Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai tsaye nan za mu gintse labarai da rahotonnin da muke kawo muku.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Iran ta jaddada cewa za ta mayar da martani kan kisan jagoran Hamas

    Muƙaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa ƙasar za ta mayar da martani kan kisan jagoran Hamas Isma'il Haniyeh a lokacin da ya dace.

    Cikin wata sanarwa, jami'in ya zargi Amurka da hannu a kisan gillar da aka yi wa Haniyeh.

    Iran da Hamas sun zargi Isra'ila da aiwatar da kisan, sai dai Isra'ilar ba ta tabbatar da hakan ba.

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya shaida wa takwaransa na Iran cewa ya zama dole a kawo ƙarshen ramuwar gayyar da ake.

  3. 'Yansanda sun kama ƙarin mutum 25 kan zargin saɓa dokar taƙaita zirga-zirga a Jos

    'Yansanda

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya a jihar Filato ta ce ta kama ƙarin mutum 25 bisa zargin saɓa wa dokar taƙaita zirga-zirga da aka sanya a Jos, babban binrin jihar.

    Kakakin rundunar 'yansandan jihar, Alabo Alfred, ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito.

    A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar ta sanya doƙar taƙaita zirga-zirga a birnin domin hana ɓata-gari shiga cikin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa domin aikata ɓarna.

    Mista Alfred ya kuma yaba wa matasan birnin bisa yin biyayya ga dokar da gwamnatin jihar ta sanya.

    Sai dai ya koka kan yadda wasu suka bijire wa dokar, waɗanda ya zarga da fitowa daga gidajensu suna farmakar jami'an tsaro a kasuwar Yen Tire da sauran wurare a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

  4. Rundunar sojin Sudan za ta mayar da shalkwatarta Omdurman

    .../

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin Sudan ta ce shugabanta, Janar Abdel Fattah al-Burhan zai mayar da matsugunin hedikwatarta zuwa Omdurman kusa da Khartoum, babban birnin ƙasar bayan nasarorin da aka samu a yaƙin basasa.

    Wata sanarwa daga babban jami'in sojin ƙasar, ta ce nan ba da jimawa ba ne janar ɗin zai jagoranci dakarunsa zuwa hedikwatar.

    A faron makon nan ne sojoji suka nausa Omdurman bayan kai hare-hare kan wuraren da ke ƙarƙashin ikon dakarun RSF.

    Janar al-Burhan yana zama ne a Port Sudan, tun bayan barin birnin Khartoum lokacin da yaƙi ya ta'azzara shekara ɗaya da ta gabata.

    Idan Janar Burhan ya mayar da matsugunin hedikwatar zuwa birnin, hakan zai nuna ƙarfin ikon sojoji a yankin.

  5. WHO za ta aike da alluran riga-kafin shan inna miliyan 1.2 zuwa Gaza

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wasu daga cikin Falasɗinawan da yaƙi ya ɗaiɗaita na zaune cikin tantunan da suka kafa a kusa da ruwan ba-haya.

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce za ta aike alluran riga-kafin cutar polio sama da miliyan ɗaya zuwa Gaza domin ɗigawa mutane sakamakon gurɓacewar muhalli a yankin.

    A watan da ya gabata ne aka gano ƙwayar cutar shan inna a magudanar ba-haya a Gaza - alamar da ke nuna cewa ƙwayar cutar na yaɗuwa.

    Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai haɗarin kamuwa da cututtuka sannan adadin waɗanda aka yi wa riga-kafin cutar shan inna a Gaza ya ragu sosai tun lokacin da Isra'ila ta soma kai hare-hare a yankin.

    WHO ta ce tana ci gaba da neman izini a kowane mataki don yi wa mutane riga-kafi da take fatan farawa ranar 17 ga watan Agusta.

  6. Ukraine ta ƙaddamar da kutse cikin Rasha a rana ta biyu

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ukraine ta ci gaba da kai hare-hare zuwa yankin Kursk na kan iyakarta da Rasha a rana ta biyu.

