Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni na yau Laraba 21 ga watan Mayu.

    Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Masu motocin sufuri a Ghana za su rage farashin kuɗin mota

    motocin sufuri

    Ƙungiyar masu motocin sufuri mai zaman kanta a Ghana (GPRTU) ta sanar da cewa ƴaƴanta za su rage farashin kuɗin mota da kashi 15 cikin 100, daga ranar Asabar 25 ga watan Mayu.

    An ɗauki matakin ne a wani taro da aka yi tsakanin shugabannin ƙungiyar na ƙasa da ministan sufuri.

    Kakakin hulɗa da masana'antu na ƙungiyar, Alhaji Abbas Ibrahim Moro ya ce sun ɗauki matakin ne domin yayi dai-dai da ragin da aka samu a farashin man fetir da kusan kashi 18 da kuma farfaɗowar darajar kuɗin ƙasar Cedi.

    Ya kuma ce su ma ƙungiyar masu sayar da kayyayakin gyaran mota na ƙasar sun ce nan ba da jimawa ba za su rage kudin kayyaykinsu.

    Alummar ƙasar sun bayyana jin daɗinsu game da matakin, inda suka ce ya dace ganin cewa an sami ragi daga gwamnati.

    A shekarun baya an yi ta ƙarin farashin kuɗin mota a Ghana saboda hauhawar farashin mai da na kayyyakin gyaran mota.

  3. Sojojin Isra'ila sun buɗe wuta kan tawagar diflomasiyya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar yankin Falasdinawa ta zargi sojojin Isra'ila da buɗe wuta kan wata tawagar diflomasiyya a yankin gaɓar yamma da kogin Jordan da ta mamaye.

    Ba a samu rahoton jikkata ba a lamarin da ya faru a birnin Jenin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an yi harbi ne a sama bayan da tawagar da ta haɗa da jami'an diflomasiyya daga Sifaniya da Canada suka kauce daga hanyar da aka amince su bi.

    Ta ce sojojin da suka yi harbin ba su yi la'akari da cewa jami'an diflomasiyya ba ne kuma sun yi harbin ne don a gargaɗe su cewa su juya.

    Jami'ar kula da harkokin waje na kungiyar EU Kaja Kalas ya yi kira ga Isra'ila da ta gudanar da bincike tare da hukunta sojojin da ke da hannu cikin lamarin.

  4. Ƙungiyoyin kare haƙƙin biladama a Jamhuriyar Nijar sun buƙaci kare haƙƙin masu ƙaura da Aljeriya ta koro

    masu gudun hijira

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu Ƙungiyoyin fararen hula a jumhuriyar Nijar dake fafutukar kare haƙƙin masu ƙaura sun yi kiran a kare haƙƙin mutanan da ƙasar Aljeriya ta koro.

    Ƙungiyoyin sun haɗa har da Alarm Phone Sahara da Maghreb Sahel Migration Network, kuma sun yi gargaɗin cewa ana turo mutane da dama daga Aljeriya ba tare da kula da dokokin kare haƙƙin ɗan adam ba.

    Ƙungiyoyin su yi wannan kira ne bisa la’akari da yadda ƙasar ta Aljeriya ke taso ƙeyar dandazon al’umma zuwa kan iyaka da ƙasar ta jamhuriyar Nijar ba tare da ɗaukar wasu matakai ba na kare haƙƙin su.

    Sun kuma yi Allah wadai game da halin ko-in-kula da ƙungiyar haɗin kan Afrika da kuma sauran ƙungiyoyin yankin su ka yi kan wannan lamari da kuma rashin ɗaukar wani matakin gaggawa a kan lamarin.

    Gwamnatin kasar Nijar ta sanar da tsarin ta na mayar da sauren yan ƙasahen Afrika su dubu huɗu kasashen su na asali daga watan Yuli .

  5. Gwamnatin Amurka ta amince da kyautar jirgin da Qatar ta bai wa Trump

    Jirgin Air Force One

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta amince da jirgin ƙasaita da Qatar ta bai wa Shugaba Trump domin amfani da shi a matsayin jirgin gwamnati na Air Force One.

    Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka Sean Parnell ya ce an amince da jirgin samfurin Boeing 747 ne bisa la'akari da dukkanin dokokin gwamnati.

    Fadar White House ta jaddada cewa kyautar jirgin daga gidan sarauta ta Qatar ya halarta.

    Sai dai amincewa da jirgin ya janyo ce-ce-kuce a makon da ya gabata.

    An buƙaci rundunar sojin saman Amurka ta hanzarta wajen kammala ƙara inganta jirgin.

    Wasu hasashen da aka yi na nuna cewa za a kashe biliyoyin daloli wajen inganta tsaron jirgin zuwa matakin da ya dace da jirgin shugaban ƙasa.

  6. An gano Hamdiyya Sidi Shariff a asibiti - Abba Hikima

    ..

    Asalin hoton, Abba Hikima

    Lauyan matashiyar nan da gwamnatin jihar Sokoto ke tuhuma da "kalaman tunzura jama'a" wadda da farko aka nema aka rasa, yanzu haka ya ce tana babban asibitin garin Bakura da ke jihar Zamfara a cikin mawuyacin hali.

    Abba Hikima wanda ya tabbatar wa da BBC hakan ya ce ya yi imanin sace matashiyar aka yi.

    A ranar Larabar nan ne dai lauyan Hamdiyya, Abba Hikima ya faɗi cewa matashiyar ta bar gida domin yin cefanen kayan abinci a ranar Talata da safe kuma tun lokacin ba a ƙara jin ɗuriyarta ba.

    BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Abubakar Bawa, mai magana da yawun gwamnan jihar Sakkwato, game da wannan batu. Amma bai amsa kiraye-kirayen wayar da muka yi masa ba, kuma bai maido da amsar saƙon kar-ta-kwana da muka aika masa ta wayar ba.

  7. Katsewar wutar lantarki ta sa ƙasashen neman haɗn kai

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasashen Sifaniya da Portugal sun buƙaci ƙungiyar Tarayyar Turai da ta ƙara ƙarfafa hada-hadar wutar lantarki tsakanin ƙasashensu da sauran ƙasashen nahiyar.

    Buƙatar ta biyo bayan katsewar wutar lantarki ne da aka yi a yankin a watan da ya gabata wanda ya jefa biranen ƙasashen biyu cikin duhu, tare da dakatar da sufurin jiragen ƙasa da kuma daƙile hanyoyin sadarwa na Intanet.

    Lisbon da Madrid sun sha zargin Faransa da hana su damar samun wutar lantarki daga sauran ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai.

  8. Za mu bincika kashe wani matashi a Oyo - Rundunar ƴansanda

    Sufeto janar na ƴan sandan Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Police/X

    Sufeto janar na ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayar da umurnin gudanar da bincike kan harbin da ya kai ga mutuwar wani matashi ɗan shekara 14 mai suna Kehinde Alade a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce a yanzu haka ana tsare da jami'in ɗan sandan da ya yi harbin.

    A safiyar jiya Talata ne rahotanni suka bayyana cewa harsashi ya kashe Alade a hanyar sa ta zuwa zana jarrabawar kammala sakandire wato WASSCE a cikin mota tare da maihaifinsa da ɗan uwansa.

    Rahotannin farko a shafukan sada zumunta sun nuna cewa harsashin ya same shi ne a lokacin da ƴan sanda suke bin wani da ake zargi da laifi.

    Sai dai a sanarwar da rundunar ƴan sandan jihar Oyo suka fitar, an yi harbin ne a lokacin da mahaifin marigayin ya karya dokar fitilan kan titi, wanda ya sa ƴan sandan sukayi zargin ko ya aikata wani laifi ne ko kuma ya sato yaran ne, wanda ya kai su ga ƙoƙarin harbin tayar motar da akayi rashin sa'a ya sami yaron da ke zaune a baya.

