'EFCC ta sallami Abubukar Malami bayan yi masa tambayoyi'

Asalin hoton, Abubakar Malami, SAN
Tsohon Ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, SAN ya ce hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci ta sallame shi bayan ya amsa wasu tambayoyi da hukumar ta gayyace shi domin samun amsarsu.
Cikin wata saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jim kaɗan bayan fitowa daga ofishin hukumar, Malami ya ce yana gode wa Allah da ya ba shi ikon kammala amsa tambayoyin hukumar lafiya.
Tsohon ministan shari'ar ya kuma ce ganawar tasa da jami'an EFCCn ta kasance mai kyau.
Sai dai ya ce hukumar ta sake sanya wani lokaci domin ya sake halarta ofishinta domin ci gaba da ganawar.

