Majalisar Ɗinkin Duniya ya fito da manhajar da za ta magance matsalar ƙarancin Abinci

Asalin hoton, Getty Images
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFO ya ƙaddamar da wani shafi da ke amfani da fasahar AI, domin ganowa da kuma magance matsalar yunwa a fadin sama da kasashe 50.
Babbar Darektar hukumar, Cindy McCain, ta ce shafin, mai suna HungerMap Live - zai rika samar da bayanai kai tsaye a lokacin da abubuwa ke faruwa, tare da bayar da hasashe, da nufin ingantawa da kuma hanzarta ayyukan samar da abinci.
Hukumar da ke fitar da bayanai kan wuraren da aka fi fama da yunwa ta duniya, IPC, ta ce an ƙaddamar da shafin a kan gaɓa - kasancewar an yi ne a daidai lokacin da aka samu karuwar matsalar ƙarancin abinci sosai a duniya, inda aka samu alkaluman da ba a taɓa samu ba na yawan mutanen da ke fama da yunwa a shekarun nan.