    Gwamnan yankin Kursk a Rasha, Alexey Smirnov, ya ayyana dokar ta-ɓaci sakamakon kutsen da Rasha ke zargin sojojin Ukraine da yi mata.

    Mista Smirnov ya kira lamarin 'mai sarƙaƙiya'

    Tun da farko shugaban Rasha, Vladimir Putin ya zargi Ukraine da abin da ya kira ''ƙarin takalar faɗa'', bayan da jami'an tsaron Rasha suka ce sojojin Ukraine sun kutsa yankin Kursk a ranar Talata.

    Rasha ta ce sojojin na Ukraine cikin tankokin yaƙi 11 da motocin sulke fiye da 20 sun tsallaka kan iyaka zuwa kusa da garin Sudzha, mai nisan kilomita 10 daga filin daga.

    Cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin, Babban hafsan tsaron Rasha, Janar Valery Gerasimov ya shaida wa Shugaba Putin cewa sojojin Rasha sun dakatar da ''dannawar dakarun na Ukraine zuwa yankin, bayan da suka kai hari don lalata wasu ababen hawa da makaman nasu a kusa da kan iyakokin ƙasashen biyu.

    Wannan hari ka iya zama ɗaya daga cikin hari mafi ban mamaki da Ukraine da kai yankunan Rasha, tun bayan mamayar da Moscow ta yi wa ƙasar cikin watan Fabrairun 2022.

  7. Ya kamata gwamnatin tarayya ta gane manufofinta ba sa aiki - Gwamnan Bauchi

    Bala Mohammed

    Asalin hoton, Bala Mohammed /X

    Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce yana da kyau gwamnatin tarayyata ta fahimci cewa shirye-shirye ko ƙudurorin da take ɓullo da su ba sa aiki.

    Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam'iyyar PDP a zaɓen ƙananan hukumomin jihar, Gwamna Bala ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta daina fakewa da bai wa 'yan Najeriya uzuri.

    “Manufofin gwamnatin tarayya ba sa aiki. Ya kamata su fahimta cewa matsalarsu da shirye-shiryensu ne ke haddasa matsalolin da ake ciki a ƙasar nan, don haka ya kamata su canja.''

    Gwamnan ya kuma ce jawabin da shugaban ƙasar ya yi a ƙarshen makon da ya gabata, fankon jawabi ne da babu wani abin ɗauka a cikinsa.

    A ranar Lahadi ne dai shugaba Tinubu ya yi wa al'ummar ƙasar jawabi, inda a ciki ya yi kira ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar su jingine ƙudurin nasu tare da rungumar hanyoyin tattaunawa.

    To sai dai gwamnan na Bauchi ya ce ''Na saurari duka jawabin shugaban ƙasar cikin nutsuwa da kunnen basira, amma babu komai a cikin a jawabin nasa,''.

    “Bai amince da yanayin da ake ciki ba, bai magance abubuwan da suka haifar da matsalolin ba. Matsalolin ba nasa ba ne shi kaɗai, namu ne duka shugabanni kama daga fadar shugaban ƙasar zuwa jihohi da ƙananan hukumomi''.

  8. Putin ya zargi Ukraine da 'takalar faɗa' kan zargin kutsen kan iyaka

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya zargi Ukraine da abin da ya kira ''ƙarin takalar faɗa'', bayan da jami'an tsaron Rasha suka ce sojojin Ukraine sun kutsa yankin Kursk a ranar Talata.

    Rasha ta ce sojojin na Ukraine cikin tankokin yaƙi 11 da motocin sulke fiye da 20 sun tsallaka kan iyaka zuwa kusa da garin Sudzha, mai nisan kilomita 10 daga filin daga.

    Cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin, Babban hafsan tsaron Rasha, Janar Valery Gerasimov ya shaida wa Shugaba Putin cewa sojojin Rasha sun dakatar da ''dannawar dakarun na Ukraine zuwa yankin, bayan da suka kai hari don lalata wasu ababen hawa da makaman nasu a kusa da kan iyakokin ƙasashen biyu.