  9. 'Ba za mu daina yaƙi ba har sai Gaza ta koma ƙarƙashin ikon Isra'ila'

    Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a shirye yake ya kawo ƙarshen yaƙin Gaza ''ƙarƙashin matakan da za su tabbatar da tsaron Isra'ila.''

    Ya ce hakan ya haɗa da sakin mutanen da ake riƙe da su, Hamas ta ajiye makamanata, shugabannin ƙungiyar su fice daga Zirin, kuma yankin ya kasance ''babu makamai bakiɗaya.''

    A cikin wani jawabi da ya yi, ya kuma ce burin Isra'ila shi ne kawar da Hamas, kuma '' za mu cimma burinmu a ƙarshe, aikin mu bai ƙare ba'' in ji shi.

    Firaministan ya kuma ce sun ''hallaka gwamman ƴan ta'adda'' a Gaza, kuma '' wataƙil sun hallaka'' shugaban Hamas Muhammed Sinwar.

    Netanyahu ya ƙara da cewa idan akwai damar tsagaita wuta na wani lokaci da kuma yarjejeniyar sakin waɗanda ake riƙe da su, Isra'ila za ta amince.

    A cewar sa, Zirin Gaza bakiɗayansa zai kasance ƙarƙashin ikon Isra'ila a ƙarshe, kuma za su ci galaba kan Hamas.

  10. Trump ya nemi ya ƙure Ramaphosa kan kisan fararen fata ƴan Afirka ta Kudu

    Shugaba Trump da Shugaba Ramaphosa

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump ya ƙalubalanci shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da wani bidiyo da ya ce yana goyon bayan iƙirarinsa na cewa ana kashe manoma fararen fata a ƙasar, wani iƙirari da aka ƙaryata.

    Bidiyon da aka nuna a yayin tattaunawarsu a gaban ƴan jarida a fadar White House, na nuna wasu dubban kabururukan manoman da aka kashe, sai dai Mista Trump ya gaza bayyana a inda su ke.

    Trump ya kuma nuna masa wasu hotunan da a cewar sa na iyalai ne da ke jimamin mutuwar ƴan uwansu ta hanyar ziyartar maƙabarta.

    Mista Ramaphosa ya musanta zargin Trump na cewa fararen fata ƴan Afirka ta kudu na fuskantar kisan ƙare dangi, duk da dai ya amince da cewa ana yawaitar samun tashe-tashen hankula a ƙasar, ya ce abin ya fi ritsawa da baƙaƙen fata sama da fararen fata.

  11. Ina so in daidaita alaƙar Afirka ta Kudu da Amurka - Ramaphosa

    Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ce yana so ya sake daidaita alaƙar ƙasarsa da Amurka.

    Ya faɗi hakan ne a lokacin da yake ganawa da Shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House.

    A yayin tattaunawar tasu a gaban ƴan jarida, Shugaban Amurka ya bayyana Mista Ramaphosa a matsayin shugaban da ake mutuntawa wanda kuma a wasu lokutan ake kallon shi a matsayin mutum mai taƙaddama.

    Dagantaka tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami a ƴan kwanakin nan.

    Mista Trump ya sake nanata cewa fararen fata ƴan Afirka ta kudu na fuskantar ''kisan ƙare dangi'' - wani zargi da aka musanta.

    Trump ya kuma dakatar da shigar da duk wani kayan agaji Afirka ta Kudu.

    Amurka ta kuma nuna rashin jin daɗinta kan ƙarar da gwamnatin Afirka ta kudu ta shigar kotun hukunta manyan laifuka kan zargin Isra'ila da kisan ƙare dangi.

  12. An kama ɗan Birtaniya mai yawon buɗe ido a Namibiya saboda ɗaukar hotunan yara tsirara

    .

    Asalin hoton, Universal Images Group via Getty Images

    Tun da farko an zargi Douglas Robert Brook da yunƙurin yin lalata da yaran ta hanyar taɓa jikinsu a lokacin da ya ke hutu a wani gari da ke tsakiyar ƙasar ta Namibiya.

