Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Ambaliya ta kashe yara biyu, ta raba 1,000 da muhallansu a Kafanchan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata mummunar ambaliyar ruwa ta raba mutane sama da 1,000 da muhallansu tare da hallaka yara biyu a Kafanchan da ke cikin ƙaramar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

    Misis Christy Usman, mataimakiyar shugabar ƙaramar hukumar Jema’a ce ta bayyana hakan, a wata ziyara da kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa domin nazari kan tasirin ambaliyar.

    Ta ce ambaliyar wadda ta shafi "wasu sassan garin Kafanchan da Jagindi da Atuku da Aso da kuma Bade ta lalata gonaki da dama da kuma amfanin gona da darajarsu takai miliyoyin naira."

    "Ambaliyar ta yi illa ga tattalin arzikin ƙaramar hukumar Jema’a, amma Gwamnatin jihar ta dauki mataki cikin gaggawa."

  2. Mutanen da suka mutu a hari kan kasuwa a Sudan sun kai 40

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin waɗanda suka mutu a wani harin atilari kan wata kasuwa a garin Sennar na Sudan, ya kai mutum 40, a daidai lokacin da ake fargabar alkaluman za su iya ƙaruwa.

    Ana dai zargin dakarun RSF da kai harin a garin da ke kudu maso gabashin ƙasar, kamar yadda jaridar Sudan Tribune ta ruwaito.

    Wata ƙungiyar likitoci ta bayyana a ranar Lahadi cewa dakarun na RSF sun kashe fararen hula 21 da kuma jikkata wasu 70 bayan ruwan bama-bamai da ta yi a kasuwar mai cike da cunkoso.

    Harin ya zo ne jim kaɗan bayan da sojojin ƙasar suka kai hare-hare ta sama kan wuraren RSF a kudanci da kuma yammacin garin Sennar da kuma kusa da birnin Al-Suki.

    Mutane da dama dai sun yi Alla-wadai da harin, inda jam'iyyar Sudanese Congress Party ta ci gaba da far wa fararen hula da dakarun RSF ke yi, yana a matsayin laifukan yaƙi.

    Lauyoyi da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam, sun kwatanta farmakin a matsayin saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, inda suka yi kiran gudanar da bincike mai zaman kansa.

    A watannin baya-bayan nan, dakarun RSF sun tsananta kai harin makaman atilari kan yankunan fararen hula a kuma biranen da sojojin gwamnati ke iko da su da suka haɗa da Omdurman, al-Fashir da Sennar, tare da kashe gomman fararen hula.

  3. Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yari a Laberiya

    ...

    Asalin hoton, Glenna Gordon/Amnesty International

    Ma'aikatar shari'a ta ƙasar Liberiya, fursunoni 47 ne suka tsere daga gidan yari sakamakon taɓarɓarewar tsaro da aka samu.

    Ma'aikatar ta yi kira ga 'yan ƙasar da su taimaka wa jami'an tsaro ta hanyar bayar da duk wani bayani da zai kai ga gano fursunonin da suka tsere.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta nuna matuƙar damuwarta kan lamarin tare da ba da tabbacin ɗaukar dukkan matakan da suka dace don ganin an sake kama fursunonin.

    Sai dai wata kafar yaɗa labarai ta Front Page Africa ta ruwaito cewa adadin waɗanda suka tsere daga gidajen yarin sun kai sama da 100.

    An fasa gidan yarin Kakata da ke gundumar Margibi, da ke arewa ta tsakiyar ƙasar a ranar Lahadin da ta wuce.

    Wani shaida da ke zaune kusa da gidan yarin ya bayyana lamarin a matsayin rikici, inda ya ce an ga gungun mutane da dama suna ta gudu ta cikin unguwar Carter high.

    Ya ƙara da cewa mazauna yankin sun yi yunƙurin kama mutanen da ke gudu amma suka kasa saboda yawansu.

    Kwamandan 'yan sandan gundumar Margibi, Patrick Kormazu ya tabbatar da cewa hukumomi na ci gaba da neman fursunonin.

    Ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar ba su duk wani bayani da zai taimaka wajen sake kama fursunonin.

  4. Tsohon saurayin 'yar wasan Olympics da ya cinna mata wuta shi ma ya mutu

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Tsohon saurayin 'yar wasan Olympics ta Uganda, Rebecca Cheptegei, wanda ya cinna mata wuta, shi ma ya mutu bayan kunar da ya samu a lokacin da ya kai mata hari.

    Tsohon saurayin, Dickson Ndiema ya zuba mata fetur ne ya ƙona ta bayan da ta koma gida daga coci a makon da ya gabata.

    Rahotanni sun ce ƴar wasan da tsohon saurayin nata sun kasance suna rikici kan wani ɗan karamin fili da ke arewa maso yammacin Kenya, inda take zaune.

    Ndiema ya mutu ne a daren ranar Litinin a sashin kula da lafiya da ke Moi Teaching and Referral Hospital, inda aka kwantar.

  5. Jarumin fina-finai James Earl Jones ya rasu

    James Earl Jones

    Asalin hoton, Getty Images

    Jarumin fina-finan Amurka James Earl Jones, ya rasu yana da shekara 93.

    Ya mutu a gaban iyalansa a safiyar ranar Litinin, kamar yadda wakilinsa Barry McPherson ya bayyana.

    Jones ya fito a cikin dubban fina-finai da suka haɗa da Field of Dreams, Coming To America, Conan the Barbarian da kuma The Lion King.