    Mista Gerasimov ya ƙara da cewa dakarun Ukraine kusan 1,000 ne suka shiga yankin da nufin ƙwace iko da garin Sudzha, yayin da sojojin Rasha suka kashe aƙalla sojojin 100, tare da jikkata wasu 215.

    Kawo yazu dai Ukraine ba ta ce komai ba game da batun.

  9. Afirka ta Kudu za ta aiwatar da dokar inshora mai cike da taƙaddama

    Shugaban afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ce gwamnatin ƙasar za ta aiwatar da dokar nan ta inshorar lafiya mai cike da taƙaddama wadda ke neman yi wa ɓangaren lafiyar ƙasar garambawul.

    Dokar inshorar lafiyar ƙasar na neman bai wa duk ƴan Afirka ta Kudu kulawa ƙarƙashin asusun ƙasa.

    An amince da dokar gabanin babban zaɓen watan Mayu kafin jam'iyyar ANC ta rasa rinjayenta a majalisar dokokin ƙasar.

    Sai dai dokar na iya fuskantar ƙalubale har daga jam'iyyar Democratic Alliance game da kuɗin da aka kashe wa shirin.

  10. Ambaliya ta kashe mutum 32 tare da jikkata 100 a Sudan

    ...

    Sudan ta ce aƙalla mutum 32 ne suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da ya janyo mummunar ambaliya a sassan ƙasar da dama.

    Jaridar Tribune a Paris ta ruwaito cewa mutum 100 suka jikkata sakamakon ambaliyar.

    Jaridar ta kuma ruwaito wani babban jami'in ma'aikar lafiya da cewa gidaje 5,575 ne suka lalace a jihohi bakwai na ƙasar da ambaliyar ruwan ta shafa.

    Jami'in ya ce "Wannan lamarin ya ƙara yiwuwar kamuwa da cutar amai da gudawa, inda aka tabbatar da cewa mutum 100 a garuruwan Kassala da Khartoum da kumaGezira sun kamu da cutar''.

    A shekarun baya-bayanan, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliya sun yi sanadin mutuwar ɗarurruwan mutane da kuma lalata dubban gidaje da gonaki a Sudan.

    Ƙasar Sudan dai ta kasance tana fafatawa da dakarun RSF tun watan Afrilun 2023.

  11. Najeriya ta kama 'yanƙasar Poland bakwai a Kano kan ɗaga tutar Rasha a zanga-zanga

    Zanga-zanga

    Asalin hoton, Social Media

    Jami'an tsaro a Najeriya sun kama 'yan ƙasar Poland bakwai bisa zargin ɗaga tutocin Rasha yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

    Kakakin rundunar tsaron farin kaya, Peter Afunanya, ya faɗa yayin taron manema labarai a yau Laraba cewa sun kama su ne lokacin da jami'ansu ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro.

    Sai dai bai yi ƙarin bayani ba game da ko su wane ne, yana mai cewa amma ba farautar 'yan ƙasar ta Poland a Najeriya suke yi ba.

    Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito jakadan Poland a Najeriya, Stanislaw Gulinski, yana tabbatar da kamen yayin ganawar da jakadu suka yi da gwamnatin Najeriya ranar Laraba a Abuja.

    "An kama su kwana biyu da suka wuce a Kano, abu na ƙarshe da na ji shi ne ana shirin kawo su Abuja a jirgi," in ji shi.

    Sai dai ya ƙi yin ƙarin bayani lokacin da Reuters ya tuntuɓe shi.

  12. Kotu ta ɗaure masu tarzomar ƙyamar baƙi a Birtaniya

    "yansanda da masu zanga-zanga a Birtaniya

    Asalin hoton, PA Media

    Wata kotu a Birtaniya ta yanke hukuncin ɗauri kan wasu mutane da aka samu da laifin tayar da tarzoma tun zanga-zangar da ta ɓarke sama da mako ɗaya.

    An yanke wa mutanen uku hukuncin shekara uku a gidan yari saboda shiga zanga-zangar a Liverpool.

    Wannan ne matakin yanke hukunci cikin hanzari wanda gwamnati take son ya zama darasi, ya kuma daƙile yiwuwar tashin hankali a gaba.