    Jami'an 'yan sanda sun ce wanda ake zargin na ƙoƙarin ganin ya yi lalata da yaran mata da maza daga a'ummar garin na San da ke yankin Otjozondjupa.

    Mutumin ɗan asalin Birtaniya mai shekara 65, na fuskantar tuhume-tuhume har 38, da suka haɗa da fyaɗe da cin zarafin yara, kamar yadda wata kafar watsa labaran Namibiya ta ruwaito.

    Sai dai Mista Douglas wanda ya je ƙasar domin yin hutu a makon da ya gabata, bai ce kome ba game da waɗannan zarge-zarge.

    An dai kama shi ne a ranar Lahadi bayan bayan an zarge shi da yaudarar yara har 34 ta hanyar ba su kuɗi da alawa domin ya ɗauki hotunansu tsirara.

    A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Lura da Muhalli da Yawon Buɗe Ido ta Namibiya ta fitar, ta ce abin da ɗan asalin Birtaniyar ya yi "cin zarafi ne ga al'adun al'ummar San".

    Ƙasar Namibiya da ke kudancin Afirka ta yi fice a ɓangaren yawon buɗe ido inda ake yawan kai ziyara ƙasar kasancewar tana da wuraren buɗ ido da suka haɗa da yankunan sahara da kuma wuraren tarihi.

  13. Sojojin Sudan sun bayar da sanarwar karɓe iko da birnin Khartoum

    Dakarun sojojin Sudan a jiya Talata, sun sanar da sake karɓe iko da ɗaukacin birnin na Khartoum daga hannun dakarun RSF.

    "A yau [20 ga Mayu] muna sanar da cewa Khartoum ya fita daga hannun 'yan ta'addan Al-Dagalo [inda suke nufin RSF] kuma mun tsaftace babban birnin ƙasarmu daga 'yan tawaye da magoya bayansu" a cewar rundunar sojojin Sudan.

    "Mun tabbatar da yanzu kam birnin Khartoum ya fita daga hannun 'yan tawaye" in ji su.

    Rundunar sojojin na Sudan sun ƙara da cewa za su fatattaki dakarun na RSF daga Sudan har sai "an tabbatar da kowane ɓangaren ƙasar ya samu 'yanci"

    A ranar 27 ga watan Maris dakarun RSF sun ce sun janye mayaƙansu daga birnin zuwa Omdurman mai maƙwabtaka da Khartoum, a wani abin da suka kira "matakin sake shiri".

    Sake kama birnin da sojojin Sudan suka yi a yanzu yana nufin sun samu cikakken iko kenan da dukan muhimman sassan ƙasar, abin da kuma ke nuna nasarar da gwamnati ke ci gaba da samu a yaƙin.

  14. Harin bom ya kashe mutum biyar a Pakistan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Jami'an Pakistan sun ce aƙalla mutum biyar ne suka mutu, wasu da dama kuma sun jikkata a wani harin bam ɗin ƙunar baƙin wake da aka kai kan motar makarantar soja a lardin Balochistan.

    Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa kusan ɗalibai arba’in ne ke cikin motar a lokacin da fashewar ta auku da safiyar ranar Laraba.

    Daga cikin waɗanda suka mutu, har da ƙananan yara uku.

    Rundunar sojin Pakistan ta zargi Indiya da kai harin, kodayake ba ta bayar da wata hujja ba.

    Babu wata ƙungiya dai da ta ɗauki alhakin kai harin zuwa yanzu.

    Lardin Balochistan na da gagarumin yawan ’yan aware, kuma sau da dama suna kai hari kan jami’an tsaro.

  15. An samu ƙaruwar zakuna a Indiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Indiya sun bayyana cewa sabuwar ƙdiddiga ta nuna ƙaruwar yawan zakunan Asiya a ƙasar da fiye da kashi 30 cikin 100 a cikin shekaru biyar da suka gabata.

    Kididdigar ta nuna cewa adadin zakunan ya ƙaru zuwa 891.

    Masu kare dabbobi sun bayyana samun ƙaruwar a matsayin sakamakon nasarar shirin kare namun daji da ake gudanarwa a ƙasar.

