Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na harin Williams, Juventus na son Marstinez, PSG na zawarcin Olise
Arsenal na nan kan aniyarta na mallakar ɗan wasan ƙungiyar Athletic da ke Sipaniya Nico Williams, yayin da Liverpool, da Manchester United su ma ke harin ɗan wasan. (Teamtalk)
Juventus na tattaunawa da Aston Villa don siyen mai tsaron ragar ƙungiyar Emiliano Martinez, wanda kuma ya amince da hakan don ƙashin kai. (Corriere dello Sport - in Italian)
Paris St-Germain na son ɗaukar ɗan wasan Faransa da Bayern Muncih Micheal Olise a wannan kaka. (L'Equipe - in French)
Manchester United na sa ido kan dan wasan Everton Iliman Ndiaye a dai-dai lokacin da suke ci gaba da inganta ƙungiyar gabanin fara gsar zakarun turai ta Champions League a kaka mai zuwa. (Sky Sports)
Liverpool za ta bar ɗan wasan Italiya Federico Chesa, ya bar ƙungiyar a wannan kaka, kan fam miliyan 17, yayin da ɗan wasan ke son komawa Serai A don ci gaba da taka leda. (Caughtoffside)
Barcelona na sane da buƙatar Chelsea da Arsenal na son ɗaukar ɗan wasa Dani Olmo, sai dai za su bar ɗan wasan ne kawai ya tafi idan har aka amince da siyensa kan fam miliyan 60. (Fichajes - in Spanish)
Ɗan wasan Faransa Mathys na iya bayar da mamaki ta hanyar komawa Bouthmouth daga Tottenham a wannan kaka. (Teamtalk).
Barcelona na son siyar da ɗan wasanta na baya Marc Casado, domin tara kuɗin ɗauko wasu ƴan wasan, yayin da Bayer Leverkusen da wasu ƙungiyoyin da ke taka leda a gasa Firimiya ke harin ɗan wasan. (Fichajes - in Spanish)
Leeds United na son kafa tarihi kan siyen ɗan wasan Sporting Ousmane Diomande, kan fam miliyan 35 baya ga tallilika na fam miliyan 8.(Mirror)
Crystal Palace na shirin gogayya da Everton wajen ɗaukar ɗan wasan Middlesbrough Hayden Hackney, a kakar nan kan fam miliyan 20m. (Mail)