    Rikicin na ƙin jinin ƴan ci-rani ko baƙi shi ne mafi muni da ya bazu zuwa sassan Ingila da arewacin Ireland.

    An kama kimanin mutum ɗari huɗu a garuruwa da dama.

  13. An haramta jam'iyya mai rinjaye a majalisar dokoki a Thailand

    Matashin shugaban jam'iyyar Move Forward Pita Limjaroenrat

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An haramta wa matashin shugaban jam'iyyar MF, Pita Limjaroenrat shiga siyasa shekara 10

    Kotun tsarin mulki a Thailand ta bayar da umarnin rushe wata jam'iyyar siyasa da ta yi nasarar samun kujeru mafiya yawa a majalisar dokokin ƙasar a babban zaɓen da aka yi bara.

    Kotun ta ce shawarar da jam'iyyar Move Forward Party ta bayar ta neman a gyara haramcin da aka ƙaƙaba kan duk wanda ya soki masarauta, dai-dai take da kifar da gwamnati.

    Jam'iyyar MFP na riƙe da kashi ɗaya bisa uku na kujerun majalisar dokokin Thailand sai dai jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi da wadda ke samun goyon bayan sojoji sun hana ta kafa gwamnati.

    Shugabannin jam'iyyar su ma an haramta musu shiga harkokin siyasa tsawon shekara 10 har da jagoran jam'iyyar ta MFP, mai kwarjini, Pita Limjaroenrat.

    Ana sa ran sauran jam'iyyu su sake shiri don kafa sabuwar jam'iyya kamar yadda suka yi da jam'iyyarsu ta baya da aka rushe ta a 2020.

  14. Hukumomin Iran na binciken ’yansanda kan amfani da karfi fiye da kima lokacin zanga-zanga

    Zanga-zanga a Iran

    Asalin hoton, Twitter

    Hukumomin Iran sun ce an soma bincike kan zargin ƴansanda da amfani da ƙarfi kan yarinya ƴar shekara 14 saboda rashin saka hijab yadda ya kamata ba.

    Wani bidiyo da ke nuna abin da ya faru ya fusata mutane da dama.

    A cewar wata sanarwa daga ƴansanda, jami'ansu sun gamu da fushin jama'a lokacin da suka gargaɗi ƴan mata biyu kan yanayin shigarsu a Tehran.

    Ƴan sanda sun ce ɗaya daga cikin ƴan matan ta ƙi yadda a kama ta, lamarin da ya sa ta samu ɗan rauni. Sai dai mahaifyarta ta ce ƴarta ta ji rauni sosai.

    Mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun Hisbah shekara biyu baya ta janyo gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati a sassan Iran.

  15. Sanata Ndume ya ce ya ba wa jam'iyyar APC haƙuri

    Sanata Ali Mohammed Ndume

    Sanata Mohammed Ali Ndume ya nuna nadama tare da bayar da hakuri kan sukar da ya fito fili ya yi a kan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma kasar Bola Ahmed Tinubu.

    Sai dai a hirarsa da BBC, Sanatan ya ce sun nemi afuwar juna ne shi da jam'iyyarsa ta APC wadda ta ba da umarnin cire shi daga mukamin mai tsawatarwa a majalisar dattawa a watan jiya.

    Ndume ya ce sun yi wata ganawa a jiya Talata da shugabannin jam'iyyar kuma ya nemi afuwa game da kalaman sukar da ya yi a kafafen yada labarai maimakon gabatar da koken nasa ga jam'iyyar.

    Ya ce shi ma an ba shi hakuri kan abin da aka yi mishi ba tare da an gayyace shi ba, domin ji daga wajenshi.

    Sai dai kuma Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu, ya ce har yanzu yana nan kan bakansa na magnaganun da ya yi domin magana ce da ya yi ta gaskiya, kuma saboda kishin kasa ba don wani abu na daban ba.

    Sanatan ya ce akwai jam'iyyu kamar PDP ta SDP da wasu da suka fara zawarcinsa domin ya koma can domin ya yi musu takara a zaben 2027, saboda a cewarsa sun ga ba a mishi adalci ba dangane da abin da aka yi masa a APC.