    A da, zakunan Asiya suna yawo daga Gabas ta Tsakiya har zuwa sassan Asiya, amma yanzu sun rage zuwa rukuni guda kacal da ke karkashin kariya a filin dajin Gir da ke jihar Gujarat a yammacin Indiya.

    Wadannan zakuna sun ɗan fi ƙaranci girma idan aka kwatanta su da zakunan Afirka. Sabuwar kididdigar adadinsu an gudanar da ita a farkon wannan wata.

    A tarihi, yawan zakunan Asiya ya faɗi matuƙa sakamakon farauta da mamayar dazuka da mutane ke yi, wanda ya sa suka ragu zuwa kusan guda 300 a shekarar 1995.

  16. 'Ƴan majalisar Najeriya na cusa kwangilolin son rai a kasafin kuɗi'

    ...

    Asalin hoton, ASIWAJU BOLA AHMED TINUBU/FACEBOOK

    Rahoton wata ƙungiya mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka (BudgIT) ya gano cewa wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya na cusa kwangiloli marasa amfani, waɗanda ba su da alfanu ga ƙasa a cikin kasafin kuɗin Najeriya.

    BudgIT ta ce ta gano kwagiloli har 11,122 wadanda za su lashe kuɗin da ya haura naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kuɗin 2025 da Majalisar ƙasa ta cusa ba tare da la’akari da cancanta ba.

    Haka nan rahoton ya bayyana cewa an cusa irin wadannan ayyuka a kasafin hukumomi da ma’aikatun gwamnati waɗanda ba su da wata alaƙa da ayyukan.

    Wasu daga cikin kwangilolin da aka lissafa sun haɗa da kwangilar bayar da tallafin karatu da rabon takin zamani da gina cibiyar koyar da kwamfuta ICT/CBT, da kuma samar da motoci don tsaro da sauransu duk da cewa babu alaƙar waɗannan kwangiloli kai tsaye da ayyukan ma’aikatun.

    BudgIT ta bayyana cewa waɗannan ƙwangiloli da aka saka cikin kasafin kuɗi sun kai kashi 12.5 cikin 100 na jimillar naira tiriliyan 54.99 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu.

    Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa irin waɗannan kwangiloli na rage tasirin amfani da kuɗin gwamnati yadda ya kamata, kuma suna rushe amana tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.

    Irin waɗannan kwangiloli da ake cusawa cikin kasafin kuɗin Najeriya sun daɗe suna faruwa tun bayan dawowar demokraɗiyya a Najeriya a 1999.

    BudgIT ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ba da muhimmanci ga gaskiya da gaskiyar lissafi a tsarin kasafin kuɗi, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen gwamnati na tafiya ne wajen ayyuka da ke amfanar da al’umma kai tsaye.

  17. An buɗe cibiyar koya wa almajirai kwamfuta a Sokoto

    ...

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da wata cibiyar bai wa almajirai da yara mata marasa zuwa makaranta ilimin kwamfuta da na sana'o'i "domin inganta rayuwarsu".

    Cibiyar wadda gwamnatin ta gina tare da tallafin asusun tallafa wa yara na duniya UNICEF, zai mayar da hankali wajen koya wa ɗaliban ilimin yadda za su yi sana'a ta amfani da fasahar zamani, ta hanyar amfani da wayoyin hannu da kuma kwamfuta.

    Manufar shirin ita ce tallafa wa tsarin bayar da ilimi ga kowa, a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

    Baya ga ilimin kwamfuta, ɗaliban za su kwashe shekara ɗaya suna samun horo a sana'o'i daban-daban da kuma ilimin rubutu da karatu.

    ...

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Sokoto na cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar yawaitar yara marasa zuwa makaranta da kuma almajirai masu gararamba a kan tituna.

    A ƙarshen shekarar 2024, gwamnatin jihar ta bayyana cewa kimanin yara 800,000 ne suka yi rajista a makarantu, lamarin da ya nuna ci gaba a ɓangaren idan aka kwatanta da shekarun baya.

