'a don rokon samun zaman lafiya, musamman ga mutanen da ke fama da rikice-rikice," in ji Fafaroma Leo.

    Buƙatar da Fafaroman ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice a sassan duniya, ciki har da yaƙin Gaza da kuma na Ukraine.

  13. Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya yi Alla-wadai da sabbin hare-hare da Rasha ta kai Ukraine.

    Ya ce abin takaici ne ganin cewa Rasha ta kai harin, kuma babu wani ƙoƙari da duniya ke yi don dakatar da yaƙin.

    Zelensky ya ce an harba jirage marasa matuki sama da 570 da kuma makaman linzami 40 zuwa ƙasar.

    Shugaban lardin Lviv ya ce an kashe mutum ɗaya a harin da jikkata guda uku.

    Harin ya kuma lalata rukunin gidaje sama da 20, ciki har da wata makaranta.

    Har ila yau, harin na Rasha ya faɗa kan wata masana'antar ƙera laturoni mallakin Amurka, inda mutum aƙalla 15 suka jikkata - har da tashin gobara.

    Wani ɗan siyasa a yankin ya ce an kai harin ne da niyyar firgita masu zuba jari daga ƙasashen waje.

  14. Buƙatar Najeriya da Tinubu ya gabatar a taron Japan

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi kiran samar da sauye-sauye a tsarin Majalisar Dinkin Duniya don bai wa Afirka kujerun dindindin biyu a kwamistin tsaro na Majalisar.

    Yayin da yake jawabi a taron duniya kan ci gaban ƙasashen Afirka a birnin Yokohama na ƙasar Japan, Tinubu ya ce nahiyar Afirka ta cancanci matakin saboda irin gudunmowarta ga zaman lafiya.

    “Babban burin Najeriya shi ne Afirka ta samu cikakken wakilci a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” in ji Tinubu.

    Shugaban na Najeriya ya ce nahiyar na samun damar samun hawa kujerar na-ƙi, baya da ƙarin wakilci a kujerun da ba na dindindin ba.

    Bola Tinubu ya kuma jinjina wa dakarun tsaron Najeriya kan nasaroroin da ya ce sun samu a baya-bayan nan kan yaƙi da ta'addanci a ƙasar.

  15. Ƴan kasuwar Sokoto sun ƙoƙa kan ɓarayi da ke fasa musu shaguna, Daga Zubairu Ahmad

    Ƴan kasuwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan kasuwa a babbar kasuwar jihar Sokoto da ta yi gobara a bara, sun ƙoƙa kan cewa ɓarayi na amfani da wani ɓangare da gwamnatin jihar ke ci gaba da aikin gina wa, wajen shiga da daddare suna fasa shaguna tare da kwashe kuɗaɗe da kuma kayayyakinsu.

    Ƴan kasuwar dai sun ce lamarin ya wuce gona da iri kasancewar cikin ƙanƙanin lokaci ɓarayin sun sace duƙiya da ta kai ta miliyoyin naira.

    Sun buƙaci hukumomi a jihar su ɗauki matakin kawo karshen wannan matsala.

    Wasu ‘yan kasuwar sun bayyana cewa sun sha yin ƙorafi a lokuta da dama, inda suka nemi hukumomi su ɗauki matakan da suka dace domin yi wa tufka hanci, amma har yanzu shiru.

    Ƴan kasuwar sun ce abin da janyo ƙaruwar wannan matsala ta fasa shaguna shi ne rashin kammala aikin wasu shaguna da ake kan gina wa tun bayan da wani ɓangaren babbar kasuwar ta Sokoto ya yi gobara a bara.

    Sun ce hakan ne ya sa ɓata-gari ke shiga cikin kasuwar idan kafa ta ɗauke suna yi musu ɓarna.

  16. Wani hari ya janyo mutuwar gomman sojojin Mali

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    Dubban sojojin Mali ne suka mutu bayan a wasu jerin hare-hare da ake zargin mayaƙa da ke alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda da kai wa cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar sojojin ƙasar.