    To amma ya ce ai, ''mutum ba zai bar gidansa ya tafi wani waje ba.''

    Dangane da tsohon mukamin nasa kuwa an ruwaito shugaban jami'iyyar ta APC Abdullahi Umar Ganduje na cewa za su rubuta wa majalisar dattawa kan ta sake duba maganar ta Ndume da nufin mayar masa da mukamin idan ta ga hakan zai yiwu.

  16. 'Maƙwabtan ƙasashe ne ke sa Najeriya kashe ɗimbin kuɗi a tallafin mai'

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu

    Ministan kudi da tattalin arziki na Najeriya Mista Wale Edun, ya ce kasar na kashe dimbin kudin da ya kai dala miliyan 600, kwakwankwacin sama da naira biliyan 956.370 a duk wata wajen siyo mai daga waje saboda makwabtan kasashe na cin moriyar man na Najeriya.

    Ministan ya ce kasashen da ke amfani da man da Najeriyar ke siyowa daga waje ba wai makwabtanta ba ne na kusa har ma zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato Santa Afirka.

    Ya ce, ''ba Najeriya kadai muke sayo wa ba, muna saya wa kasashe ta gabas, har zuwa Afirka ta Tsakiya. Muna saya wa kasashe na arewa, muna saya wa kasashe na yamma.

    Saboda haka dole ne mu tsaya mu tambayi kanmu, har zuwa yaushe za mu ci gaba da yin haka, to wannan shi ne muhimmin abu da ya shafi tattalin arzikinmu.''

    Mista Edun wanda ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na AIT, ya kara da cewa wannan shi ne ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin mai, saboda Najeriya ba ta san ainahin adadin man da take amfani da shi ba a cikin gida.

    Ministan ya ce wannan shi ya sa dole Najeriya ta dauki tsattsauran mtaki kan matsalar saboda tana hana bunkasar tattalin arzikin kasar.

    Hukumar kididdiga ta kasar ta ce, yawan man da kasar ke shigowa da shi daga waje ya ragu zuwa kusan lita biliyan daya a wata bayan da Tinubu ya cire tallafin man, ranar 29 ga watan Mayu na bara.

  17. Daga mako mai zuwa za a dakatar da karbar haraji kan shigo da kayan abinci - Kwastan

    Shugaban Kwastan Bashir Adeniyi

    Asalin hoton, X/CustomsNG

    Gwamnatin Najeriya ta ce daga mako mai zuwa ne za a fara aiwatar da umarnin da ta bayar na dakatar da karbar haraji a kan kayayyakin abinci da ake shigar da su kasar daga waje.

    Tun a watan Yuli ne gwamnatin ta sanar da cewa ta amince da wa'adin kwana 150 na shigar da masara da shinkafa da alkama daga waje ba tare da biyan haraji ba, domin magance matsalar tsadar kayan abinci a kasar, to amma har yanzu ba a ga hakan ba, inda 'yan kasuwa ke korafi da cewa ba su gani a kasa ba.

    To amma da yake jawabi a lokacin taron shugabannin hukumomin tsaro na kasar da aka yi jiya Talata a Abuja, shugaban hukumar hana fasa kwauri, Bashir Adeniyi, ya ce za a fara aiwatar da shirin da zarar an kammala tsara ka'idojin da aka shimfida.

    Ya ce: “Ana fayyace ka'idojin a ma'aikatar kudi, kuma ina tabbatar muku cewa zuwa mako mai zuwa, za a kammala fitar da ka'idojin...''

    Ya ce an samu jinkirin aiwatar da tsarin ne domin ganin an yi laka'ari da yadda zai amfani dukkanin masu ruwa da tsaki da suka hada da manoma.

    Shugaban na kwastan ya ce tuni ma wasu daga cikin kayan abin sun riga sun shigo kasar, kuma za a fitar da su ba tare da biyan haraji ko kudin fito ba.