    ...

    Asalin hoton, Sokoto State Government

  18. Sabon Fafaroma ya buƙaci Isr'ila ta bari a shigar da agaji Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon Fafaroma Leo ya buƙaci Isra’ila da ta ba da damar shigar da agajin jin ƙai zuwa Gaza.

    Wannan kiran ya fito ne yayin jawabinsa na farko a taron janar na mako-mako da ake gudanarwa a Dandalin St. Peter’s da ke Vatican.

    A cikin jawabin nasa, Fafaroma Leo ya kuma roƙi a kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa, yana mai cewa rikicin na ƙara tabarbarewa ne a kan yara da tsofaffi da marasa lafiya.

    Fafaroma Leo wanda aka zaɓa a ranar 8 ga Mayu, ya bayyana cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙi jagorancinsa a matsayinsa na Fafaroma.

    Tun daga fara mulkinsa, Fafaroman ya nuna damuwa da rikice-rikicen da ke ci gaba da jefa fararen hula cikin halin ƙunci, inda ya jaddada cewa ya zama wajibi a nemo mafita mai ɗorewa da gaggawa.

    Ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su tashi tsaye wajen kare rayukan mutane da samar da hanyoyin da za su kawo ƙarshen tashin hankali a yankin.

  19. Kotu ta ɗaure mutum biyar a Kano saboda awakinsu sun ci shukar gwamnati

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Kano ta yanke wa mutum biyar hukunci ɗaurin wata ɗaya ko tarar naira 25,000 kowannensu saboda awakinsu sun lalata shukokin gwamnati a gefen titunan Lodge Road da Race Course Road da ke tsakiyar birnin.

    Haka kuma kotun ta umarci mutanen su biya naira 100,000 jimilla, a matsayin diyya kan barnar da awakin nasu suka yi.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ma’aikatar muhallin jihar ce ta kai mutanen kotu a wani yunƙuri na kare dukiyoyin gwamnati da kuma kiyaye tsaftar birnin.

    Lauyar gwamnati, Barista Bahijjah H. Aliyu, ta bayyana wa kotu cewa waɗanda ake tuhuma sun karya dokar Lafiyar Jama’ar jihar ta 2019, wadda ta haramta hakan da kuma haddasa ɓarna ga muhalli ko dukiyar gwamnati.

    Sanarwar ta ce shukar da aka lalata na cikin wani shiri da gwamnatin jihar ke yi na ƙawata birnin Kano da kuma inganta lafiyar iskar da al'ummar birin ke shaƙa.

    "Kotun ta samu waɗanda aka gurfanar ɗin da laifin sakaci da ɓarna ga dukiyar jama’a." in ji sanarwar.

  20. Harin Rasha da makami mai linzami ya kashe sojoji shida a Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Russian MOD

    Harin makami mai linzami da Rasha ta kai a wurin sansanin atisayen sojoji a yankin iyakar Sumy da ke Ukraine ya yi sanadin mutuwar sojoji shida tare da jikkata fiye da goma, in ji rundunar tsaron cikin gida ta Ukraine.

    A baya dai ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar da bidiyo da take iƙirarin na nuna harin makamin Iskander da aka kai wani sansanin horo, inda kamfanin dillancin labarai na Rasha, Tass, ya ruwaito cewa mutane har 70 ne suka mutu a harin.

    Yankin Sumy ya daɗe yana fuskantar hare-hare daga Rasha, kuma daga wannan yanki ne Ukraine ta ƙaddamar da mamayar wata ƙasa a gundumar Kursk da ke makwabtaka da ita a Rasha, har na tsawon watanni.

    Rundunar tsaron cikin gida ta Ukraine ta tabbatar da faruwar harin a safiyar Laraba, inda ta ce lamarin ya faru ne yayin da dakarunta ke gudanar da atisaye a filin harbi.

    Ta ƙara da cewa an dakatar da kwamandan da ke jagorantar atisayen tare da buɗe bincike na hukuma kan lamarin.