    An fi saninsa a fim ɗin Star Wars, saboda yadda ya yi amfani da salo na muryarsa a cikinsa.

    Lokacin rayuwarsa, Jones ya lashe kyautuka da ake bai wa gwarazan jarumai har sau uku da suka haɗa da na Emmy guda biyu da kuma Grammy ɗaya, da kuma kyautar Oscars ta girmamawa a 2011 saboda irin nasarar da ya samu a rayuwarsa ta fim.

    A shekarar 1971, ya zama bakin fata na biyu da aka taɓa saka sunansa cikin jerin gwarazan jarumai, bayan Sidney Poitier.

  6. Ƙungiyar IS ta 'kafa tsauraran dokoki' a yankin yammacin Nijar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar IS ta kafa tsauraran dokoki kan mata da 'yan mata a yammacin jamhuriyar Nijar, bayan da suka karɓe iko da yankunan karkarar Abala.

    Rahotonni sun bayyana cewa kungiyar IS ta umarci mata da ‘yan mata a yankin su sanya baƙaƙen tufafi sannan kuma ta haramta mu’amala tsakanin maza da mata marasa aure.

    Kungiyar IS dai ta ƙwace Abala jim kaɗan bayan janyewar sojojin Faransa da na Amurka, wanda ya biyo bayan juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi a shekarar 2023

    Abala dai na cikin yankin Tillaberi mai fama da tashin hankali a yankin kan iyaka tsakanin Nijar da Burkina Faso da kuma Mali, wanda ya zama tungar 'yan ta'adda a shekarun baya-bayan nan.

    Jamhuriyar Nijar dai na samun ƙaruwar hare-haren ta'addanci tun bayan hamɓarar da shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi a shekara ta 2023, bayan ficewar Faransa da wasu sojojin ƙasashen yamma.

  7. Ƴan majalisa sun gayyaci shugaban jami'ar Dutsin-Ma kan 'rashin iya shugabanci'

    ...

    Asalin hoton, FUDMA Website

    Kwamitin majalisar wakilai da ke kula da korafe-korafen jama'a ta gayyaci shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Armayau Hamisu Bichi da ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi kan zargin 'rashin iya jagoranci' da ake yi masa.

    Gayyatar tasa ta biyo ne bayan wani mai suna Shehu Abubakar Tadda ya shigar da korafi kan yadda Farfesa Bichi yake tafiyar da salon shugabancinsa wanda bai dace ba, a cewarsa.

    Kwamitin ya buƙaci shugaban jami'ar da ya bayyana gabansa a ranar Laraba 18 ga watan Satumban 2024.

    Sanarwar ta ce ko da bai bayyana gaban kwamitin ba, za a iya ci gaba da sauraron batun a bayansa.

    Majalisar wakilan ta ce gayyatar na a sashe na 88 da kuma 89 na kundin mulkin Najeriya, wanda ya ba ta damar bincike kan batutuwa da suka shafi al'umma.

    Haka kuma, majalisar ta buƙaci wanda ya shigar da korafin Shehu Abubakar Tadda da shi ma ya bayyana gabanta.

  8. Ambaliya ta ɗaiɗaita dubban mutane a Maiduguri

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ambaliyar ruwa ta tilasta wa dubban mutane barin muhallansu a Maidguri, babban birnin jihar Borno.

    Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da madatsar ruwa ta Alau ta ɓalle, bayan cikar da ta yi tsawon mako ɗaya.

    Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Farfesa Usman Tar ya fitar a safiyar yau Talata, ya yi kira ga mutane da su gaggauta tashi daga wajen da lamarin ya faru.

    Ya ce "Sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu a wannan shekara, muna kira ga mutanen da ke zaune kusa da koguna da su tashi nan take domin kare kansu da kuma dukiyoyinsu.

    Tituna da dama dai sun cika da ruwa wanda hakan ya janyo wahala wajen zirga-zirgar ababen hawa.

    Ambaliya

    Asalin hoton, ....

  9. Mun bi ka'ida wajen mamaye ofishin SERAP - DSS

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa jami’anta suka mamaye ofishin ƙungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin ƙasa (SERAP) a Abuja ranar Litinin.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Talata a shafinta na intanet, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa jami’anta sun kai farmaki ofishin SERAP, inda ta ce ziyarar wani ɓangare ne na bincike da ta saba yi.

    DSS ɗin ta jaddada cewa ba daidai ba ne misalta abin da jami’an suka yi a matsayin cin zarafi da kuma tsoratarwa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta cika da tambayoyi da dama dangane da mamaye ofisoshin SERAP da ke Abuja da Legas ba bisa ka’ida ba."

    “Waɗannan bayanan duk ba haka bane ne, kuma idan dai za a iya tunawa, an aike da wata tawaga ta ma’aikatanmu guda biyu bisa doka domin gudanar da bincike na yau da kullum a ofishin SERAP da ke Abuja."

    "Abin takaicin shi ne yadda aka yi kuskuren fassara wannan a matsayin hari da cin zarafi, da kuma tursasa wa jami’an SERAP ba bisa ƙa’ida ba." in ji sanarwar.

    Hukumar ta DSS dai ta buƙaci jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotannin da ba su tushe.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barkanmu da warhaka. Da fatan mun wayi gari a wannan rana ta Talata.

    Kamar yadda muka saba, za mu kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Instagram inda a nan ma akwai ƙarin labaran da za ku iya karantawa har ma da bidiyo da za ku iya kalla.