  18. 'Ba ma jin daɗi idan maza na kallonmu lokacin shayar da yara nono'

    Wata mata na shayar da jaririnta

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce rashin isasshen nonon uwa ga jarirai na haddasa mutuwar yara sama da dubu 800, a duk shekara, kuma hakan na kara barazanar kamuwa da cututtuka na dogon lokaci.

    A yayin da a yau Laraba ake kammala makon shayar da yara nonon uwa na duniya, BBC ta tattauna da wata uwa take shayarwa a Abuja.

    Matar ta shaida wa BBC irin kalubalen da take fuskanta a lokacin shayar da jaririyarta, idan ta bar gida.

    Ta ce a duk lokacin da jaririyar take jin yunwa sai ta kebe domin ba ta nono, to amma duk da cewa tana sanye da hijabi da take lullube jaririyar ta shayar da ita, sai ta ga wasu maza na zura mata ido, wanda hakan ya sa ba ta jin dadi.

    Matar da ƙara da cewa hatta wasu matan ma kan yi mata magana cewa, ''ke ba kya ganin yadda ake kallonki kina ba ta nono?'' duk dacewa ta rufe jaririyar da hijabi.

    Haka kuma ta ce tana fuskantar kalubalen gudanar da ayyukanta na gida da kuma shayarwa, inda a wani lokacin jaririyar na bukatar nono amma ita kuma ayyuka sun yi mata yawa.

    Matar ta ce idan da za ta samu damar daukar 'yar aiki hakan zai rage mata dawainiya.

    Sannan ta bukaci jama'a da idan sun ga mace tana shayar da jariri a titi ko wani waje su rika tallafa mata a matsayin uwa domin abu ne da ya kama dole saboda yaro na jin yunwa, maimakon su riga tsangwamarta.

  19. Ɗan hamayya zai jagoranci gwamnatin riƙon-ƙwarya a Bangladesh

    Muhammad Yunus

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin dalibai za su gana da jam'iyyun siyasa a Bangladesh a yau, Laraba, domin tattaunawa kan kafa gwamntin rikon-kwarya bayan hambarar da gwamnatin Firaminista Sheikh Hasina, ranar Litinin.

    Muhammad Yunus, mai shekara 84, mai sukar Sheik Hasina, wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel kuma masanin tattalin arziki, shi ne zai zama shugaban wucin-gadi.

    An sauya shugaban 'yan sandan kasar cikin dare kuma babu jami'an 'yansanda a titunan babban birnin kasar.

    Ana ci gaba da samun rahotannin tashin hankali da kuma kwasar kayan mutane a Dhaka.

  20. Zanga-zanga: Sojojin Najeriya sun nuna nadama kan kisan matashi a Zaria

    Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

    Asalin hoton, X/HQNigerianArmy

    Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta nuna nadamarta kan yadda wani sojanta ya kashe wani daga cikin masu zanga-zanga a unguwar Samaru da ke Zaria a jihar Kaduna.

    A wata sanarwa da darektan hulda da jama'a na rundunar sojin Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce rundunar ta samu kiran neman agaji ne cewa wasu bata-gari sun yi gangami a Samaru suna kona tayoyi a titi tare da jifan jami'an tsaro, daga nan ne aka tura sojoji domin su je su tarwatsa su tare da tabbatar da bin umarnin da gwamnatin jihar ta yi na dokar hana fita.

    Nwachukwu ya ce zuwan sojojin ke da wuya sai gungun masu zanga-zangar ya fara kokarin kai wa sojojin hari, saboda haka ne ya ce wani soja ya yi harbi na gargadi, to amma harsashin sai ya samu wani yaro mai shekara 16 Isma'il Mohammed.

    Sanarwar ta kara da cewa tuni aka tsare sojan da ya yi harbin kuma ana gudanar da bincike a kansa.

    Haka kuma kakakin ya ce shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriyar, Laftna Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ya tura wata tawaga ta musamman domin zuwa ta yi ta'aziyya ga iyalan matashin.

    Sanarwar ta ce an yi jana'izar matashin tare da wasu manyan jami'an soji da suka halarta.