Shugaban Dimokuradiyyar Kongo ya zargi wanda ya gada da goyon bayan ƴantawaye

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya zargi wanda ya gada Joseph Kabila, da goyon bayan ƴantawaye a gabashin kasar.
A wata hira, Felix Tshisekedi ya zargi tsohon shugaban wanda ya kaurace wa zaben bara da shirin tayar da kayar baya.
Ya yi wannan ikirarin ne bayan ƴantawayen M23 sun kwace ikon wani gari da ke kusa da kan iyaka da Uganda jim kadan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da sojojin Kongo ta soma aiki.
Ita dai jam'iyyar Mista Kabila, People's Party for Reconstruction and Democracy, ta yi watsi da zargin.
Duk da kokarin shiga tsakani da ake yi, rikici a yankin gabashi mai arzikin mai na ci gaba da kamari.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan bakwai aka raba da mahallansu sakamakon rikicin na fiye da shekara 10.