    An kai harin ne kan sansanin sojojin ƙasar a Farabougou da sanyin safiya, bayan afka wa garin Kassela mai nisan kilomita 40 da Bamako, babban birnin ƙasar.

    An ruwaito cewa mayaƙa daga ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) sun buɗe wuta kan shingayen binciken sojoji da dama.

    Sun ce sun kashe aƙalla sojoji 21 tare da ƙwace makamansu.

    Harin na zuwa ne lokacin da ake samun ƙaruwar zaman fargaba, inda shugaban gwamnatin mulkin sojin ƙasar Janar Assimi Goïta ya amince da wata doka da za ta ba shi damar zama kan mulki sai yanda hali ya yi.

    Tun bayan karɓe iko bayan juyin mulki a 2020, gwamnatin ƙasar ta yanke hulɗa da ƙawayenta na yamma tare da komawa ga Rasha don neman taimakon soji.

  17. Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 47 a Nijar

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce ambaliya ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 47 a ƙasar.

    Sannan ta kuma ɗaiɗaita sama da mutum 56,000.

    Kwamitin da gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta kafa don taƙaita afkuwar ambaliya, ta ce ta fara tallafawa mutanen da lamarin ya shafa ta hanyar raba wa iyalai abinci.

    Ana ƙara samun afkuwar ambaliya a faɗin yankin Sahel, sakamakon sauyin yanayi da ake samu.

  18. Sojojin Sudan sun musanta far wa ayarin motocin WFP

    Motocin agaji

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Sojojin Sudan sun musanta kai wa ayarin motocin shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) hari a arewacin Darfur, bayan da dakarun RSF suka zarge su da kai hari a garin Mellit.

    WFP ya tabbatar da cewa hari ya faɗa kan motocinsa na agaji guda uku, lamarin da ya jikkata ma'aikatansa.

    Motocin na kan hanyarsu ne zuwa wani yanki da yake fama da fari a arewa maso yammacin birnin El Fasher da aka yi wa ƙawanya.

    Dakarun RSF suna ƙara matsa ƙaimi a ƙoƙarinsu na ganin sun karɓe iko da birnin a makonnin baya-bayan, duk da kiran tsagaita wuta daga ƙasashen waje don samun damar shigar da agajin da ake buƙata.

    Rikicin Sudan dai ya ɗaiɗaita miliyoyin mutane, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa da yawa na fuskantar barazanar faɗa wa yunwa.

  19. Tarihi ba zai taɓa mantawa da Buhari ba - Bisi Akande

    Bisi Akande

    Asalin hoton, Godwin Isenyo

    Shugaban jam'iyyar APC na farko kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande ya jagoranci tawagar ƴansiyasa zuwa ta'aziyyar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

    Sun kai ziyarar ce gidan marigayin a jihar Kaduna ranar Laraba, inda Akande ya kwatanta shi da shugaba na gari wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba saboda kyayawan ayyuka da ya yi a ƙasar.

    Matar marigayin ne Aisha Buhari da kuma ɗansa Yusuf Buhari ne suka tarbi tawagar ƴansiyasar.

    Akande ya nuna kaɗuwarsa kan mutuwar tsohon shugaban ƙasar, inda ya ce lokaci na karshe da suka haɗu shi ne lokacin da ya kai masa ziyara a Daura.

  20. An zargi tsohon shugaban Brazil da katsalanda lokacin yi masa shari'a

    Bolsonaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansanda a Brazil sun zargi tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro da ɗansa Eduardo da yin katsalandan yayin shari'ar da ake masa bisa zargin kitsa juyin mulki.

    Eduardo Bolsonaro ya koma Amurka a shekarar nan, inda ya nemi goyon bayan Amurka kan ta taimakawa mahaifinsa wanda abokin siyasar Donald Trump ne, kuma wannan yunkuri nasa ya janyo Amurka ta sanya harajin kashi 50 cikin 100 kan Brazil.

    Eduardo Bolsonaro ya musanta zargin, inda ya kira shi da cewa bita da kulli ne.

    Jair Bolsonaro wanda ke karkashin daurin talala ya musanta kitsa hambarar da gwamnatin shugaban kasar na yanzu Lula da Silva.